/1 Ubangiji ya bayana gareni tun daga nesa, ya ce, Hakika, na yi kamnarka da madawamiyar kamna; domin wannan na jawo ka da rahama. Amma kuwa Allah na tabbatar mana da kaunad da ya ke mana, wato, tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domimmu. Da kuma Yesu Almasihu amintaccen mashaidi, Na Farko cikin masu tashi daga matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Daukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wannan da ke kaunarmu, ya kuma balle mana kangin zunubammu ta jininsa. Ana nan tun kafin Idin Ketarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da ya ke ya kaunaci mutanensa da ke duniya, sai ya kaunace su har matuka. Saboda kaunad da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makadaicin Dansa, don duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami. /2 An yi wannan ne duk don a cika abin da Ubangiji ya fada ta bakin annabin, cewa, Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi da, Kuma za a sa masa suna Immanu'el, (Ma'anar Immanu'el kuwa, Allah na tare da mu.) Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah ya ke, Kalman nan kuwa Allah ne. Kalman nan kuwa ya zama mutun, ya zauna a cikimmu, yana mai matukar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi daukakarsa, daukaka ce ta makadaicin Da daga wurin Ubansa. Yesu ya ce masa, Na dade tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai ya ga Uban. Yaya, za ka ce, Nuna mana Uban? Wato ba ka gaskata ba cewa ni cikin Uba na ke, Uba kuma cikina? Babu shakka, asirin addinimmu muhimmi ne kwarai: Am bayyana shi da jiki, Ruhun ya nuna shi mai adalci ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An dauke shi sama wurin daukaka. /3 Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, Wannan shi ne Dana kaunataccena, wanda na ke farin ciki da shi kwarai. Don a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar allahntaka ke tabbata. Kowa ya bayyana cewa Yesu Dan Allah ne, sai Allah ya dawwama cikinsa, shi kuma a cikin Allah. Gama an haifa mana yaro, a garemu an bada da: mulkin za ya kasance a kafadassa: za a che da sunansa Al'ajibi, Maishawara, Allah mai-iko duka, Uba Madawami, Sarkin Salama. Mala'ikan ya amsa mata ya ce, Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Madaukaki kuma zai lullube ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa za a kira shi Dan Allah. Yana cikin magana sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, Wannan shi ne Dana kaunataccena, wanda na ke farin ciki da shi kwarai. Ku saurare shi. /4 Muddar ina duniya ni ne hasken duniya. Sai ya ce musu, Ku daga kasa ku ke, ni kuwa daga sama na ke. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyan nan ba ne. Yesu ya ce mata, Ai ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. Yesu ya ce musu, Ni ne Gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai kara jin kishirwa ba har abada. Kuna kirana Malan, kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka na ke. Sai Yesu ya ce musu, Lalle, hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne. Don haka Yesu ya sake ce da su, Lalle, hakika, ina gaya muku, ni ne kofar tumakin. /5 Sai ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne ke wucewa, sai suka daga murya suka ce. Ya Ubangiji, ka ji tausayimmu, ya Dan Dawuda! Don kuma tausayi, sai Yesu ya taba idanunsu, nan take suka sami gani, suka bi shi. Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a kan danyar ciyawa. Da ya dauki gurasa biyar din da kifi biyun, sai ya daga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a. Duka kuwa suka ci suka koshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu. Wadanda suka cin kuwa misalin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara. Siman ya amsa masa ya ce, Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama komai ba, amma da ka yi magana zan saki tarunan. Da suka yi haka kuwa, sai suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa. /6