Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka mulkin ka shi zo.
abin da ka ke so, a yi shi cikin duniya kamar yadda a ke yinsa 
cikin sama. ka ba mu yau abincin yini ka gafarta mana laifun mu,
kamar yadda mu ke gafarta ma wadanda su ke yi mamu laifi.
Kada ka kai mu wurin jaraba, amma ka cece mu daga mugun.
gama mulki, da iko, da girma, naka ne, har abada. Amin.