The Old Testament of the Holy Bible

Farawa 1

Allah ya Halicci Duniya ya kuma Halicci Mutum

1 A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya, 2 duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. 3 Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu, 5 ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan. 6 Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.” 7 Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance. 8 Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan. 9 Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance. 10 Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. 11 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa ke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 12 Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau. 13 Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan. 14 Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai. 15 Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 16 Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin. 17 Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya, 18 su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan. 20 Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.” 21 Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22 Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.” 23 Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan. 24 Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.” 25 Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 26 Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.” 27 Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su. 28 Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.” 29 Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itace da yake da ƙwaya cikin 'ya'yansa su zama abincinku. 30 Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabba da take duniya, da kowane irin tsuntsu da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance. 31 Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

Farawa 2

1 Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu. 2 A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi. 3 Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta. 4 Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa'ad da aka halicce su. A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama, 5 a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar, 6 amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka. 7 Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

Gonar Aidan

8 Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata. 9 Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta. 10 Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu. 11 Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. 12 Zinariyar ƙasar nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin. 13 Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush. 14 Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne. 15 Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. 16 Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da 'yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar, 17 amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.” 18 Sa'an nan sai Ubangiji Allah ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.” 19 Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan. 20 Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba. 21 Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama, 22 haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin. 23 Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.” 24 Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya. 25 Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.

Farawa 3

Faɗuwar Mutum

1 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itace da yake a gonar ba?’ ” 2 Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3 amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin 'ya'yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ” 4 Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. 5 Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.” 6 Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7 Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura. 8 Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9 Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?” 10 Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.” 11 Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?” 12 Mutumin ya ce, “Matar nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.” 13 Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.” 14 Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15 Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.” 16 Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.” 17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. 18 “Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19 Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” 20 Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam. 21 Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.

An Fitar da Adamu da Hawwa'u daga Gonar

22 Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.” 23 Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato, inda aka ɗauko shi. 24 Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.

Farawa 4

Kayinu da Habila

1 Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” 2 Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3 Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5 amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har ya kwantsare fuskarsa. 6 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har fuskarka ya kwantsare? 7 In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.” 8 Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi. 9 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?” Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?” 10 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11 Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka. 12 In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.” 13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina. 14 Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.” 15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi. 16 Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.

Zuriyar Kayinu

17 Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu. 18 An haifa wa Anuhu ɗa, wato, Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek. 19 Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai. 20 Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi. 21 Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa. 22 Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubal-kayinu Na'ama ne. 23 Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa, na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni. 24 Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai.”

Zuriyar Shitu

25 Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.” 26 Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.

Farawa 5

Zuriyar Adamu

1 Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah. 2 Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su. 3 Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu. 4 Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza. 5 Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu. 6 Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh. 7 Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 8 Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu. 9 Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan. 10 Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 11 Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu. 12 Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel. 13 Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 14 Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu. 15 Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared. 16 Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 17 Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu. 18 Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu. 19 Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza. 20 Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu. 21 Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela. 22 Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza. 23 Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar. 24 Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba. 25 Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek. 26 Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 27 Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu. 28 Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa, 29 ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.” 30 Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 31 Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu. 32 Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

Farawa 6

Muguntar 'Yan Adam

1 Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata, 2 sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. 3 Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.” 4 A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru. 5 Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin. 6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai. 7 Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.” 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji. 9 Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah. 10 Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet. 11 Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina. 12 Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Nuhu ya Sassaƙa Jirgi

13 Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi. 14 Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro. 15 Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba'in da biyar, tsayinsa ƙafa arba'in da biyar. 16 Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. 17 Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu. 18 Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da 'ya'yanka, da matarka, da matan 'ya'yanka tare da kai. 19 Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace. 20 Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu. 21 Ka ɗauki kuma kowane irin abinci da ake ci, ka tanada, zai kuwa zama abincinka da nasu.” 22 Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.

Farawa 7

Ruwan Tsufana

1 Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni. 2 Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace, 3 da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka. 4 Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.” 5 Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi. 6 Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya. 7 Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana. 8 Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa, 9 biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu. 10 Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya. 11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12 Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba'in da dare arba'in. 13 A wannan rana Nuhu da 'ya'yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan 'ya'yansa tare suka shiga jirgin, 14 su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi. waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya. 17 Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba'in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya. 18 Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye. 19 Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da suke ƙarƙashin sammai duka. 20 Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar. 21 Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum, 22 da kowane abu da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. 23 Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi. 24 Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

Farawa 8

Ƙarshen Ruwan Tsufana

1 Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye. 2 Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai, 3 ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu. 4 Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat. 5 Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo. 6 A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7 sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya. 8 Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye, 9 amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi. 10 Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin. 11 Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya. 12 Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba. 13 A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya. 14 Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe. 15 Sa'an nan sai Allah ya ce wa Nuhu, 16 “Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai. 17 Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato, tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.” 18 Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi, 19 da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.

Nuhu ya Miƙa Hadaya

20 Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden. 21 Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. 22 Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.”

Farawa 9

Allah ya Yi Alkawari da Nuhu

1 Allah kuwa ya sa wa Nuhu da 'ya'yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku cika duniya. 2 Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku. 3 Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome. 4 Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato, mushe. 5 Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa. 6 “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa. 7 Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.” 8 Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa. 9 “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku, 10 da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya. 11 Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.” 12 Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa, 13 na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14 Sa'ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai, 15 zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba. 16 Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da yake bisa duniya.” 17 Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

Nuhu da 'Ya'yansa Maza

18 'Ya'yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana. 19 Su uku ɗin nan su ne 'ya'yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane. 20 Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi. 21 Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa. 22 Sai Ham, mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa 'yan'uwansa biyu waɗanda suke waje. 23 Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba. 24 Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa. 25 Sai ya ce, “La'ananne ne Kan'ana, bawan bayi zai zama ga 'yan'uwansa.” 26 Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan'ana kuwa ya bauta masa. 27 Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan'ana kuwa ya bauta masa.” 28 Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin. 29 Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.

Farawa 10

Zuriyar 'Ya'yan Nuhu, Maza

1 Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya. 2 'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras. 3 'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma. 4 'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim. 5 Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu. 6 'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana. 7 'Ya'yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama kuwa Sheba da Dedan. 8 Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya. 9 Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.” 10 Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke. 11 Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala, 12 da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato, babban birni. 13 Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa, 14 da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa. 15 Kan'ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het, 16 shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa, 17 da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa, 18 da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu. 19 Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha. 20 Waɗannan su ne 'ya'yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu. 21 An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, 'ya'ya, shi ne kakan 'ya'yan Eber duka. 22 'Ya'yan Shem su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram. 23 'Ya'yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek. 24 Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber. 25 An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan. 26 Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera, 27 da Adoniram, da Uzal, da Dikla, 28 da Ebal, da Abimayel, da Sheba, 29 da Ofir, da Hawila da Yobab, dukan waɗannan 'ya'yan Yokatan ne. 30 Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas. 31 Waɗannan su ne 'ya'yan Shem bisa ga iyalansu, da harsunansu, da ƙasashensu, da kabilansu. 32 Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al'ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.

Farawa 11

Hasumiyar Babila

1 A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. 2 Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can. 3 Sai suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka. 4 Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.” 5 Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina. 6 Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su. 7 Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.” 8 Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin. 9 Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.

Zuriyar Shem

10 Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu. 11 Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 12 Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela. 13 Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 14 Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber, 15 Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 16 Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg, 17 Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 18 Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu. 19 Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 20 Sa'ad da Reyu ya yi shekara talatin da biyu ya haifi Serug. 21 Reyu kuwa ya yi shekara metan da bakwai bayan haihuwar Serug, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 22 Sa'ad da Serug ya yi shekara talatin ya haifi Nahor, 23 Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 24 Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera, 25 Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 26 Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran. 27 Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu. 28 Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa. 29 Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya. 30 Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato, ba ta da ɗa. 31 Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato, matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kaldiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can. 32 Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.

Farawa 12

Allah ya Kira Abram

1 Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka. 2 Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka. 3 Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.” 4 Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran. 5 Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran. Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana, 6 Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar. 7 Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi. 8 Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji. 9 Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.

Abram a Masar

10 A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar. 11 Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce, 12 lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, ‘Wannan matarsa ce,’ za su kashe ni, amma za su bar ki da rai. 13 Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.” 14 Sa'ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai. 15 Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna. 16 Saboda ita Fir'auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.

17 Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya. 18 Sai Fir'auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba? 19 Don me ka ce ita 'yar'uwarka ce, har na ɗauke ta ta zama matata? To, ga matarka, ka ɗauke ta ka tafi.” 20 Fir'auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.

Farawa 13

Rabuwar Abram da Lutu

1 Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu. 2 Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya. 3 Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai, 4 a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji. 5 Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai, 6 domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba. 7 Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne. 8 Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne. 9 Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.” 10 Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata. 11 Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna. 12 Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma. 13 Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.

Abram ya yi Ƙaura zuwa Hebron

14 Sai Ubangiji ya ce wa Abram, bayan da Lutu ya rabu da shi, “Ɗaga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu, 15 gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada. 16 Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka. 17 Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.” 18 Sai Abram ya cire alfarwarsa, ya zo ya zauna kusa da itatuwan oak na Mamre, waɗanda suke Hebron. A can ya gina wa Ubangiji bagade.

Farawa 14

Abram ya 'Yanto Lutu

1 A zamanin Amrafel Sarkin Shinar, shi da Ariyok Sarkin Ellasar, da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, 2 suka fita suka yi yaƙi da Bera Sarkin Saduma, da Birsha Sarkin Gwamrata, da Shinab Sarkin Adma, da Shemeber Sarkin Zeboyim, da kuma Sarkin Bela, wato, Zowar. 3 Waɗannan sarakuna biyar suka haɗa kai don su kai yaƙi, suka haɗa mayaƙansu a kwarin Siddim, inda Tekun Gishiri take. 4 Shekara goma sha biyu suka bauta wa Kedarlayomer, amma suka tayar a shekara ta goma sha uku. 5 A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim, 6 da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato, Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji. 7 Sai suka juya suka je Enmishfat, wato, Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar. 8-9 Sai Sarkin Saduma, da Sarkin Gwamrata, da Sarkin Adma da Sarkin Zeboyim, da Sarkin Bela, wato, Zowar, suka fita suka ja dāga da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, da Amrafel Sarkin Shinar, da Ariyok Sarkin Ellasar a kwarin Siddim, sarakuna huɗu gāba da biyar. 10 Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen. 11 Sai abokan gāba suka kwashe dukan kayayyakin Saduma da na Gwamrata, da abincinsu duka, suka yi tafiyarsu. 12 Suka kuma kama Lutu ɗan ɗan'uwan Abram, wanda yake zaune a Saduma, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu. 13 Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba'ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram. 14 Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan. 15 Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu. 16 Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan'uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.

Malkisadik ya Sa wa Abram Albarka

17 Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa'ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato, Kwarin Sarki. 18 Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato, Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki. 19 Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka. 20 Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka. 21 Sai Sarkin Saduma ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanen, amma ka riƙe kayayyakin don kanka.” 22 Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa, 23 cewa, ba zan ɗauki ko da zare ɗaya ko maɗaurin takalmi ba, ko kowane abin da yake naka, domin kada ka ce, ‘Na arzuta Abram.’ 24 A ni kaina ba zan ɗauki kome ba illa abin da samari suka ci, da rabon mutanen da suka tafi tare da ni. Sai dai kuma Aner, da Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu rabo.”

Farawa 15

Alkawarin da yake tsakanin Allah da Abram

1 Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.” 2 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?” 3 Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.” 4 Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.” 5 Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.” 6 Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi. 7 Ubangiji kuma ya ce masa, “Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ka daga Ur ta Kaldiyawa, don in ba ka wannan ƙasa ka gāje ta.” 8 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, yaya zan mallake ta?” 9 Ya ce masa, “Kawo mini karsana bana uku, da burguma bana uku, da rago bana uku, da hazbiya da ɗan tattabara.” 10 Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. 11 Sa'ad da tsuntsaye masu cin nama suke sauka bisansu sai Abram ya kore su. 12 Sa'ad da rana take faɗuwa, barci mai nauyi ya kwashe Abram, sai ga babban duhu mai bantsoro ya rufe shi. 13 Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani lalle ne zuriyarka za ta yi baƙunci cikin ƙasar da ba tata ba ce, za ta kuwa yi bauta, za a kuma tsananta mata har shekara arbaminya, 14 amma zan hukunta al'ummar da suka bauta wa, daga baya kuma da dukiya mai yawa za ta fita. 15 Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka. 16 A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.” 17 Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka. 18 A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato, Kogin Yufiretis ke nan, 19 ƙasar Keniyawa, da Kenizziyawa, da Kadmoniyawa, 20 da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Refayawa, 21 da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”

Farawa 16

Hajaratu da Isma'ilu

1 Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu. 2 Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya. 3 A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan'ana sa'ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa. 4 Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine. 5 Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai.” 6 Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta. 7 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato, maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur. 8 Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?” Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.” 9 Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.” 10 Mala'ikan Ubangiji kuma ya ce mata, “Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu.” 11 Mala'ikan Ubangiji kuma ya ƙara ce mata, “Ga shi, kina da ciki, za ki haifi ɗa, za ki kira sunansa Isma'ilu, domin Ubangiji ya lura da wahalarki. 12 Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.” 13 Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?” 14 Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered. 15 Hajaratu ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya sa wa ɗa da Hajaratu ta haifa suna, Isma'ilu. 16 Abram yana da shekara tamanin da shida sa'ad da Hajaratu ta haifa masa Isma'ilu.

Farawa 17

Kaciya ita ce Shaidar Alkawarin

1 A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili. 2 Zan yi maka alkawari, in ba ka zuriya mai yawa.” 3 Sai Abram ya yi ruku'u, Allah kuwa ya ce masa, 4 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa. 5 Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa. 6 Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito. 7 “Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka. 8 Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato, dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.” 9 Allah kuma ya ce wa Ibrahim, “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, da kai da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu. 10 Wannan shi ne alkawarina da za ka kiyaye, da kai da zuriyarka a bayanka. Sai a yi wa kowane ɗa namiji kaciya. 11 Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku. 12 Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba. 13 Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan. 14 Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato, wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama'arsa, don ya ta da alkawarina.” 15 Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta. 16 Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.” 17 Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?” 18 Sai Ibrahim ya ce wa Allah, “Da ma dai a bar Isma'ilu kawai ya rayu a gabanka.” 19 Allah ya ce, “A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa. 20 Ga zancen Isma'ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin 'ya'yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al'umma mai girma. 21 Amma ga Ishaku ne zan tsai da alkawarina, wato, wanda Saratu za ta haifa maka a baɗi war haka.” 22 Sa'ad da Allah ya gama magana da Ibrahim, sai ya tafi ya bar Ibrahim. 23 Ibrahim kuwa ya ɗauki Isma'ilu ɗansa, da dukan bayi, haifaffun gidansa, da waɗanda aka sayo su da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji na jama'ar gidansa kaciyar loɓarsa a wannan rana bisa ga faɗar Allah. 24 Ibrahim na da shekara tasa'in da tara sa'ad da aka yi masa kaciyar loɓarsa. 25 Isma'ilu ɗansa yana ɗan shekara goma sha uku sa'ad da aka yi masa kaciya. 26 A wannan rana, Ibrahim da ɗansa Isma'ilu aka yi musu kaciya, 27 da mazajen gidansa duka, da waɗanda suke haifaffun gidan da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙi, aka yi musu kaciya tare da shi.

Farawa 18

An Alkawarta Haihuwar Ishaku

1 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana. 2 Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u, 3 ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima. 4 Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace, 5 ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.” Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.” 6 Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.” 7 Sai Ibrahim ya sheƙa zuwa garke, ya ɗauki maraƙi, matashi mai kyau, ya ba baransa, ya kuwa shirya shi nan da nan. 8 Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa'ad da suke ci. 9 Suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ya ce, “Tana cikin alfarwa.” 10 Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne. 11 Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al'adar mata. 12 Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa'an nan zan sami wannan gatanci?” 13 Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, ‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?’ 14 Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.” 15 Amma Saratu ta yi m�su, tana cewa, “Ai, ban yi dariya ba,” Gama tana jin tsoro. Ya ce, “A'a, hakika kin yi dariya.”

Ibrahim ya Yi Roƙo don Saduma

16 Sai mutanen suka tashi daga wurin, suka fuskanci Saduma, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya ya sallame su. 17 Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa? 18 Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al'umma mai iko, sauran al'umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa. 19 Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa. 20 Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai, 21 zan sauka in gani ko sun aikata kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.” 22 Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji. 23 Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun? 24 Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba? 25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato, da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?” 26 Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.” 27 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka. 28 Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?” Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.” 29 Ya kuma sāke yin masa magana, ya ce, “Da a ce za a sami arba'in a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da arba'in ɗin ba zan yi ba.” 30 Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?” Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.” 31 Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.” 32 Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.” 33 Ubangiji kuwa ya yi tafiyarsa, bayan ya gama magana da Ibrahim. Ibrahim kuwa ya koma gida.

Farawa 19

Zunubin Sadumawa ya Haɓaka

1 Mala'ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa'ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku'u a gabansu, 2 ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.” Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.” 3 Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci. 4 Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan. 5 Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.” 6 Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane, 7 ya ce, “Ina roƙonku 'yan'uwana, kada ku aikata mugunta haka. 8 Ga shi, ina da 'ya'ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.” 9 Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar. 10 Amma baƙin suka miƙa hannunsu, suka shigar da Lutu cikin gida inda suke, suka rufe ƙofa. 11 Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.

Lutu ya Bar Saduma

12 Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko 'ya'ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin, 13 gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.” 14 Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi. 15 Sa'ad da safiya ta gabato, mala'ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da 'ya'yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.” 16 Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na 'ya'yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin. 17 Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.” 18 Sai Lutu ya ce musu, “A'a, ba haka ba ne iyayengijina, 19 ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu. 20 Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.” 21 Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. 22 Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.

Halakar Saduma da Gwamrata

23 Da hantsi Lutu ya isa Zowar. 24 Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama, 25 ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire. 26 Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri. 27 Da sassafe kuwa sai Ibrahim ya tafi wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji, 28 ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar. 29 Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.

Asalin Mowabawa da Ammonawa

30 Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata. 31 Sai 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko'ina a duniya. 32 Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa'an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” 33 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi. Da daren nan kuwa 'yar farin ta shiga ta kwana da mahaifinta, shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta. 34 Kashegari kuma, 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Ga shi, daren jiya na kwana da mahaifina, bari daren yau kuma, mu sa shi ya sha ruwan inabi, ke ma sai ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” 35 Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta. 36 Haka nan kuwa, 'ya'yan Lutu biyu ɗin nan suka sami ciki daga mahaifinsu. 37 Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau. 38 Ƙaramar kuma ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Benammi, shi ne asalin Ammonawa har yau.

Farawa 20

Ibrahim da Abimelek

1 Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi zuwa wajen karkarar Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. A lokacin da Ibrahim yake baƙunci a Gerar, 2 ya ce, matarsa Saratu 'yar'uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu. 3 Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.” 4 Abimelek bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ubangiji, za ka hallaka marar laifi? 5 Ba shi ya faɗa mini, ‘Ita 'yar'uwata ce’ ba? Ba ita kanta kuma ta ce, ‘Shi ɗan'uwana ne’ ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.” 6 Allah ya ce masa cikin mafarki, “I, na sani ka yi wannan cikin mutunci, ai, ni na hana ka ka aikata zunubin, don haka ban yarda maka ka shafe ta ba. 7 Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.” 8 Abimelek ya tashi da sassafe, ya kira barorinsa duka ya kuma faɗa musu waɗannan abubuwa duka. Mutanen kuwa suka ji tsoro ƙwarai. 9 Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.” 10 Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?” 11 Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata. 12 Banda haka nan ma, hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta. 13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawaceyawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ” 14 Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu. 15 Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.” 16 Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan'uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa, ba ki da laifi.” 17 Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa. 18 Gama dā Allah ya kulle mahaifar dukan gidan Abimelek saboda Saratu matar Ibrahim.

Farawa 21

Haihuwar Ishaku

1 Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta. 2 Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa. 3 Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku. 4 Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi. 5 Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa'ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku. 6 Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.” 7 Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa 'ya'ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.” 8 Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.

Korar Hajaratu da Isma'ilu

9 Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku. 10 Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.” 11 Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa. 12 Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka. 13 Zan kuma yi al'umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.” 14 Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba. 15 Sa'ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. 16 Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka. 17 Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me ke damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake. 18 Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al'umma.” 19 Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha. 20 Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi. 21 Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.

Ibrahim da Abimelek suka Ƙulla Yarjejeniya

22 A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha'aninka duka, 23 don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa, ba za ka ci amanata, ko ta 'ya'yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.” 24 Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.” 25 Sa'ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace, 26 Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.” 27 Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari. 28 Ibrahim ya ware 'yan raguna bakwai daga cikin garke. 29 Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Ina ma'anar waɗannan 'yan raguna bakwai da ka keɓe?” 30 Ya ce, “Waɗannan 'yan raguna bakwai za ka karɓe su daga hannuna domin su zama shaida a gare ni, cewa, ni na haƙa rijiyan nan.” 31 Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa. 32 Saboda haka suka yi alkawari a Biyer-sheba. Sai Abimelek, tare da Fikol shugaban sojojinsa, ya tashi ya koma ƙasar Filistiyawa. 33 Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami. 34 Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.

Farawa 22

An Umarci Ibrahim ya yi Hadaya da Ishaku

1 Bayan waɗannan al'amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.” 2 Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.” 3 Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa. 4 A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa. 5 Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa'an nan mu komo wurinku.” 6 Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare. 7 Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!” Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.” Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?” 8 Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare. 9 Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden. 10 Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa. 11 Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.” 12 Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.” 13 Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa. 14 Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.” 15 Mala'ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama, 16 ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba, 17 hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka, 18 ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.” 19 Sai Ibrahim ya koma wurin samarinsa. Suka tashi suka tafi Biyer-sheba tare. Ibrahim ya yi zamansa a Biyer-sheba.

Zuriyar Nahor

20 Ana nan bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan'uwanka Nahor, 'ya'ya. 21 Uz ɗan fari, da Buz ɗan'uwansa, da Kemuwel mahaifin Aram, 22 da Kesed, da Hazo, da Fildash, da Yidlaf, da Betuwel.” 23 Betuwel kuwa ya haifi Rifkatu, su takwas ɗin nan Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim. 24 Banda haka, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifi Teba, da Gaham, da Tahash, da Ma'aka.

Farawa 23

Ibrahim ya Sayi Makabarta a Rasuwar Saratu

1 Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya, 2 sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato, Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu. 3 Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa, 4 “Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!” 5 Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce, 6 “Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.” 7 Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar. 8 Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar, 9 ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.” 10 A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce, 11 “Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.” 12 Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama'ar ƙasar. 13 Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama'ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.” 14 Efron ya amsa wa Ibrahim, 15 “Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.” 16 Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci. 17 Don haka saurar Efron da ke cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka 18 an tabbatar wa Ibrahim, cewa, mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu. 19 Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato, Hebron, cikin ƙasar Kan'ana. 20 Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.

Farawa 24

Aka Auro wa Ishaku Mata

1 Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka. 2 Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, 3 ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa, ba za ka auro wa ɗana mata daga 'yan matan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba. 4 Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.” 5 Sai baransa ya ce masa, “Watakila matar ba za ta yarda ta biyo ni zuwa wannan ƙasa ba, tilas ke nan, in koma da ɗanka ƙasar da ka fito?” 6 Ibrahim ya ce masa, “Ka kiyaye wannan fa, kada ka kuskura ka koma da ɗana can. 7 Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala'ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can. 8 Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.” 9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi. 10 Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor. 11 Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato, lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa. 12 Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim. 13 Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma 'yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa. 14 Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.” 15 Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan'uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta. 16 Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro. 17 Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.” 18 Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha. 19 Sa'ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.” 20 Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka. 21 Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu? 22 Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta, 23 ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?” 24 Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.” 25 Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.” 26 Mutumin ya yi ruku'u ya yi wa Ubangiji sujada, 27 ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.” 28 Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa. 29 Rifkatu kuwa tana da ɗan'uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya. 30 Sa'ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan 'yar'uwarsa, sa'ad da kuma ya ji maganar Rifkatu 'yar'uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. 31 Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.” 32 Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi. 33 Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Laban ya ce, “Faɗi maganarka.” 34 Ya ce, “Ni baran Ibrahim ne. 35 Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai. 36 Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi. 37 Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin 'ya'yan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba, 38 amma ka tafi gidan mahaifina da dangina, ka auro wa ɗana mace.’ 39 Sai na ce wa maigidana, ‘Watakila matar ba za ta biyo ni ba.’ 40 Amma ya amsa mini ya ce, ‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala'ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina. 41 Sa'an nan za ka kuɓuta daga rantsuwata. Sa'ad da ka zo wurin dangina, idan kuwa ba su ba ka ita ba, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’ 42 “Yau kuwa da na iso bakin rijiyar, sai na ce a raina, ‘Ya Ubangiji, Allah na shugabana Ibrahim, in nufinka ne ka arzuta tafiyata. 43 Ga ni, ina tsaye a bakin rijiyar kuwa, bari budurwar da za ta fito ɗibar ruwa, wadda in na ce mata, “Roƙo nake, ba ni ruwa kaɗan daga ruwan tulunki in sha,” 44 in ta amsa mini, “To, sha, zan ɗebo wa raƙumanka kuma,” bari ta zama ita ce wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’ 45 Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, ‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.’ 46 Nan da nan ta sauke tulunta daga kafaɗarta, ta ce, ‘To, sha, zan kuma shayar da raƙumanka.’ Na sha, ta kuma shayar da raƙuman. 47 Na kuwa tambaye ta, ‘'Yar gidan wane ne ke?’ Ta ce, ‘Ni 'yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu. 48 Sa'an nan na yi ruku'u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa 'yar danginsa. 49 Yanzu fa, idan za ku amince ku gaskata da maigidana, ku faɗa mini, in ba haka ba, sai ku faɗa mini, domin in san abin yi, in juya dama ko hagu.” 50 Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a. 51 Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.” 52 Sa'ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji. 53 Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan'uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada. 54 Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.” 55 Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.” 56 Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.” 57 Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.” 58 Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?” Sai ta ce, “Zan tafi.” 59 Suka kuwa sallami Rifkatu 'yar'uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa. 60 Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata, “'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyar dubbai, Har dubbai goma, Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin maƙiyansu!” 61 Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma. 62 A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb. 63 A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa. 64 Da Rifkatu ta ɗaga idanunta, ta hangi Ishaku, sai ta sauka daga raƙumi, 65 ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?” Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi. 66 Sai baran ya faɗa wa Ishaku dukan abin da ya yi. 67 Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Farawa 25

Sauran Zuriyar Ibrahim

1 Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura. 2 Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. 'Ya'yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le'umomim. 4 'Ya'yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka 'ya'yan Ketura ne. 5 Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi. 6 Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.

Rasuwar Ibrahim da Jana'izarsa

7 Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar. 8 Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi. 9 Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre, 10 wato, saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa. 11 Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.

Zuriyar Isma'ilu

12 Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim. 13 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma'ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam, 14 da Mishma, da Duma, da Massa, 15 da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema. 16 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu. 17 Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi. 18 Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.

Haihuwar Isuwa da Yakubu

19 Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku. 20 Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye. 21 Ishaku kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji domin matarsa Rifkatu, da shike ita bakarariya ce. Ubangiji ya ji addu'arsa, sai matarsa Rifkatu ta yi ciki. 22 'Ya'yan kuwa suka kama kokawa da juna a cikinta, har ta ce, “In haka ne don me zan rayu?” Sai ta je ta tambayi Ubangiji. 23 Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.” 24 Sa'ad da kwanakin haihuwarta suka cika, sai ga shi, ashe, tagwaye ne suke a cikin mahaifarta. 25 Na farin ya fito ja wur kamar riga mai gashi, saboda haka suka raɗa masa suna Isuwa. 26 Daga baya kuma ɗan'uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa'ad da ya haife su.

Isuwa ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari

27 Sa'ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida. 28 Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu. 29 Wata rana, sa'ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai. 30 Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom. 31 Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.” 32 Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?” 33 Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari. 34 Sa'an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.

Farawa 26

Ishaku a Gerar da Biyer-sheba

1 Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa. 2 Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka. 3 Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka. 4 Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka, 5 saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka'idodina, da shari'una.” 6 Ishaku ya yi zamansa a Gerar. 7 Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce. 8 Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu. 9 Sai Abimelek ya kira Ishaku, ya ce, “Ashe lalle ita matarka ce, ƙaƙa fa ka ce, ‘Ita 'yar'uwata ce?’ ” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.” 10 Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ai, da wani daga jama'a ya kwana da matarka a sawwaƙe, da ka jawo laifi a bisanmu.” 11 Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.” 12 Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekarar nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka, 13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. 14 Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa. 15 Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai. 16 Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.” 17 Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can. 18 Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu. 19 Amma sa'ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa. 20 Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa, “Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta. 21 Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna. 22 Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.” 23 Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba. 24 Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.” 25 Ishaku ya gina bagade a wurin ya kira bisa sunan Ubangiji, a can kuwa ya kafa alfarwarsa. A can ne kuma barorin Ishaku suka haƙa rijiya.

Yarjejeniya tsakanin Ishaku da Abimelek

26 Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku. 27 Sai Ishaku ya ce musu, “Me ke tafe da ku zuwa gare ni, ga shi kun ƙi ni, kun kuma kore ni nesa da ku?” 28 Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa, bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai, 29 cewa, ba za ka cuce mu ba, daidai kamar yadda ba mu taɓe ka ba, ba mu yi maka kome ba sai alheri, muka kuwa sallame ka cikin salama. Yanzu, kai albarkatacce ne na Ubangiji.” 30 Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha. 31 Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama. 32 Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.” 33 Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba. 34 Sa'ad da Isuwa yake da shekara arba'in, ya auro Judit, 'yar Biyeri Bahitte, da Basemat 'yar Elon Bahitte, 35 suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.

Farawa 27

Yakubu ya Karɓi Albarka daga wurin Ishaku

1 Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!” Sai ya amsa, “Ga ni nan.” 2 Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba. 3 Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama, 4 ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.” 5 Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa'ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo, 6 sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan'uwanka Isuwa, ya ce, 7 ‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’ 8 Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka. 9 Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so. 10 Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.” 11 Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne. 12 Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.” 13 Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.” 14 Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so. 15 Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su, 16 fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi. 17 Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya. 18 Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.” Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?” 19 Yakubu ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini, in ka yarda ka tashi ka ci naman da na harbo, domin ka sa mini albarka.” 20 Amma Ishaku ya ce wa ɗansa, “Ƙaƙa aka yi ka same shi da sauri haka, ɗana?” Sai ya amsa, “Domin Ubangiji, Allahnka, ya ba ni sa'a.” 21 Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.” 22 Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.” 23 Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka. 24 Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa, “Ni ne.” 25 Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha. 26 Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.” 27 Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce, “Duba, ƙanshin ɗana Yana kama da ƙanshin jeji Wanda Ubangiji ya sa wa albarka! 28 Allah ya ba ka daga cikin raɓar sama, Daga cikin ni'imar ƙasa, Da hatsi a yalwace da ruwan inabi. 29 Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.” 30 Ishaku yana gama sa wa Yakubu albarka, Yakubu yana fita daga gaban mahaifinsa ke nan sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya komo daga farauta. 31 Shi kuma ya shirya abinci mai daɗin ci, ya kawo wa mahaifinsa. Sai ya ce wa mahaifinsa, “In ka yarda baba, ka tashi, ka ci naman da na harbo don ka sa mini albarka.” 32 Mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.” 33 Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka?�I, albarkatacce zai zama.” 34 Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi k�wwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.” 35 Amma ya ce, “Ɗan'uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.” 36 Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?” 37 Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?” 38 Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka. 39 Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisanci mazauninka, Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za ta nisance ka. 40 Ta wurin takobinka za ka rayu Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka, Amma sa'ad da ka ɓalle, Za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.” 41 Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.” 42 Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan'uwanka Isuwa, yana ta'azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa. 43 Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran, 44 ka zauna tare da shi 'yan kwanaki, har zafin fushin ɗan'uwanka ya huce, 45 ya manta da abin da ka yi masa, sa'an nan zan aika in komo da kai daga can. Don me zan rasa ku, ku biyu a rana ɗaya?”

Ishaku ya Aika da Yakubu wurin Laban

46 Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato, daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”

Farawa 28

1 Ishaku ya kira Yakubu ya sa masa albarka, ya umarce shi da cewa, “Ba za ka auri ɗaya daga cikin 'ya'yan matan Kan'aniyawa ba. 2 Tashi, ka tafi Fadan-aram, zuwa gidan Betuwel kakanka na wajen mahaifiya, ka zaɓo wa kanka mata daga cikin 'ya'ya mata na Laban ɗan'uwan mahaifiyarka a can. 3 Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i, 4 ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!” 5 Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.

Isuwa ya Ƙara Auro Wata

6 Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka, ya kuwa sallame shi zuwa Fadan-aram domin ya auro mace daga can. Da Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka ya kuma umarce shi da cewa, “Ba za ka auro wata daga cikin 'yan matan Kan'aniyawa ba,” 7 ya kuma ga Yakubu ya biye wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, har ya tafi Fadan-aram, 8 sai Isuwa ya gane 'yan matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba. 9 Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma'ilu ya auro Mahalat 'yar'uwar Nebayot, 'yar Isma'ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.

Mafarkin Yakubu a Betel

10 Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran. 11 Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci. 12 Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa! 13 Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka. 14 Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka. 15 Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasar nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.” 16 Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.” 17 Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.” 18 Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al'amudi, ya kuwa zuba mai a kan al'amudin. 19 Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz. 20 Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa, 21 har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna, 22 wannan dutse kuwa wanda na kafa shi al'amudi zai zama wurin sujada ga Allah. Daga cikin dukan abin da ya ba ni, zan ba shi ushirinsa.”

Farawa 29

Yakubu ya Isa Gidan Laban

1 Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya. 2 Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba. 3 A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya. 4 Yakubu ya ce musu, “'Yan'uwana, daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga Haran muke.” 5 Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?” Suka ce, “Mun san shi.” 6 Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?” Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila 'yarsa, tana zuwa da bisashensa!” 7 Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?” 8 Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa'an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa'an nan mu shayar da garkuna.” 9 Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu. 10 Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, 'yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa. 11 Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi. 12 Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta. 13 Sa'ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al'amura duka. 14 Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.

Yakubu ya yi wa Laban Barantaka domin Rahila da Lai'atu

15 Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?” 16 Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila. 17 Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya. 18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.” 19 Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.” 20 Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata. 21 Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.” 22 Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki. 23 Amma da maraice, ya ɗauki 'yarsa Lai'atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta. 24 (Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta). 25 Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?” 26 Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari. 27 Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.” 28 Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa'an nan Laban ya aurar masa da 'yarsa Rahila. 29 (Laban ya ba 'yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta). 30 Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai'atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.

An Haifa wa Yakubu 'Ya'ya

31 Sa'ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai'atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce. 32 Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.” 33 Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu. 34 Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni, domin na haifa masa 'ya'ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi. 35 Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.

Farawa 30

1 Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!” 2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?” 3 Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami 'ya'ya ta wurinta.” 4 Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta. 5 Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa. 6 Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan. 7 Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 8 Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da 'yar'uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali. 9 Sa'ad da Lai'atu ta ga ta daina haihuwa, sai ta ɗauki kuyangarta Zilfa, ta ba Yakubu ta zama matarsa. 10 Kuyangar Lai'atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa. 11 Lai'atu kuma ta ce, “Sa'a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad. 12 Kuyangar Lai'atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 13 Lai'atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru. 14 A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta mahaifiya a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.” 15 Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?” Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.” 16 Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan. 17 Allah ya saurari Lai'atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar. 18 Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka. 19 Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida. 20 Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna. 21 Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu. 22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta. 23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,” 24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”

Yakubu ya Yi Jinga da Laban

25 Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu. 26 Ka ba ni matana da 'ya'yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.” 27 Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa, Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai. 28 Ka faɗa mini ladanka in ba ka.” 29 Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna. 30 Gama kafin in zo, kana da 'yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?” 31 Ya ce, “Me zan ba ka?” Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi, 32 bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana. 33 Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.” 34 Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.” 35 Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun 'ya'yansa maza, 36 ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban. 37 Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili. 38 Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato, kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa'ad da suka zo shan ruwa. 39 Garkunan suka yi barbara a gaban tsabgogin, don haka garkunan sukan haifi masu zāne, dabbare-dabbare da masu sofane. 40 Yakubu kuwa yakeɓe 'yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da ke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba. 41 A kowane lokacin da ƙarfafan suke barbara Yakubu yakan sa tsabgogin a magudana a gaban idanun garken, domin su yi barbara a tsakanin tsabgogin. 42 Amma ga marasa ƙarfi na garken, ba ya sa musu. Don haka marasa ƙarfin ne na Laban, ƙarfafan kuwa na Yakubu. 43 Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.

Farawa 31

Yakubu ya Gudu daga wurin Laban

1 Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.” 2 Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā. 3 Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.” 4 Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai'atu zuwa cikin saura inda garkensa yake, 5 ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni. 6 Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina, 7 duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba. 8 In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane. 9 Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni. 10 “A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garke, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne. 11 Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’ 12 Ya kuwa ce, ‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da ke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka. 13 Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasar nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ” 14 Rahila da Lai'atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu? 15 Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu. 16 Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da 'ya'yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.” 17 Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa, 18 ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku. 19 Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta. 20 Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba. 21 Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

Laban ya Bi Sawun Yakubu

22 Sa'ad da aka sanar da Laban, cewa, Yakubu ya gudu da kwana uku, 23 sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai. 24 Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.” 25 Sai Laban ya ci wa Yakubu. A yanzu Yakubu ya riga ya kafa alfarwarsa a ƙasa ta tuddai, Laban da danginsa kuma suka yi zango a ƙasar Gileyad ta tuddai. 26 Laban ya ce wa Yakubu, “Me ka yi ke nan, da ka cuce ni, ka gudu da 'ya'yan matana kamar kwason yaƙi? 27 Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya. 28 Don me ba ka bari na sumbaci 'ya'yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta. 29 Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’ 30 Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?” 31 Yakubu ya amsa wa Laban, ya ce, “Domin na ji tsoro ne gama na yi zaton za ka ƙwace 'ya'yanka mata ƙarfi da yaji. 32 Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba. 33 Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai'atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai'atu, ya shiga ta Rahila. 34 Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba. 35 Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al'adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba. 36 Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina? 37 Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gidanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari'a tsakanina da kai. 38 Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba. 39 Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna. 40 Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci. 41 A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma. 42 Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”

Yarjejeniya Tsakanin Yakubu da Laban

43 Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa? 44 Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.” 45 Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al'amudi. 46 Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu,” sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin. 47 Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed. 48 Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed. 49 Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa'ad da muka rabu da juna. 50 Idan ka wulakanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda 'ya'yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.” 51 Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al'amudi, wanda na kafa tsakanina da kai. 52 Wannan tsibi, shaida ce, al'amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al'amudi zuwa wurina don cutarwa ba. 53 Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku. 54 Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen. 55 Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.

Farawa 32

Yakubu ya yi Shirin Saduwa da Isuwa

1 Yakubu ya yi tafiyarsa, mala'ikun Allah kuma suka gamu da shi. 2 Sa'ad da Yakubu ya gan su ya ce, “Waɗannan rundunar Allah ce!” Saboda haka ya sa wa wannan wuri suna Mahanayim. 3 Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan'uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom, 4 yana umartarsu da cewa, “Haka za ku faɗa wa shugabana Isuwa, ‘Ga abin da baranka Yakubu ya ce, “Na yi baƙunta a ƙasar Laban, na zauna har wa yau. 5 Ina da takarkarai, da jakai, da garkuna, da barori mata da maza, na kuwa aika a faɗa wa shugabana domin in sami tagomashi a idonka.” ’ ” 6 Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan'uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.” 7 Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu, 8 yana tunani cewa, “In Isuwa ya zo ya hallaka ƙungiya guda, ƙungiyar da ta ragu sai ta tsira.” 9 Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’ 10 ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu. 11 Ka cece ni ina roƙonka daga hannun ɗan'uwana, wato, daga hannun Isuwa, gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya karkashe mu duka, 'ya'ya da iyaye. 12 Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ” 13 Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi, 14 awakai metan da bunsurai ashirin, tumaki metan da raguna ashirin, 15 raƙuman tatsa talatin tare da 'yan taguwoyi, shanu arba'in da bijimai goma, jakai mata ashirin da jakai maza goma. 16 Waɗannan ya sa su a hannun barorinsa ƙungiya ƙungiya, ya ce wa barorinsa, “Ku yi gaba, ku ba da rata tsakanin ƙungiya da ƙungiya.” 17 Ya umarci na kan gaba, ya ce, “Sa'ad da Isuwa ɗan'uwana ya gamu da ku, ya tambaye ku cewa, ‘Ku mutanen wane ne? Ina za ku? Waɗannan da suke gabanku na wane ne?’ 18 Sa'an nan sai ku ce, ‘Na Yakubu baranka ne, kyauta ce zuwa ga shugabana Isuwa, ga shi nan ma biye da mu.’ ” 19 Da haka nan ya umarci na biyu da na uku da dukan waɗanda suke korar garkunan, ya ce, “Sai ku faɗa wa Isuwa daidai haka nan. 20 Ku kuma ce, ‘Ga shi ma, Yakubu ɗan'uwanka yana biye da mu.’ ” Gama, cikin tunaninsa ya ce, “Ya yiwu in gamshe shi da kyautar da ta riga ni gaba, daga baya in ga fuskarsa, watakila ya karɓe ni.” 21 Saboda haka kyautar ta yi gaba, shi kansa kuwa a daren, ya sauka a zango.

Yakubu ya Yi Kokawa a Feniyel

22 A wannan dare kuwa ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da kuyanginsa biyu da 'ya'yansa goma sha ɗaya ya haye mashigin Jabbok. 23 Ya ɗauke su ya haye da su rafi, haka kuma ya yi da dukan abin da yake da shi. 24 Aka bar Yakubu shi kaɗai. Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari. 25 Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi. 26 Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.” Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.” 27 Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Yakubu.” 28 Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.” 29 Sa'an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka. 30 Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.” 31 Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa. 32 Saboda haka, har wa yau, Isra'ilawa ba sā cin jijiyar kwatangwalo wadda take a kwarin kwatangwalo, domin an taɓi kwarin kwatangwalon Yakubu ta jijiyar kwatangwalo.

Farawa 33

Yakubu ya Sadu da Isuwa

1 Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai'atu da Rahila 'ya'yan, tare da kuyangin nan biyu. 2 Ya sa kuyangin da 'ya'yansu a gaba, sa'an nan Lai'atu sa'an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka. 3 Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa'ad da ya kai kusa da ɗan'uwansa. 4 Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka. 5 Sa'ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da 'ya'ya, ya ce, “Suwane ne waɗannan tare da kai?” Yakubu ya ce, “Su ne 'ya'ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.” 6 Sai kuyangin suka matso kusa, su da 'ya'yansu, suka sunkuya ƙasa. 7 Haka nan kuma Lai'atu da 'ya'yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa. 8 Isuwa kuwa ya ce, “Ina manufarka da duk waɗannan ƙungiyoyi da na gamu da su?” Yakubu ya amsa, ya ce, “Ina neman tagomashi ne a idon shugabana.” 9 Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.” 10 Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni. 11 Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa. 12 Sa'an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.” 13 Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani 'ya'yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka. 14 Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.” 15 Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.” Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.” 16 A ran nan Isuwa ya koma a kan hanyarsa zuwa Seyir. 17 Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot. 18 Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin. 19 Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari. 20 A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.

Farawa 34

An Yi wa Dinatu Faɗe

1 Yanzu fa Dinatu 'yar Lai'atu, wadda ta haifa wa Yakubu, ta fita ta ziyarci waɗansu matan ƙasar, 2 sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta. 3 Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu 'yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi. 4 Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.” 5 Yakubu kuwa ya ji an ɓata 'yarsa, Dinatu, amma 'ya'yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo. 6 Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi. 7 'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi kwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba. 8 Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure. 9 Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu. 10 Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana'a, ku sami dukiya.” 11 Shekem kuma ya ce wa mahaifin Dinatu da 'yan'uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku, dukan abin da kuka ce kuwa, sai in yi. 12 Ku fada mini ko nawa ne dukiyar auren da sadakin, zan kuwa bayar bisa ga yadda kuka faɗa mini, in dai kawai ku ba ni budurwar ta zama matata.” 13 'Ya'yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha'ince, domin ya ɓata 'yar'uwarsu Dinatu. 14 Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu. 15 Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato, idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya. 16 Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya. 17 Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki 'yarmu, mu kama hanyarmu.” 18 Hamor da ɗansa Shekem suka yi na'am da sharuɗan. 19 Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan. 20 Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce, 21 “Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata. 22 Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama'a ɗaya, wato, kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya. 23 Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.” 24 Duk jama'ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya. 25 A rana ta uku, sa'ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka. 26 Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu. 27 'Ya'yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata 'yar'uwarsu. 28 Suka kwashe garkunan awaki da tumaki, da garkunan shanu da jakunansu da dukan abin da yake cikin birnin da na cikin saura, 29 dukan dukiyarsu, da 'yan ƙananansu, da matansu, wato, dukan abin da yake cikin gidajen, suka kwashe. 30 Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.” 31 Amma 'ya'yansa suka ce, “Zai mai da ƙanwarmu kamar karuwa?”

Farawa 35

Allah ya Sa wa Yakubu Albarka a Betel

1 Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.” 2 Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku, 3 sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.” 4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda yake kusa da Shekem. 5 Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu. 6 Sai Yakubu ya zo Luz, wato, Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi. 7 A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa. 8 Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut. 9 Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka. 10 Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila. 11 Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka. 12 Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.” 13 Sa'an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana. 14 Sai Yakubu ya kafa al'amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa. 15 Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.

Rasuwar Rahila

16 Da suka tashi daga Betel, tun suna da 'yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu. 17 Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.” 18 Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu. 19 Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato, Baitalami. 20 Yakubu ya kafa al'amudi bisa kabarinta, al'amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau. 21 Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.

'Ya'yan Yakubu Maza

22 A lokacin da Isra'ila ke zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari. 'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne. 23 'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna. 24 'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu. 25 'Ya'yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali. 26 'Ya'yan Zilfa, kuyangar Lai'atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne 'ya'yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.

Rasuwar Ishaku

27 Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato, Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci. 28 Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin. 29 Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, 'ya'yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.

Farawa 36

Zuriyar Isuwa

1 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato, Edom. 2 Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan'aniyawa, wato, Ada 'yar Elon Bahitte, da Oholibama 'yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye, 3 da Basemat, 'yar Isma'ilu, 'yar'uwar Nebayot. 4 Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel. 5 Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan'ana. 6 Isuwa ya kwashi matansa, da 'ya'yansa mata da maza, da dukan jama'ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan'ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu. 7 Gama abin mallakarsu ya yi yawa har ba zai yiwu su zama tare ba, ƙasar baƙuntarsu kuwa ba ta wadace su ba saboda yawan dabbobinsu. 8 Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom. 9 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai. 10 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato, Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa. 11 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz. 12 Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa. 13 Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa. 14 Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora. 15 Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga 'ya'yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz, 16 da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada. 17 Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa. 18 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa. 19 Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato, Edom, da shugabanninsu.

Zuriyar Seyir

20 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 21 da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom. 22 'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce. 23 Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam. 24 Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon. 25 Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana. 26 Waɗannan su ne 'ya'yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran. 27 Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilha, da Zayawan, da Akan. 28 Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran. 29 Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 30 da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.

Sarakunan Edom

31 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa. 32 Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba. 33 Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa. 34 Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa. 35 Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne. 36 Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa. 37 Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa. 38 Da Shawul ya rasu, sai Ba'al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa. 39 Da Ba'al-hanan ɗan Akbor ya rasu, sai Hadad ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetebel 'yar Matred, 'yar Mezahab. 40 Waɗannan su ne sunayen sarakunan Isuwa bisa ga dangoginsu da bisa ga wurin zamansu. Ga sunayensu, sarki Timna, da Alwa, da Yetet, 41 da Oholibama, da Ila, da Finon, 42 da Kenaz, da Teman, da Mibzar, 43 da Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne sarakunan Edom, (wato, Isuwa ne kakan Edomawa) bisa ga wuraren zamansu a ƙasar mallakarsu.

Farawa 37

1 Yakubu ya zauna a ƙasar Kan'ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci. 2 Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.

Yusufu da 'Yan'uwansa

Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa, 3 Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da ko wannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado. 4 Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi. 5 Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6 Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi. 7 Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.” 8 'Yan'uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa. 9 Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.” 10 Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?” 11 'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.

An Sayar da Yusufu zuwa Masar

12 Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem, 13 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.” Sai ya ce masa, “Ga ni.” 14 Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron. Da Yusufu ya isa Shekem, 15 wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?” 16 Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.” 17 Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun 'yan'uwansa, ya kuwa same su a Dotan. 18 Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi. 19 Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa. 20 Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.” 21 Amma sa'ad da Ra'ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa. 22 Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyar nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu. 23 Don haka, sa'ad da Yusufu ya zo wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa. 24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki. 25 Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma'ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar. 26 Yahuza ya ce wa 'yan'uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan'uwanmu, muka ɓoye jininsa? 27 Ku zo mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan'uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” 'Yan'uwansa suka yarda da shi. 28 Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar. 29 Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa, 30 ya koma wurin 'yan'uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?” 31 Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin. 32 Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?” 33 Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.” 34 Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa. 35 Dukan 'ya'yansa mata da maza suka tashi domin su ta'azantar da shi, amma ya ƙi ta'azantuwa, yana cewa, “A'a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa. 36 A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir'auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir'auna.

Farawa 38

Yahuza da Tamar

1 Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar 'yan'uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba'adullame mai suna Hira. 2 A can, sai Yahuza ya ga 'yar wani Bakan'ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta, 3 ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er. 4 Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan. 5 Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela. 6 Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar. 7 Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi. 8 Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.” 9 Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya. 10 Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi. 11 Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta. 12 A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame. 13 Sa'ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,” 14 sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba. 15 Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta. 16 Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce. Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?” 17 Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.” Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?” 18 Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?” Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki. 19 Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba. 20 Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba. 21 Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?” Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.” 22 Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ” 23 Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.” 24 Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.” Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.” 25 Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.” 26 Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba. 27 Sa'ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne. 28 Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.” 29 Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan'uwansa ya fito, sai ta ce, “A'a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa. 30 Daga baya ɗan'uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.

Farawa 39

Yusufu da Matar Fotifar

1 Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir'auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma'ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can. 2 Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren. 3 Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka. 4 Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi. 5 Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji. 6 Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci. Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani. 7 Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.” 8 Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna. 9 Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” 10 Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba. 11 Amma wata rana, sa'ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan, 12 sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita. 13 Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje, 14 sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba'ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi. 15 Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.” 16 Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo. 17 Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina, 18 amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.” 19 Sa'ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata. 20 Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda 'yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku. 21 Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun. 22 Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan 'yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi. 23 Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.

Farawa 40

Yusufu ya Fassara Mafarkan 'Yan Kurkuku

1 Bayan waɗannan al'amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi. 2 Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya. 3 Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato, kurkuku inda Yusufu yake a tsare. 4 Shugaban 'yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe. 5 Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin. 6 Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu. 7 Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?” 8 Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.” 9 Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana. 10 A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi. 11 Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.” 12 Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne, 13 bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa. 14 Amma ka tuna da ni sa'ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir'auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida. 15 Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.” 16 Sa'ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina. 17 A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir'auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato, wanda yake bisa kaina ɗin.” 18 Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne, 19 bayan kwana uku Fir'auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.” 20 A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa. 21 Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna, 22 amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu. 23 Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.

Farawa 41

Yusufu ya Fassara wa Fir'auna Mafarkansa

1 Bayan shekaru biyu cif, Fir'auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu, 2 sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa. 3 Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu. 4 Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir'auna ya farka. 5 Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara guda. 6 Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar. 7 Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir'auna ya farka, ashe, mafarki ne. 8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su. 9 Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir'auna, “Yau, na tuna da laifofina. 10 Sa'ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, 11 muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin. 12 Akwai wani Ba'ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa'ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa ko wannenmu fassara bisa kan mafarkinsa. 13 Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.” 14 Sai Fir'auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir'auna. 15 Fir'auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.” 16 Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.” 17 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu, 18 ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa. 19 Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu. 20 Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko, 21 amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka. 22 Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda, 23 zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu. 24 Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.” 25 Yusufu ya ce wa Fir'auna, “Mafarkin Fir'auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa. 26 Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne. 27 Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa. 28 Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir'auna, Allah ya nuna wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa. 29 Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka, 30 amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar. 31 Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar. 32 Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa, Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba. 33 “Yanzu fa bari Fir'auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar. 34 Bari Fir'auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi. 35 Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir'auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi. 36 Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”

An Naɗa Yusufu Mai Mulki a Masar

37 Fir'auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara. 38 Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?” 39 Domin haka Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka, 40 za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama'ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.” 41 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.” 42 Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya, 43 ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar. 44 Har yanzu dai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir'auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.” 45 Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar. 46 Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar. 47 A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske, 48 sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi. 49 Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa. 50 Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu 'ya'ya biyu maza, waɗanda Asenat 'yar Fotifera, firist na On ta haifa masa. 51 Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.” 52 Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.” 53 Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika, 54 aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci. 55 Sa'ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir'auna kuka domin abinci, sai Fir'auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.” 56 Domin haka sa'ad da yunwar ta bazu ko'ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar. 57 Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.

Farawa 42

'Yan'uwan Yusufu sun Zo Masar Sayen Abinci

1 A sa'ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa 'ya'yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido? 2 Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.” 3 Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar. 4 Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.” 5 Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana. 6 Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 7 Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.” 8 Yusufu kuwa ya gane da 'yan'uwansa amma su ba su gane shi ba. 9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.” 10 Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo. 11 Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.” 12 Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.” 13 Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.” 14 Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku. 15 Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan. 16 Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan'uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir'auna, lalle ku magewaya ne.” 17 Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku. 18 A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah, 19 sai ku bar ɗan'uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata, 20 sa'an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi. 21 Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.” 22 Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.” 23 Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu. 24 Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.

'Yan'uwan Yusufu suka Komo Kan'ana

25 Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu. 26 Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi. 27 Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa. 28 Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!” Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?” 29 Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa, 30 “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa. 31 Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne. 32 Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.’ 33 “Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku. 34 Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan'uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ” 35 Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin ko wannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana. 36 Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.” 37 Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.” 38 Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”

Farawa 43

'Yan'uwan Yusufu sun Sāke Komawa Masar da Biliyaminu

1 A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar. 2 Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.” 3 Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’ 4 In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci. 5 Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan'uwanku ba.’ ” 6 Sai Isra'ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan'uwa?” 7 Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan'uwanku?’ ” 8 Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu. 9 Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada, 10 gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.” 11 Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure. 12 Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi. 13 Ku kuma ɗauki ɗan'uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin. 14 Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.” 15 Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu. 16 Sa'ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.” 17 Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu. 18 Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.” 19 Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida, 20 suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci, 21 amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin ko wannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su, 22 ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.” 23 Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu. 24 Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna, 25 sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan. 26 Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 27 Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?” 28 Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a. 29 Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri, ɗana!” 30 Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan'uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka. 31 Sa'an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci. 32 Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. 33 Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. 34 Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na ko wannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

Farawa 44

Finjalin Yusufu a Taikin Biliyaminu

1 Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa, 2 ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa. 3 Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu. 4 Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu, 5 ‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne maigidana ke sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.’ ” 6 Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu. 7 Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan! 8 Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan'ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka? 9 Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.” 10 Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.” 11 Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa. 12 Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu. 13 Suka kyakkece rigunansu, ko wannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin. 14 Sa'ad da Yahuza da 'yan'uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa. 15 Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?” 16 Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.” 17 Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.” 44 .18 Yahuza ya yi G�d� domin Biliyaminu Yahuza ya yi G�d� domin Biliyaminu 18 Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir'auna kake. 19 Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?’ 20 Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’ 21 Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’ 22 Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’ 23 Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’ 24 “Sa'ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce. 25 Don haka sa'ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’ 26 sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’ 27 Sa'an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani 'ya'ya biyu matata ta haifa mini, 28 ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba. 29 In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’ 30-31 “Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. 32 Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina dukan raina.’ 33 Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da 'yan'uwansa. 34 Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”

Farawa 45

Yusufu ya Bayyana Kansa ga 'Yan'uwansa

1 Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa'ad da Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa. 2 Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir'auna. 3 Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma 'yan'uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa. 4 Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan'uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar. 5 Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai. 6 Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. 7 Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa. 8 Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka. 9 “Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, ‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata. 10 Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da 'ya'yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi. 11 A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.” ’ 12 Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan'uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa, bakina ne yake magana da ku. 13 Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.” 14 Sai Yusufu ya rungumi ɗan'uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu. 15 Ya sumbaci 'yan'uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai 'yan'uwansa suka yi taɗi da shi. 16 Sa'ad da labari ya kai gidan Fir'auna cewa, “'Yan'uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir'auna da fādawansa daɗi ƙwarai. 17 Sai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa 'yan'uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan'ana. 18 Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’ 19 Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo. 20 Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ” 21 Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya. 22 Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar. 23 Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa. 24 Ya sallami 'yan'uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.” 25 Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan'ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu. 26 Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba. 27 Amma sa'ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa'ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo. 28 Isra'ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

Farawa 46

Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar

1 Isra'ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku. 2 Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.” 3 Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma. 4 Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.” 5 Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su. 6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka, 7 'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar. 8 Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato, Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu. 9 'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. 10 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya. 11 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari. 12 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul. 13 'Ya'yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron. 14 'Ya'yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel, 15 (waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne). 16 'Ya'yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli. 17 'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel. 18 Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai'atu, 'yarsa. 19 'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu. 20 Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar. 21 'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar. 22 Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila. 23 Hushim shi ne ɗan Dan. 24 'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. 25 Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila. 26 Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne. 27 'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.

Yakubu da Iyalinsa a Masar

28 Isra'ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen, 29 sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra'ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa. 30 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.” 31 Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir'auna, in ce masa, ‘'Yan'uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā suke a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina, 32 mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’ 33 To, sa'ad da Fir'auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana'arku?’ 34 Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna 'yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

Farawa 47

1 Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir'auna, ya ce, “Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan'ana, yanzu suna ƙasar Goshen.” 2 Daga cikin 'yan'uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir'auna. 3 Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?” Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.” 4 Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.” 5 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka. 6 Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.” 7 Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka. 8 Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?” 9 Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.” 10 Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna. 11 Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta. 12 Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.

Hidimar Yusufu a Lokacin Yunwa

13 A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar. 14 Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna. 15 Sa'ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan'ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.” 16 Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.” 17 Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara. 18 Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa, kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana. 19 Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.” 20 Ta haka Yusufu ya saya wa Fir'auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir'auna. 21 Yusufu ya mai da jama'ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan. 22 Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba. 23 Yusufu ya ce wa jama'ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir'auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin. 24 Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir'auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na 'yan ƙanananku.” 25 Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir'auna.” 26 Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.

Wasiyyar Yakubu

27 Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai. 28 Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato, shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai. 29 A sa'ad da lokaci ya gabato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar, 30 amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.” Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.” 31 Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa'an nan sai Isra'ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

Farawa 48

Yakubu ya Sa wa Ifraimu da Manassa Albarka

1 Ya zama fa bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Yusufu, “Ga mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki 'ya'yansa biyu maza, Manassa da Ifraimu ya tafi ya gai da mahaifinsa. 2 Sa'ad da aka ce wa Yakubu, “Ɗanka Yusufu ya zo wurinka,” sai Yakubu ya ƙoƙarta ya tashi zaune a kan gadon. 3 Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan'ana ya sa mini albarka, 4 ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’ 5 Yanzu fa, a kan waɗannan 'ya'yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra'ubainu da Saminu suke. 6 'Ya'ya waɗanda za a haifa a bayansu za su zama naka, za a kira su da sunan 'yan'uwansu cikin gādonsu. 7 Sa'ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan'ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato, Baitalami. 8 Sa'ad da Isra'ila ya ga 'ya'yan Yusufu, maza, ya ce, “Suwane ne waɗannan?” 9 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “'Ya'yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.” Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.” 10 Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su. 11 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.” 12 Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa. 13 Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra'ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra'ila, ya kawo su kusa da shi. 14 Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari. 15 Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka. 16 Mala'ikan da ya fanshe ni Daga dukan mugunta, Ya sa wa samarin albarka, Bari a dinga ambatarsu da sunana, Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena, Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama taron jama'a a tsakiyar duniya.” 17 Sa'ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa. 18 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “Ba haka ba ne baba, gama wannan ne ɗan fari. Sa hannunka na dama a bisa kansa.” 19 Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al'umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al'ummai.” 20 Ya sa musu albarka a wannan rana, yana cewa, “Ta gare ku Isra'ila za su sa albarka da cewa, ‘Allah ya maishe ku kamar Ifraimu da Manassa.’ ” Da haka ya sa Ifraimu gaba da Manassa. 21 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka. 22 Ni ne nake ba ka Shekem, kashi ɗaya fiye da 'yan'uwanka, wanda na ƙwace da takobina da bakana daga hannun Amoriyawa.”

Farawa 49

Faɗar Yakubu a kan 'Ya'yansa

1 Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa. 2 “Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yan Yakubu, maza, Ku kuma kasa kunne ga Isra'ila mahaifinku. 3 “Ra'ubainu, kai ɗan farina ne, ƙarfina, Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi ƙarfi duka cikin 'ya'yana. 4 Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi. 5 “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne, Suka mori takubansu cikin ta da hankali. 6 Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba, Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu ba, Gama cikin fushinsu suka kashe mutane, Cikin gangancinsu kuma suka gurgunta bijimai. 7 La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa. 8 “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka. 9 Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi. 10 Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i. 11 Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini. 12 Idanunsa za su yi ja wur saboda shan ruwan inabi, Haƙoransa kuma su yi fari fat saboda shan madara. 13 “Zabaluna zai zauna a gefen teku, Zai zama tashar jiragen ruwa, Kan iyakarsa kuma zai kai har Sidon. 14 “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa, Ya kwanta a miƙe tsakanin jakunkunan shimfiɗa. 15 Saboda ya ga wurin hutawa ne mai kyau, Ƙasar kuma mai kyau ce, Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin ɗaukar kaya, Ya zama bawa, yana yin aiki mai wuya. 16 “Dan zai zama mai mulki ga mutanensa Kamar ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila. 17 Dan zai zama maciji a gefen hanya, Zai zama kububuwa a gefen turba, Mai saran diddigen doki Don mahayin ya fāɗi da baya. 18 “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji. 19 “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari, Shi kuwa zai runtume su. 20 “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfani mai yawa, Zai kuma yi tanadin abincin da ya dace da sarki. 21 “Naftali sakakkiyar barewa ce, Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya. 22 “Yusufu jakin jeji ne, Jakin jeji a gefen maɓuɓɓuga Aholakan jeji a gefen tuddai. 23 Maharba suka tasar masa ba tausayi Suka fafare shi da kwari da baka. 24 Duk da haka bakunansu sun kakkarye. Damatsansu sun yayyage Ta wurin ikon Allah Mai Girma na Yakubu, Makiyayi, Dutse na Isra'ila. 25 Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa. 26 Albarkun hatsi da na gari Albarkun daɗaɗɗun duwatsu, Abubuwan jin daɗi na madawwaman tuddai, Allah ya sa su zauna a kan Yusufu, Da a goshin wanda aka raba shi da 'yan'uwansa. 27 “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa, Da safe yakan cinye abin da ya kaso, Da maraice kuma yakan raba abin da ya kamo.” 28 Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa ko wannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.

Rasuwar Yakubu da Jana'izarsa

29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte, 30 a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 31 A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu. 32 Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.” 33 Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.

Farawa 50

1 Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi. 2 Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra'ila da maganin hana ruɓa. 3 Suka ɗauki kwana arba'in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba'in. 4 Sa'ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir'auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir'auna, ku ce masa, 5 ‘Sa'ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa, zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan'ana.’ Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa'an nan in komo.” 6 Fir'auna ya amsa, ya ce, “Ka haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya rantsar da kai.” 7 Saboda haka, Yusufu ya haura ya binne mahaifinsa, tare da shi kuma dukan barorin Fir'auna suka haura, da dattawan gidan Fir'auna, da dukan dattawan ƙasar Masar, 8 da kuma dukan iyalin gidan Yusufu, da 'yan'uwansa, da iyalin gidan mahaifinsa. Sai 'yan ƙananansu, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanunsu, aka bari a ƙasar Goshen. 9 Da karusai da mahayan dawakai kuma suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiya ce ƙwarai. 10 Sa'ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa. 11 Sa'ad da Ka'aniyawa mazaunan ƙasar, suka ga makokin da aka yi a farfajiyar masussukar Atad, sai suka ce, “Wannan makoki mai zafi ne ga Masarawa.” Don haka aka sa wa wurin suna Abel-mizrayim, wanda yake wajen Urdun. 12 Haka 'ya'yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta, 13 gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 14 Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da 'yan'uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana'izar mahaifinsa.

Yusufu ya Tabbatar wa 'Yan'uwansa ba zai Rama Ba

15 Sa'ad da 'yan'uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.” 16 Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa, 17 ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi. 18 'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.” 19 Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba. 20 A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau. 21 Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta'azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.

Rasuwar Yusufu

22 Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya. 23 Yusufu fa ya ga 'ya'yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi 'ya'yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu. 24 Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” 25 Sa'an nan Yusufu ya rantse wa 'ya'yan Isra'ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.” 26 Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.

Fitowa 1

Wahalar Isra'ilawa a Masar

1 Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa. 2 Su ne Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, 3 da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu, 4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru. 5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar. 6 Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara. 7 Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar. 8 A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba. 9 Sai ya ce wa mutanensa, “Duba, jama'ar Isra'ila sun cika yawa sun fi ƙarfinmu. 10 Zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su riɓaɓɓanya, domin in aka faɗa mana da yaƙi, kada su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su tsere daga ƙasar.” 11 Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato, Fitom da Ramases. 12 Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra'ilawa. 13 Suka kuma tilasta wa Isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani. 14 Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu. 15 Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a, 16 “Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.” 17 Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar 'ya'ya maza da rai. 18 Don haka Sarkin Masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, “Me ya sa kuka bar 'ya'ya maza da rai?” 19 Ungozomar suka ce wa Fir'auna, “Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba.” 20 Allah kuwa ya yi wa ungozomar nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai. 21 Allah kuma ya ba ungozomar nan zuriya domin sun ji tsoronsa. 22 Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”

Fitowa 2

Haihuwar Musa

1 Sai wani mutum, Balawe, ya auro 'yar Lawi. 2 Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku. 3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu. 4 Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi. 5 Gimbiya, wato, 'yar Fir'auna, ta gangaro don ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi. 6 Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne.” 7 'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?” 8 Sai Gimbiya ta ce mata, “Je ki.” Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn. 9 Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, “Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki.” Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa. 10 Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, “Domin na tsamo shi daga cikin ruwa.”

Musa ya Gudu zuwa Madayana

11 Ana nan wata rana, sa'ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana d�kan Ba'ibrane, ɗaya daga cikin 'yan'uwansa. 12 Da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe Bamasaren, ya turbuɗe shi cikin yashi. 13 Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan'uwansa, “Me ya sa kake bugun ɗan'uwanka?” 14 Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?” Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al'amarin!” 15 Da Fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir'auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya. 16 Ana nan waɗansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa don su shayar da garken mahaifinsu. 17 Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu. 18 Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato, Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?” 19 Sai suka ce, “Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu.” 20 Reyuwel kuwa ya ce wa 'ya'yansa mata, “A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci.” 21 Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora. 22 Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.” 23 Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah. 24 Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 25 Allah ya dubi jama'ar Isra'ila, ya kuwa kula da su.

Fitowa 3

Allah ya Kira Musa

1 Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato, dutsen Allah. 2 A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba. 3 Musa kuwa ya ce, “Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.” 4 Sa'ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, “Musa, Musa.” Musa ya ce, “Ga ni.” 5 Allah kuwa ya ce, “Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne.” 6 Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato, Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah. 7 Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu, 8 don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato, ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 9 Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su. 10 Zo, in aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da jama'ata, wato, Isra'ilawa, daga cikin Masar.” 11 Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir'auna in fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?” 12 Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa, ni ne na aike ka. Sa'ad da ka fito da jama'ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.” 13 Sai Musa ya ce wa Allah, “Idan na je wurin Isra'ilawa na ce musu, ‘Allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,’ idan sun ce mini, ‘Yaya sunansa?’ Me zan faɗa musu?” 14 Allah kuwa ya ce wa Musa, “NI INA NAN YADDA NAKE,” ya kuma ce, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘NI NE ya aiko ni gare ku.’ ” 15 Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato, na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai. 16 Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato, na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar. 17 Ya yi alkawari cewa, zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’ 18 Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’ 19 Amma na sani Sarkin Masar ba zai bar ku ku fita ba, sai an yi masa tilas. 20 Domin haka zan miƙa hannuna in bugi Masar da dukan mu'ujizaina waɗanda zan aikata cikinta, sa'an nan zai bar ku ku fita. 21 “Zan sa wannan jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa'ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba. 22 Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa 'ya'yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”

Fitowa 4

1 Musa kuwa ya amsa ya ce, “Ai, ba za su gaskata ni ba, ba kuma za su kasa kunne ga maganata ba, gama za su ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba.’ ” 2 Amma Ubangiji ya ce masa, “Mene ne wannan a hannunka?” Ya ce, “Sanda ne.” 3 Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Sai ya jefa shi ƙasa, sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya yi gudunsa. 4 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka ka kama wutsiyarsa.” Ya miƙa hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa. 5 Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato, na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.” 6 Sai Ubangiji ya sāke ce masa, “Sa hannunka cikin ƙirjinka.” Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannunsa a kuturce fari fat. 7 Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa. 8 Ubangiji kuma ya ce, “Idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu'ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun. 9 Idan ba su gaskata mu'ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka ɗibi ruwa daga Kogin Nilu, ka zuba bisa busasshiyar ƙasa. Ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasa.” 10 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.” 11 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne? 12 Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.” 13 Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.” 14 Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa. 15 Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi. 16 Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi. 17 Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”

Musa ya Koma Masar

18 Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.” Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.” 19 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu. 20 Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa. 21 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita. 22 Za ka ce wa Fir'auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra'ila ɗan fārina ne. 23 Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.’ ” 24 Ya zama kuwa sa'ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi. 25 Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.” 26 Sa'an nan Ubangiji ya ƙyale shi. Ta kuma ce, “Kai angon jini ne,” saboda kaciyar. 27 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi. 28 Sa'an nan Musa ya faɗa wa Haruna abubuwan da Ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu'ujizan da ya umarce shi ya aikata. 29 Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra'ila. 30 Haruna dai ya hurta wa dattawan al'amuran da Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuma aikata mu'ujizan a idanunsu. 31 Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.

Fitowa 5

Musa da Haruna sun Tafi gaban Fir'auna

1 Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.’ ” 2 Amma Fir'auna ya ce, “Wane ne Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra'ilawa su tafi? Ai, ban san Ubangiji ɗin nan ba, balle in bar Isra'ilawa su tafi.” 3 Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.” 4 Amma Sarkin Masar ya ce wa Musa da Haruna, “Me ya sa kuke hana jama'ar yin aikinsu? Ku tafi wurin aikin gandunku.” 5 Ya kuwa ci gaba ya ce, “Ga jama'ar ƙasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu.” 6 A ran nan fa Fir'auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama'a, ya ce, 7 “Nan gaba kada ku ƙara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. Ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu. 8 Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, ‘A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.’ 9 Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba.” 10 Sai shugabannin aikin gandu da manyan jama'a suka tafi suka faɗa wa jama'a cewa, “Ga abin da Fir'auna ya ce, ‘Ba zan ba ku budu ba. 11 Ku je, ku da kanku, ku nemi budu inda duk za ku iya samowa, amma daɗai, ba za a sawwaƙe muku aikinku ba.’ ” 12 Sai jama'a suka watsu ko'ina cikin ƙasar Masar, suna tattara budu. 13 Shugabannin aikin gandun suka matsa musu, suna cewa, “Sai ku cika aikinku na kowace rana daidai yadda kuke yi a dā lokacin da ake ba ku budu.” 14 Aka kuwa bulali manya waɗanda suke Isra'ilawa waɗanda shugabannin aikin gandu na Fir'auna suka sa a bisa Isra'ilawa, ana cewa, “Me ya sa jiya da yau ba ku cika yawan tubalin da aka ƙayyade, kamar dā ba?” 15 Manyan Isra'ilawa kuwa suka tafi suka yi kuka a gaban Fir'auna, suka ce, “Me ya sa ka yi wa bayinka haka? 16 Ba a ba mu budu, amma ana ce mana mu yi tubali. Ga shi ma, d�kan bayinka suke yi. Ai, jama'arka ne suke da laifin.” 17 Fir'auna kuwa ya ce musu, “Ku ragwaye ne ƙwarai, shi ya sa kuke cewa, a bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji hadaya. 18 Ku tafi, ku kama aiki, ba za a ba ku budu ba, duk da haka za ku cika yawan tubali da aka sa muku.” 19 Manyan Isra'ilawa suka ga lalle sun shiga uku, da yake aka ce dole su cika yawan tubali da aka yanka musu kowace rana. 20 Da suka fita daga gaban Fir'auna, sai suka sadu da Musa da Haruna, suna jiransu. 21 Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”

Addu'ar Musa

22 Sai Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangijina, me ya sa ka jawo wa wannan jama'a masifa? Me ya sa ka aike ni? 23 Gama tun da na tafi wurin Fir'auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama'a, kai kuwa ba ka ceci jama'arka ba ko kaɗan!”

Fitowa 6

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”

An Sāke Kiran Musa

2 Allah kuma ya yi magana da Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji. 3 Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba. 4 Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci. 5 Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina. 6 Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku. 7 Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa. 8 Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ” 9 Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta. 10 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 11 “Tafi gaban Fir'auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.” 12 Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra'ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?” 13 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra'ilawa da wurin Fir'auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar.

Asalin Musa da Haruna

14 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu. 15 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan'aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu. 16 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai. 17 'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu. 18 'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku. 19 'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu. 20 Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai. 21 'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri. 22 'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri. 23 Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 24 'Ya'ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora. 25 Ele'azara, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Futiyel. Ita kuwa ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan kabilar Lawi bisa ga kabilansu. 26 Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya. 27 Su ne waɗanda suka yi magana da Sarkin Masar ya bar Isra'ilawa su fita daga Masar. Musa da Haruna ne suka yi wannan.

Umarnin Ubangiji ga Musa da Haruna

28 Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce, 29 “Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.” 30 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”

Fitowa 7

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, zan maishe ka kamar Allah ga Fir'auna. Ɗan'uwanka, Haruna kuwa, zai zama manzonka. 2 Kai za ka faɗa wa Haruna, ɗan'uwanka, dukan abin da na umarce ka, shi kuwa zai faɗa wa Fir'auna ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa. 3 Amma zan taurare zuciyar Fir'auna don in aikata alamu da mu'ujizai cikin ƙasar Masar. 4 Amma Fir'auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama'ata, wato, Isra'ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko. 5 Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra'ilawa daga tsakiyarsu.” 6 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. 7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa'ad da suka yi magana da Fir'auna.

Sandan Haruna

8 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 9 “Idan Fir'auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al'ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir'auna. Sandan kuwa zai zama maciji.” 10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir'auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji. 11 Fir'auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa. 12 Ko wannensu ya jefa sandansa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. 13 Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Jini

14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna yana da taurin zuciya, ga shi, ya ƙi sakin jama'ar. 15 Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji. 16 Za ka faɗa wa Fir'auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa, ka saki jama'ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba. 17 Ubangiji ya ce, za ka sani shi ne Ubangiji ta wurin abin da zan aikata. Zan bugi ruwan Nilu da sandan da yake hannuna, ruwan kuwa zai rikiɗe ya zama jini. 18 Kifayen da suke cikin Nilu za su mutu. Nilu kuwa zai yi ɗoyi, har da Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’ ” 19 Ubangiji kuma ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa ya miƙa shi a bisa ruwayen Masar, da kogunansu, da rafuffukansu, da fadamunsu, da dukan tafkunansu don ruwansu ya zama jini. Jini zai kasance ko'ina a ƙasar Masar, i, har ma cikin randuna. 20 Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir'auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini. 21 Kifayen da suke cikin Nilu suka mutu. Nilu kuwa ya yi ɗoyi, har Masarawa ba su iya shan ruwansa ba. Ko'ina kuma a ƙasar Masar akwai jini. 22 Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir'auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. 23 Sai ya juya, ya koma fādarsa, bai ko kula da abin da aka yi ba. 24 Dukan Masarawa suka tattone ramummuka a bakin Nilu, suna neman ruwan sha, gama ba su iya shan ruwan Nilu ba. 25 Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.

Fitowa 8

Annobar Kwaɗi

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir'auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama'arsa domin su yi masa sujada. 2 Idan ka ƙi sakinsu, zai hore ka da kwaɗi. 3 Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama'arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka, 4 har ma za su hau bisa kanka, da jama'arka, da dukan fādawanka.’ ” 5 Sai Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa sandansa a bisa koguna, da rufuffuka, da tafkuna don ya sa kwaɗi su fito, su rufe ƙasar Masar. 6 Haruna ya miƙa sandansa a bisa ruwayen Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka rufe ƙasar Masar. 7 Masu sihiri kuma suka sa kwaɗi su fito a bisa ƙasar Masar ta wurin sihirinsu. 8 Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya. 9 Musa ya ce wa Fir'auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama'arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?” 10 Fir'auna ya ce, “Gobe ne.” Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu. 11 Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama'arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.” 12 Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir'auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir'auna. 13 Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu. 14 Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi. 15 Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Kwarkwata

16 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar. 17 Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa 'yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko'ina cikin ƙasar Masar. 18 Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe 'yan adam da dabbobi. 19 Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Ƙudaje

20 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada. 21 In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa. 22 A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama'ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya. 23 Zan sa iyaka tsakanin jama'ata da jama'arka. Gobe ne wannan mu'ujiza za ta auku.’ ” 24 Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir'auna, da gidan fādawansa, da ko'ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje. 25 Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasar nan.” 26 Amma Musa ya ce, “Ba zai kyautu a yi haka ba, gama irin dabbobin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadaya da su, haramu ne ga Masarawa. Idan fa muka miƙa hadaya da waɗannan dabbobi da suke haramu a idon Masarawa za su jajjefe mu da duwatsu. 27 Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.” 28 Sai Firauna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya a jeji, sai dai kada ku tafi da nisa. Ku kuma yi mini addu'a.” 29 Musa kuwa ya ce, “Nan da nan da tashina daga gabanka, zan yi addu'a ga Ubangiji, ƙudajen kuwa za su rabu da kai, da fādawanka, da jama'arka gobe, kada ka sāke yin ruɗi, ka ƙi barin jama'ar su tafi, su miƙa wa Ubangiji hadaya.” 30 Musa ya fita daga wurin Fir'auna, ya roƙi Ubangiji. 31 Ubangiji kuwa ya aikata bisa ga roƙon Musa. Ƙudajen suka rabu da Fir'auna, da fādawansa, da jama'arsa. Ko ƙuda ɗaya bai ragu ba. 32 Duk da haka Fir'auna ya taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, ya ƙi sakin jama'ar.

Fitowa 9

Mutuwar Dabbobi

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, ka faɗa masa cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada. 2 Amma idan ka ƙi sakinsu, wato, kana ta riƙonsu, 3 to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani. 4 Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin. 5 Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.’ ” 6 Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba. 7 Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.

Marurai

8 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir'auna. 9 Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.” 10 Sa'an nan suka ɗauko toka daga matoya, suka tsaya a gaban Fir'auna. Da Musa ya watsa ta sama, sai ta zama marurai suna ta fitowa a jikin mutum da dabba. 11 Amma masu sihirin suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran, gama suka kamu da maruran kamar sauran Masarawa. 12 Ubangiji kuma ya taurare zuciyar Fir'auna har ya ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa wa Musa.

Ƙanƙara

13 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada. 14 A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama'arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya. 15 Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama'arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf. 16 Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya. 17 Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba. 18 Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu. 19 Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato, wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.’ ” 20 Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir'auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida. 21 Amma waɗanda ba su kula da abin da Ubangiji ya faɗa ba, suka bar bayinsu da dabbobinsu a waje cikin saura. 22 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa mutum da dabba da bisa dukan itatuwan saura a dukan ƙasar Masar.” 23 Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar. 24 Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma. 25 Ƙanƙarar ta bugi ko'ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da suke a saura aka ragargaza su. 26 Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra'ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba. 27 Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure. 28 Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.” 29 Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce. 30 Amma dai na sani, da kai da fādawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.” 31 Rama da sha'ir suka lalace, gama sha'ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana huda. 32 Amma alkama da maiwa ba su lalace ba, gama kakarsu ba ta yi ba tukuna. 33 Sai Musa ya fita daga wurin Fir'auna ya rabu da birnin. Ya yi addu'a ga Ubangiji sai walƙiya da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. 34 Da Fir'auna ya ga an ɗauke ruwa, da ƙanƙara, da kuma walƙiya, sai ya sāke yin zunubi, ya taurare zuciyarsa, da shi da fādawansa. 35 Zuciyar Fir'auna ta taurare, har ya ƙi sakin Isra'ilawa kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta bakin Musa.

Fitowa 10

Fara

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu'ujizai nawa a tsakiyarsu, 2 domin kuma ka sanar da 'ya'yanka da jikokinka yadda na shashantar da Masarawa, na kuma aikata waɗannan mu'ujizai a tsakiyarsu. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.” 3 Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada. 4 In kuwa ka ƙi yarda ka bar jama'ata su tafi, to, gobe zan aiko da fara cikin ƙasarka, 5 za ta rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za ta cinye sauran abin da ya kuɓuta daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a ƙasar. 6 Za su cika fādarka, da dukan gidajen fādawanka, da na dukan Masarawa. Iyayenka da kakanninka ba su taɓa ganin irin farar nan ba, tun daga ran da suke ƙasar, har wa yau.’ ” Sai ya juya ya fita daga gaban Fir'auna. 7 Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?” 8 Aka komar da Musa da Haruna gaban Fir'auna. Sai Fir'auna ya ce musu, “Ku tafi ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?” 9 Musa ya amsa, “Da samarinmu, da tsofaffinmu za mu tafi, da 'ya'yanmu mata da maza za su fita tare da mu, da kuma garkunanmu da shanunmu, gama wajibi ne mu yi idi a gaban Ubangiji.” 10 Fir'auna ya ce musu, “To, Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba, gama kuna da niyyar mugunta a zuciyarku. 11 Sai dai ku mazaje, ku tafi ku bauta wa Ubangiji, gama abin da kuke so ke nan.” To, aka kore su daga gaban Fir'auna. 12 Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa ƙasar Masar domin fara ta zo. Farar kuwa za ta rufe ƙasar Masar, ta cinye duk tsire-tsire da ganyayen da suke cikin ƙasar, da iyakar abin da ƙanƙara ta rage.” 13 Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar. 14 Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba. 15 Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar. 16 Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku. 17 Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.” 18 Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji. 19 Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba. 20 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.

Duhu

21 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.” 22 Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar. 23 Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune. 24 Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya ce musu, “Ku tafi ku bauta wa Ubangiji, sai dai ku bar tumakinku, da awakinku, da shanunku a nan, amma ku ku tafi da 'ya'yanku.” 25 Musa kuwa ya ce, “In haka ne, kai ka ba mu abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadayu da su. 26 Don haka sai mu tafi da dabbobinmu, ko kofato ba za a bari a baya ba, gama daga cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.” 27 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna har bai yarda ya sake su ba. 28 Fir'auna ma ya ce wa Musa, “Tafi, ka ba ni wuri, ka mai da hankali fa, kada in ƙara ganinka, gama ran da na sāke ganinka ran nan kā mutu.” 29 Sai Musa ya amsa ya ce, “Haka nan ne kuwa, ba zan ƙara ganin fuskarka ba.”

Fitowa 11

Musa ya Hurta Mutuwar 'Ya'yan Fari

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir'auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa'ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku. 2 Sai ka faɗa wa jama'a, kowane mutum da kowace mace su roƙi kayan ado na azurfa da na zinariya daga wurin maƙwabtansu.” 3 Ubangiji kuwa ya sa jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa. Musa kuwa ya zama babban mutum a ƙasar Masar a gaban fādawan Fir'auna da kuma gaban jama'ar. 4 Musa ya ce wa Fir'auna, “Ga abin da Ubangiji ya faɗa, ‘A wajen tsakar dare zan ratsa cikin Masar. 5 Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu. 6 Za a kuwa yi kuka mai zafi ko'ina a ƙasar Masar irin wanda ba a taɓa yi ba, ba kuma za a ƙara yi ba. 7 Amma ko kare ba zai yi wa wani mutum ko dabba na Isra'ila haushi ba, domin ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.’ 8 Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace. 9 Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna ba zai kasa kunne gare ka ba, sai na ƙara aikata waɗansu mu'ujizai cikin ƙasar Masar.” 10 Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu'ujizai a gaban Fir'auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa saki Isra'ilawa daga ƙasarsa ba.

Fitowa 12

Idin Ketarewa

1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar, 2 wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su. 3 A faɗa wa dukan taron Isra'ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida. 4 Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu. 5 Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki. 6 Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice. 7 Sa'an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin. 8 A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci. 9 Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin. 10 Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11 Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji. 12 A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji. 13 Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa'ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar. 14 Ranar nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada. 15 “Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila. 16 A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci. 17 Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada. 18 Za ku ci abinci marar yisti da maraice a kan rana ta goma sha huɗu ga wata na fari, har zuwa rana ta ashirin da ɗaya ga watan da maraice. 19 Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama'ar Isra'ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar. 20 Dukan abin da yake da yisti ba za ku ci shi ba, wato, sai abinci marar yisti ne kaɗai za ku ci a dukan gidajenku.” 21 Musa ya kirayi dattawan Isra'ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa. 22 Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe. 23 Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa'ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba. 24 Za ku kiyaye waɗannan ka'idodi, ku riƙe su farilla, ku da 'ya'yanku har abada. 25 Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla. 26 Sa'ad da 'ya'yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma'anar wannan farilla?’ 27 Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada. 28 Isra'ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

Mutuwar 'Ya'yan Fari

29 Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato, magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi. 30 Da dare Fir'auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba. 31 Sai Fir'auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, “Tashi, ku da jama'arku, ku fita daga cikin jama'ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce. 32 Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.” 33 Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.” 34 Sai jama'ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu. 35 Isra'ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. 36 Ubangiji ya sa jama'a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.

Isra'ilawa sun Fita Masar

37 Isra'ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000 ), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot. 38 Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim. 39 Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba. 40 Zaman da Isra'ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin. 41 A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar. 42 Daren nan da Ubangiji ya sa don ya fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra'ilwa su kiyaye don su girmama Ubangiji dukan zamanansu.

Ka'idodin Idin Ƙetarewa

43 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ka'idar Idin Ƙetarewa, baƙo ba zai ci ba. 44 Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya. 45 Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba. 46 A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa. 47 Dukan taron jama'ar Isra'ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa. 48 Idan baƙon da yake zaune tare da ku yana so ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji tare da ku, to, sai a yi wa kowane namiji da yake a gidansa kaciya sa'an nan ya iya shiga idin, shi kuma ya zama ɗan ƙasa. Daɗai, marar kaciya ba zai ci ba. 49 Wannan ka'ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.” 50 Isra'ilawa suka yi na'am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna. 51 A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.

Fitowa 13

Keɓewar 'Ya'yan Fari

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Keɓe mini 'ya'yan fari maza duka. Kowane ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa cikin Isra'ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

Idin Abinci Marar Yisti

3 Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba. 4 A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib. 5 Sai ku kiyaye wannan farilla a wannan wata sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, wadda ya rantse wa kakanninku zai ba ku, wato, ƙasar da take ba da yalwar abinci. 6 Sai ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai, amma a rana ta bakwai za ku yi idi ga Ubangiji. 7 Abinci marar yisti za a ci har kwana bakwai. Kada a ga wani da abinci mai yisti, ko kuma yisti ɗin kansa, a ko'ina a wurarenku. 8 A wannan rana kowa zai sanar wa ɗansa cewa, abubuwan nan da muke yi, muna yi ne don tunawa da abin da Ubangiji ya yi mana sa'ad da ya fitar da mu daga Masar. 9 Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar. 10 Sai ku kiyaye farillar nan kowace shekara a lokacinta.”

'Ya'yan Fari

11 “Sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku, 12 sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne. 13 Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. Idan kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Kowane ɗan farin 'ya'yanku, sai ku fanshe shi. 14 In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta. 15 Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’ 16 Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”

Al'amudin Gizagizai da na Wuta

17 Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.” 18 Amma Allah ya kewaya da jama'a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra'ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi. 19 Musa ya kuma ɗauki ƙasusuwan Yusufu, gama Yusufu ya riga ya rantsar da Isra'ilawa su kwashe ƙasusuwansa daga Masar sa'ad da Allah ya ziyarce su. 20 Sai suka ci gaba da tafiya daga Sukkot suka yi zango a Etam a gefen jejin. 21 Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al'amudin girgije, da dare kuwa da al'amudin wuta, don ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana. 22 Al'amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama'a jagora ba.

Fitowa 14

Hayen Bahar Maliya

1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Faɗa wa Isra'ilawa su juya su yi zango a gaban Fi-hahirot tsakanin Migdol da bahar, a gaban Ba'alzefon. Sai ku yi zango gab da bahar. 3 Gama Fir'auna zai ce, ‘Aha, Isra'ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta cinye su.’ 4 Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi. 5 Da aka faɗa wa Sarkin Masar jama'a sun gudu, sai shi da fādawansa suka sāke tunaninsu game da jama'ar, suka ce, “Me muka yi ke nan, da muka bar Isra'ilawa su fita daga cikin bautarmu?” 6 Ya kuwa shirya karusarsa, ya ɗauki rundunarsa tare da shi. 7 Ya kuma ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shida da sauran karusan Masar duka waɗanda shugabanni suke bi da su. 8 Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Sarkin Masar, sai ya bi Isra'ilawa sa'ad da suka fita gabagaɗi. 9 Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba'alzefon. 10 Da Fir'auna ya matso, Isra'ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji. 11 Suka ce wa Musa, “Don ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar? 12 Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, ‘Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa?’ Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji.” 13 Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau. 14 Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!” 15 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra'ilawa su ci gaba. 16 Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye. 17 Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa. 18 Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.” 19 Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu. 20 Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani. 21 Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre. 22 Isra'ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu. 23 Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir'auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa. 24 Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al'amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su. 25 Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.” 26 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa bahar domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da bisa karusansu, da mahayan dawakansu.” 27 Gari na wayewa sai Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, ruwan kuwa ya koma kamar yadda yake a dā. Da Masarawa suka yi ƙoƙarin tserewa, sai ruwan ya rufe su. Ubangiji kuwa ya hallaka su a tsakiyar bahar. 28 Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir'auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu. 29 Amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busasshiyar ƙasa a tsakiyar bahar, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu. 30 A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra'ilawa daga hannun Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar. 31 Isra'ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.

Fitowa 15

Waƙar Musa

1 Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar. 2 Ubangiji ne ƙarfina da mafakata, Shi ne wanda ya cece ni. Wannan ne Allahna, zan yabe shi, Allah na kakana, zan ɗaukaka shi. 3 Ubangiji mayaƙi ne, Yahweh ne sunansa. 4 “Karusan Fir'auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar, Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya. 5 Rigyawa ta rufe su, Suka nutse cikin zurfi kamar dutse. 6 Ya Ubangiji dantsen damanka, mai iko ne, Ya Ubangiji, dantsen damanka ya ragargaza magabta. 7 Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka, Ka cinye su kamar ciyawa. 8 Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru, Rigyawa ta tsaya kamar tudu, Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar. 9 Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima, Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’ 10 Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye. 11 “Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli? Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki? Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu'ujizai. 12 Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su. 13 Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama'arka da ka fansa, Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka. 14 Al'ummai suka ji suka yi rawar jiki, Tsoro ya kama mazaunan Filistiya. 15 Sarakunan Edom suka tsorata, Shugabannin Mowab suna rawar jiki, Dukan mazaunan Kan'ana sun narke. 16 Tsoro da razana sun aukar musu, Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse, Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye, I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye, 17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka, Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka, Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka. 18 Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.” 19 Gama sa'ad da dawakan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar. 20 Sai Maryamu, annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa. 21 Maryamu tana raira musu waƙa tana cewa, “Raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Doki da mahayinsa, ya jefar cikin bahar.”

Maɓuɓɓugan Ruwan Ɗaci

22 Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba. 23 Sa'ad da suka zo Mara, sun kasa shan ruwan Mara saboda ɗacinsa, don haka aka sa masa suna Mara. 24 Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?” 25 Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa'an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi. A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka'idodi, a nan ne kuma ya gwada su. 26 Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.” 27 Daga nan suka je Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa goma sha biyu, da itatuwan giginya saba'in. A nan suka yi zango a bakin ruwa.

Fitowa 16

Manna da Makware

1 Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar. 2 Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka yi wa Musa da Haruna gunaguni cikin jejin, suka ce musu, 3 “Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.” 4 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama'a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu. 5 A kan rana ta shida, sai su ninka abin da suka saba tattarawa na kowace rana, su shirya shi.” 6 Musa da Haruna kuwa suka ce wa Isra'ilawa, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fisshe ku daga ƙasar Masar. 7 Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?” 8 Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.” 9 Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama'ar Isra'ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.” 10 Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije. 11 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa ya ce, 12 “Na ji gunagunin Isra'ilawa, amma ka faɗa musu cewa, ‘A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa'an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne.’ ” 13 Da maraice makware suka zo suka rufe zangon, da safe kuma raɓa ta kewaye zangon. 14 Sa'ad da raɓar ta kaɗe, sai ga wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo a ƙasa. 15 Sa'ad da Isra'ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato, “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba. Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci. 16 Abin da Ubangiji ya umarta ke nan, ko wannenku ya tattara wadda ta ishe shi ci, kowa ya sami mudu daidai bisa ga yawan mutanen da suke cikin kowace alfarwa.” 17 Isra'ilawa suka yi haka nan, suka tattara, waɗansu suka zarce, waɗansu kuma ba su kai ba. 18 Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa. 19 Musa ya ce musu, “Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya.” 20 Amma waɗansu ba su kasa kunne ga Musa ba, suka bar saura, har ta kwana, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su. 21 Kowace safiya sukan tattara ta, kowa gwargwadon cinsa, amma da rana ta yi zafi sai manna ɗin ta narke. 22 A kan rana ta shida suka tattara biyu ɗin abin da suka saba, kowane mutum mudu biyu biyu. Sai shugabannin taron suka zo suka faɗa wa Musa. 23 Shi kuwa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarta, ‘Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe.’ ” 24 Suka ajiye har gobe kamar yadda Musa ya umarta, amma ba ta yi ɗoyi ba, ba ta kuwa yi tsutsotsi ba. 25 Sai Musa ya ce, “Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba. 26 Kwana shida za ku tattara ta, amma a rana ta bakwai wadda take asabar, ba za a iske kome ba.” 27 Amma a rana ta bakwai ɗin waɗansu mutane suka tafi don su tattara, ba su kuwa sami kome ba. 28 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina? 29 Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin.” 30 Sai jama'a suka huta a rana ta bakwai. 31 Isra'ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma. 32 Sai Musa ya ce, “Ubangiji ya umarta a cika mudu da ita, a adana ta dukan zamananku domin kowane zamani a ga irin abincin da ya ciyar da ku cikin jeji lokacin da ya fito da ku daga ƙasar Masar.” 33 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki tukunya, ka zuba mudu guda na manna a ciki, ka ajiye a gaban Ubangiji, a adana har dukan zamananku.” 34 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, haka Haruna ya ajiye ta a gaban akwatin alkawari don kiyayewa. 35 Shekara arba'in Isra'ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan'ana. 36 Mudu ɗaya humushin garwa ɗaya ta gari.

Fitowa 17

Ruwa daga Dutse

1 Dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama'a za su sha. 2 Domin haka jama'a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.” Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?” 3 Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, don ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?” 4 Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Me zan yi wa jama'ar nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu.” 5 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ɗauki waɗansu dattawa daga cikin jama'ar Isra'ila, ka wuce a gaban jama'ar. Ka kuma ɗauki sandanka wanda ka bugi Nilu da shi, ka tafi. 6 Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila. 7 Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba,” saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”

Yaƙi da Amalekawa

8 Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra'ilawa a Refidim. 9 Sai Musa ya ce wa Joshuwa, “Zaɓo mana mutane, ka fita ka yi yaƙi da Amalekawa gobe. Zan tsaya a bisa dutsen da sandan mu'ujiza a hannuna.” 10 Joshuwa kuwa ya yi yadda Musa ya faɗa masa, ya fita ya yi yaƙi da Amalekawa. Musa, da Haruna, da Hur kuma suka hau kan dutsen. 11 Muddin hannun Musa na miƙe, sai Isra'ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara. 12 Sa'ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana. 13 Joshuwa kuwa ya ragargaza rundunar Amalekawa da takobi. 14 Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.” 15 Sai Musa ya gina bagade ya sa masa suna, Yahweh Nissi, wato, Ubangiji ne tutarmu. 16 Ya ce, “Ubangiji ya tabbata zai yaƙi Amalekawa har abada.”

Fitowa 18

Yetro ya Ziyarci Musa

1 Yetro, firist na Madayana, surukin Musa, ya ji dukan abin da Allah ya yi wa jama'arsa, wato, Musa da Isra'ilawa, yadda Ubangiji ya fito da su daga Masar. 2 Ya kawo Ziffora matar Musa, wadda Musa ya aika da ita gida. 3 Yetro kuma ya kawo 'ya'yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin 'ya'yansa, suna, Gershom. 4 Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir'auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer. 5 Sai Yetro ya kawo wa Musa 'ya'yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah. 6 Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da 'ya'yanta biyu tare da ita.” 7 Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa'an nan suka shiga alfarwa. 8 Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su. 9 Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra'ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa. 10 Yetro kuma ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da Fir'auna, wanda kuma ya ceci jama'arsa daga bautar Masarawa. 11 Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra'ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.” 12 Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra'ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah. 13 Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama'ar shari'a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma. 14 Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?” 15 Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah. 16 A sa'ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.” 17 Amma surukin Musa ya ce, “Abin nan da kake yi ba daidai ba ne. 18 Kai da jama'ar nan da take tare da kai za ku rafke, saboda abin da kake yi ya fi ƙarfinka, kai kaɗai ba za ka iya ba. 19 Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama'a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi. 20 Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi. 21 Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma. 22 Za su yi wa mutane shari'a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama'a tare da kai don ya yi maka sauƙi. 23 In ka bi wannan shawara, in kuma Allah ya umarce ka da yin haka, za ka iya ɗaukar nawayar jama'ar. Mutane duka kuwa za su yi zamansu lafiya.” 24 Musa kuwa ya saurari maganar surukinsa, ya yi abin da ya ce duka. 25 Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma. 26 Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu. 27 Sa'an nan Musa ya sallami surukinsa, ya koma garinsu.

Fitowa 19

Isra'ilawa a Dutsen Sina'i

1 Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar. 2 Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina'i, sai suka yi zango gaban dutsen. 3 Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah. Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, “Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato, Isra'ilawa ke nan, 4 ‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa yake ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni. 5 Yanzu fa, in za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama'ata, 6 za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa.” 7 Sa'an nan Musa ya je ya kira taron dattawan jama'a, ya bayyana musu dukan zantuttukan da Ubangiji ya umarce shi. 8 Dukan jama'a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, “Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar. 9 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, ni da kaina, ina zuwa a gare ka cikin duhun girgije, domin jama'a su ji sa'ad da nake magana da kai, domin su amince da kai tutur.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar. 10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin jama'a ka tsarkake su yau da kuma gobe, su kuma wanke tufafinsu. 11 Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina'i a gabansu duka. 12 Sai ka yi wa jama'a iyaka kewaye da dutsen, ka faɗa musu cewa, ‘Ku yi hankali kada ku hau dutsen ko ku taɓa shi. Duk wanda ya taɓa dutsen za a kashe shi, 13 za a jajjefe shi da duwatsu ko a harbe shi da kibiya, kada kowa ya taɓa dutsen da hannu. Wannan kuwa ya shafi mutane duk da dabbobi, tilas ne a kashe su.’ Sa'ad da aka busa ƙahon rago, sai mutane su taru a gindin dutsen.” 14 Da Musa ya gangaro daga dutsen zuwa wurin mutane, ya tsarkake su. Su kuwa suka wanke tufafinsu. 15 Sai Musa ya ce musu, “Ku shirya saboda rana ta uku, kada ku kusaci mace.” 16 A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da take cikin zango suka yi rawar jiki. 17 Musa kuwa ya fito da jama'a daga zango ya shugabance su, su sadu da Allah, suka tsattsaya a gindin dutsen. 18 Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai. 19 Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa. 20 Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau. 21 Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama'ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu. 22 Ko firistocin da za su kusato Ubangiji, sai su tsarkake kansu, don kada in hukunta su.” 23 Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su iya hawan dutsen Sina'i ba, gama kai da kanka ka umarce mu cewa, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen, ku tsarkake shi.’ ” 24 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sauka, ka hau tare da Haruna. Amma kada ka bar firistoci da jama'a su ƙetare kan iyakar su hau zuwa wurina, don kada in hukunta su.” 25 Sai Musa ya sauka wurin jama'a ya faɗa musu.

Fitowa 20

Dokoki Goma

1 Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce, 2 “Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 3 “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni. 4 “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa. 5 Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina. 6 Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararraki da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina. 7 “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza. 8 “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki. 9 Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida, 10 amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku. 11 Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji yakeɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta. 12 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka. 13 “Kada ka yi kisankai. 14 “Kada ka yi zina. 15 “Kada ka yi sata. 16 “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka. 17 “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”

Jama'a suka Tsorata

18 Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa. 19 Suka ce wa Musa, “Kai, ka yi magana da mu, za mu ji, amma kada Allah ya yi magana da mu don kada mu mutu.” 20 Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.” 21 Sai jama'a suka tsattsaya nesa, Musa kuwa ya matsa kusa da girgije mai duhu inda Allah yake.

Dokoki a kan Bagadai

22 Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama. 23 Banda ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa da na zinariya. 24 Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka. 25 Idan kuwa za ku gina mini bagade na dutse, kada ku gina mini da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama idan guduma ta taɓa duwatsun sun haramtu. 26 Kada ku yi wa bagadena matakai domin kada tsiraicinku ya bayyana a bisansu sa'ad da kuke hawansu.’ ”

Fitowa 21

Yadda za a Yi da Bayi

1 “Waɗannan su ne ka'idodin da za a ba Isra'ilawa. 2 Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a 'yantar da shi kyauta. 3 Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa'ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi. 4 Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa 'ya'ya mata ko maza, to, matar da 'ya'yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita. 5 Amma idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da 'ya'yansa, ba ya son 'yancin, 6 to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa'an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa. 7 “Idan mutum ya sayar da 'yarsa kamar baiwa, ba za a 'yanta ta kamar bawa ba. 8 Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba. 9 Idan ya ba da ita ga ɗansa ne sai ya maishe ta kamar 'yarsa. 10 In mutumin ya auri wata kuma, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba. 11 Idan kuwa bai cika mata wajiban nan uku ba, sai ta fita abinta, ba zai karɓi kome ba.”

Dokoki game da Nuna Ƙarfi da Yaji

12 “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle, shi ma sai a kashe shi. 13 In ba da nufi ya kashe shi ba, amma tsautsayi ne, to, sai mutumin ya tsere zuwa inda zan nuna muku. 14 Amma idan mutum ya fāɗa wa ɗan'uwansa da niyyar kisankai, lalle, sai a kashe shi ko da ya gudu zuwa bagadena. 15 “Wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle, kashe shi za a yi. 16 “Wanda ya saci mutum, ya sayar, ko kuwa a iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi. 17 “Wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle kashe shi za a yi. 18 “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya, 19 idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai. 20 “In mutum ya d�ki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi. 21 Amma idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, to, kada a hukunta shi, gama bawan dukiyarsa ne. 22 “Idan mutum biyu na faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. 23 Amma in wani lahani ya auku, to, sai a hukunta rai a maimakon rai, 24 ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa, 25 ƙuna a maimakon ƙuna, rauni a maimakon rauni, ƙujewa a maimakon ƙujewa. 26 “Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya lalace, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon idon. 27 Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

Hakkin Masu Abu

28 “Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta. 29 Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi. 30 Idan an yanka masa diyya, sai ya biya iyakar abin da aka yanka masa don ya fanshi ransa. 31 Haka kuma za a yi idan san ya kashe ɗan wani ko 'yar wani. 32 Idan san ya kashe bawa ko baiwa, sai mai san ya biya wa ubangijin bawan, ko baiwar, shekel talatin a kuma jajjefi san. 33 “Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki, 34 mai ramin zai biya mai san ko mai jakin, mushen ya zama nasa. 35 Idan san wani ya yi wa na wani rauni har ya mutu, sai ya sayar da san da yake da rai a raba kuɗin. Haka kuma za su raba mushen. 36 Amma idan dā ma an sani san mafaɗaci ne, mai san kuwa bai kula da shi ba, sai ya biya, wato, ya ba da sa a maimakon mushen. Mushen kuwa zai zama nasa.”

Fitowa 22

Dokokin Biya

1 “Idan mutum ya saci sa ko tunkiya, ya yanka ko ya sayar, zai biya shanu biyar a maimakon sa, tumaki huɗu maimakon tunkiya. 2 In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba, 3 sai dai ko in gari ya riga ya waye. Dole ɓarawon ya yi cikakkiyar ramuwa, in kuwa ba shi da abin biya, a sayar da shi a biya abin da ya satar. 4 In kuwa aka iske dabbar da ya satar a hannunsa da rai, ko sa, ko jaki, ko tunkiya, lalle ne ya biya riɓi biyu. 5 “In mutum ya kai dabbarsa kiwo a saura ko a garka, ya bar ta, ta yi ɓarna a gonar wani, ko a gonar inabin wani, sai a sa mai dabbar ya biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka. 6 “Idan wuta ta tashi a jeji ta ƙone tarin hatsi, ko hatsin da yake tsaye, ko gona, wanda ya sa wutar lalle ya biya cikakkiyar ramuwa. 7 “Idan mutum ya ba amininsa amanar kuɗi, ko amanar kadara, amma aka sace, in aka sami ɓarawon, a sa shi ya biya ninki biyu. 8 In kuwa ba a sami ɓarawon ba, sai a kawo maigidan a gaban Allah don a tabbatar babu hannunsa a cikin dukiyar amininsa. 9 “A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu. 10 “In mutum ya bai wa amininsa amanar jaki, ko sa, ko tunkiya ko kowace irin dabba, amma dabbar ta mutu, ko ta yi rauni, ko ta ɓace, in ba shaida, 11 rantsuwa ce za ta raba tsakaninsu don a tabbatar babu hannunsa a dukiyar amininsa, mai dukiyar kuwa ya yarda da rantsuwar. Wanda aka bai wa amanar ba zai biya ba. 12 In dai sacewa aka yi, sai ya biya mai shi. 13 Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba. 14 “Idan mutum ya yi aron wani abu a wurin maƙwabcinsa, in abin ya yi rauni ko ya mutu, sa'ad da mai abin ba ya nan, lalle ne ya yi ramuwa. 15 Amma in mai abin yana wurin, wanda ya yi aro ba zai yi ramuwa ba. Idan kuwa jingina ce aka yi, kuɗin jinginar ne ramuwar.”

Dokokin Addini da na Inganta Halin Kirki

16 “Idan mutum ya rarrashi budurwa wadda ba a tashinta, har ya ɓata ta, sai ya biya sadaki, ya aure ta. 17 Amma idan mahaifinta bai yarda ya ba da ita gare shi ba, sai mutumin ya ba da sadaki daidai da abin da akan biya domin budurwa. 18 “Kada a bar mace mai sihiri ta rayu. 19 “Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi. 20 “Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum. 21 “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. 22 Kada ku ci zalun marayu da gwauraye. 23 In kun tsananta musu, ba shakka za su yi kuka gare ni, ni kuma, hakika zan ji kukansu. 24 Zan husata, in sa a kashe ku cikin yaƙi, matanku, su ma, su zama gwauraye, 'ya'yanku kuwa su zama marayu. 25 “Idan kun ranta wa jama'ata matalauta da suke tsakaninku kuɗi, ba za ku zama musu kamar masu ba da rance da ruwa ba. Kada ku nemi ruwan kuɗin daga gare su. 26 In har wani ya karɓi rigar amininsa jingina, lalle ne ya mayar masa da ita kafin faɗuwar rana. 27 Gama wannan ne kaɗai mayafinsa, da shi zai rufe huntancinsa. Da me zai rufa ya yi barci? Zan amsa masa kuwa in ya yi kuka gare ni, gama cike nake da juyayi. 28 “Kada ku saɓi Allah, kada kuma ku zagi mai mulkin jama'arku. 29 “Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa. “'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su. 30 Haka kuma za ku yi da 'ya'yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi. 31 “Za ku zama keɓaɓɓun mutane a gare ni. Kada ku ci dabbar da naman jeji ya yayyage shi, sai ku jefa wa karnuka.”

Fitowa 23

Adalci da Aikata Gaskiya

1 Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi. 2 Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci. 3 Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari'a. 4 “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi. 5 Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa. 6 “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari'a. 7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba. 8 Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya. 9 “Kada ku wulakanta baƙo, kun dai san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.”

Shekara ta Bakwai da Rana ta Bakwai

10 “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu. 11 Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun. 12 “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake. 13 Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”

Ƙayyadaddun Idodi Uku

14 “Sau uku a shekara za ku yi mini idi. 15 Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi. 16 Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa'an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara. 17 Sau uku a shekara mazaje za su gabatar da kansu a gaban Ubangiji. 18 “Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana. 19 “Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”

Mala'ikan Ubangiji zai Bi da Isra'ilawa

20 “Ni da kaina zan aiki mala'ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa'ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku. 21 Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne. 22 Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku. 23 Mala'ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf. 24 Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu. 25 Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo. 26 A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai. 27 “Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje. 28 Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa. 29 Ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar ta zama kufai har namomin jeji su fi ƙarfinku. 30 Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku ya kai yadda za ku mallaki ƙasar. 31 Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku. 32 Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu. 33 Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”

Fitowa 24

Tabbatar da Alkawari

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan. 2 Musa ne kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama'a su hau tare da shi.” 3 Musa ya tafi, ya faɗa wa jama'a dukan dokokin Ubangiji da ka'idodinsa, sai dukan jama'a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.” 4 Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila. 5 Ya kuma sa samarin Isra'ila su miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama, da bijimai ga Ubangiji. 6 Sai Musa ya zuba rabin jinin a tasa, sauran rabin jinin kuwa ya yayyafa a kan bagade. 7 Ya kuma ɗauki Littafin Alkawari, ya karanta wa jama'a, sai suka ce, “Za mu yi dukan abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi biyayya.” 8 Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama'ar. Sa'an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake a cikin dokokin nan duka.” 9 Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba'in na Isra'ila. 10 Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake a ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama. 11 Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.

Musa a bisa Dutsen Sina'i

12 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da suke da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.” 13 Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah. 14 Ya ce wa dattawan, “Ku dakata a nan har mu komo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai ya je wurinsu.” Sa'an nan Musa ya hau bisa dutsen. 15 Da hawan Musa bisa dutsen, girgije ya rufe kan dutsen. 16 Ɗaukakar Ubangiji kuma ta zauna bisa Dutsen Sina'i. Girgijen ya lulluɓe dutsen har kwana shida, a rana ta bakwai kuwa Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen. 17 Isra'ilawa suka ga ɗaukakar Ubangiji kamar wuta mai cinyewa a bisa ƙwanƙolin dutsen. 18 Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.

Fitowa 25

Sadakoki domin Yin Wuri Mai Tsarki

1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Faɗa wa Isra'ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa. 3 Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla, 4 da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya, 5 da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya, 6 da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa, 7 da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 8 Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su. 9 Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”

Akwatin Alkawari

10 “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi. 11 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya. 12 Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato, ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon. 13 Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya. 14 Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa. 15 Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su. 16 A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin. 17 “Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18 Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin. 19 Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin. 20 Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21 Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka. 22 A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato, tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”

Teburin Gurasar Ajiyewa ga Ubangiji

23 “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 24 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. 25 Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. 26 Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin. 27 Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin. 28 Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin. 29 Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha. 30 Kullum za ku riƙa ajiye gurasar da kuke kawo mini a bisa teburin.”

Alkuki

31 “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su. 32 Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe. 33 A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni. 34 Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni. 35 A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya. 36 Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su. 37 Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. 38 Ku kuma yi hantsuka da farantai da zinariya tsantsa. 39 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya za ku yi alkukin da waɗannan abubuwa duka. 40 Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”

Fitowa 26

Alfarwa, wato, wurin da Allah zai Zauna

1 “Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani. 2 Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida. 3 Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka. 4 Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa. 5 Za ku yi wa kowane labule hantuna hamsin. Hantunan labulen nan biyu su yi daura da juna. 6 Za ku yi maɗauri guda hamsin da zinariya don a haɗa hantuna na labulen nan domin alfarwa ta zama ɗaya. 7 “Ku yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki, da za ku rufe alfarwar da shi. 8 Tsawon kowanne zai zama kamu talatin, fāɗinsa kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida. 9 Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi. 10 Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan. 11 Sa'an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya. 12 Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar. 13 Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar. 14 Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme. 15 “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye. 16 Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi. 17 Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan. 18 Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu. 19 Ku kuma yi kwasfa arba'in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa. 20 Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar. 21 Haka kuma za ku yi kwasfa arba'in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako. 22 A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida. 23 Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa. 24 Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwar nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu. 25 Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu. 26 “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya. 27 Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma. 28 Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe. 29 Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya. 30 Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen. 31 “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa. 32 Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa. 33 Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa'an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki. 34 Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki. 35 Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin. 36 Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta. 37 Ku yi dirkoki biyar da itacen ƙirya saboda makarin, ku dalaye su da zinariya. Ku kuma yi maratayansu da zinariya. Ku yi wa waɗannan dirkoki kwasfa biyar da tagulla.”

Fitowa 27

Bagade

1 “Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba'i. 2 A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla. 3 Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla. 4 Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa'an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu. 5 Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya. 6 Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla. 7 Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa. 8 Za ku yi bagaden da katakai, sa'an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.

Farfajiyar Alfarwar

9 “Za ku yi wa alfarwa farfajiya. A kudancin farfajiyar, sai ku rataye labule mai tsawo kamu ɗari wanda aka saƙa da lallausan zaren lilin. 10 Za ku yi masa dirkoki guda ashirin, da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa. 11 A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa. 12 Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma. 13 Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin. 14 Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku. 15 Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku. 16 Za a saƙa labule mai kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai launi shuɗi, da shunayya, da mulufi domin ƙofar farfajiyar. Za a sa wa ƙofar dirkoki huɗu tare da kwasfansu huɗu. 17 Za a yi wa dukan dirkokin da suke kewaye da farfajiyar maɗaurai da maratayai na azurfa, da kwasfa ta tagulla. 18 Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla. 19 Da tagulla kuma za a yi turakun alfarwar, da turakun farfajiyar, da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a cikin alfarwar.”

Kulawa da Fitila

20 “Sai a umarci Isra'ilawa su kawo tsabtataccen man zaitun tatacce domin fitilar. Za a kunna fitilar ta yi ta ci koyaushe. 21 Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”

Fitowa 28

Tufafin Firistoci

1 “Daga cikin 'ya'ya maza na Isra'ila sai ka kirawo ɗan'uwanka Haruna tare da 'ya'yansa, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki. 2 A ɗinka wa Haruna ɗan'uwanka, tufafi masu tsarki domin daraja da kwarjini. 3 Ka kuma yi magana da gwanayen sana'a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina. 4 Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan'uwanka, Haruna, da 'ya'yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki. 5 Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. 6 “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani. 7 Za a yi mata kafaɗa biyu, sa'an nan a haɗa su a karbunsu. 8 Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta. 9 A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai. 10 Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu. 11 Za a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu'ulu'u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya. 12 A sa duwatsun a kafaɗun falmaran don a riƙa tunawa da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su. 13 Za ku yi tsaiko biyu na zinariya, 14 ku kuma yi tukakkun sarƙoki biyu na zinariya tsantsa. Za ku ɗaura wa tsaikunan nan tukakkun sarƙoƙi. 15 “Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji don neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. 16 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba'i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya. 17 Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. 18 A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon. 19 A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis. 20 A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya. 21 A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi. 22 Ku kuma yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirji tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa. 23 Za ku yi ƙawanya biyu na zinariya, ku sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 24 Ku sa tukakkun sarkoƙin nan biyu na zinariya a cikin ƙawanya biyu na zinariya da suke a gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a haɗa su daga gaba a kafaɗun falmaran. 25 Za ku kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a cikin tsaikuna, sa'an nan a sa shi a gaban kafaɗun falmaran. 26 Ku kuma yi waɗansu ƙawane na zinariya, a sa su a sauran kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefe na ciki da yake manne da falmaran. 27 Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamarar nan. 28 Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran. 29 Duk sa'ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai ɗauki sunayen 'ya'yan Isra'ila a gaban Ubangiji kullum, a kan ƙyallen maƙalawa domin nemar musu nufin Allah. 30 Za ku kuma sa Urim da Tummin a kan ƙyallen maƙalawar domin su kasance a zuciyar Haruna sa'ad da ya shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai kokekoken Isra'ilawa a gaban Ubangiji. 31 “Sai ku yi taguwar falmaran da shuɗi duka. 32 Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa'an nan a yi wa wuyan basitsa, wato, cin wuya, domin kada ya kece. 33 Za a yi wa karbun taguwar ado da fasalin 'ya'yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu. 34 Za a jera su bi da bi, wato, 'ya'yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya. 35 Sai Haruna ya sa taguwar sa'ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu. 36 “Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’ 37 Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba. 38 Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji. 39 “Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado. 40 “Za a yi wa 'ya'yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini. 41 Ka sa wa Haruna, ɗan'uwanka, da 'ya'yansa maza, sa'an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki. 42 Sai kuma ku yi musu mukurai na lilin don su rufe tsiraicinsu daga kwankwaso zuwa cinya. 43 Haruna da 'ya'yansa maza za su sa su sa'ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa'ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”

Fitowa 29

Keɓewar Haruna da 'Ya'yansa Maza

1 “Abin da za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani, 2 da abinci marar yisti, da waina wadda aka cuɗe da mai, wadda aka yi da garin alkama mai laushi. 3 Ka sa waɗannan abu cikin kwando, sa'an nan ka kawo su cikin kwandon, ka kuma kawo ɗan bijimin da raguna biyu ɗin. 4 “Ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwar ta sujada, ka yi musu wanka. 5 Sa'an nan ka kawo tufafin, ka sa wa Haruna zilaikar, da taguwar falmaran, da falmaran ɗin, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ka ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta. 6 Za ka naɗa masa rawanin, sa'an nan ka ɗora kambi mai tsarki a bisa rawanin. 7 Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi. 8 “Sa'an nan ka kawo 'ya'yansa maza, ka sa musu zilaikun. 9 Ka kuma ɗaura musu ɗamara, ka sa musu hulunan. Aikin firist kuwa zai zama nasu har abada bisa ga dokar. Haka za ka keɓe Haruna da 'ya'yansa maza. 10 “A kuma kawo bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada. Haruna da 'ya'yansa maza za su ɗora hannuwansu a kan bijimin. 11 Za ka yanka bijimin a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 12 Za ka ɗibi jinin bijimin ka sa a bisa zankayen bagaden da yatsanka. Sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden. 13 Ka cire dukan kitsen da yake rufe da kayan cikin, da kitsen da yake manne da hanta, da wanda yake manne a ƙoda biyu ɗin. Ka ƙone su a bisa bagaden. 14 Amma naman bijimin da fatarsa, da tarosonsa, za ka ƙone da wuta a bayan zango, wannan hadaya ce don zunubi. 15 “Sai a kawo rago ɗaya, Haruna kuwa da 'ya'yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon. 16 Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa, ka yayyafa shi kewaye a kan bagaden. 17 Ka kuma yanyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikinsa, da ƙafafunsa, ka haɗa su da gunduwoyin, da kan. 18 Sa'an nan ka ƙone ragon duka a bisa bagaden don ya ba da ƙanshi. Wannan hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, wato, hadayar da aka ƙone da wuta. 19 “A kuma kawo ɗayan ragon, Haruna kuma da 'ya'yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon. 20 Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan 'ya'yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden. 21 Ka ɗiba daga cikin jinin da yake bisa bagaden, da man keɓewa, ka yayyafa wa Haruna da tufafinsa, da bisa 'ya'yansa maza, da tufafinsu don a tsarkake Haruna, da 'ya'yansa maza, da tufafinsu. 22 “Sai ka ɗebe kitsen ragon, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebe kitsen da yake rufe da kayan ciki, da dunƙulen kitsen da yake a bisa hanta, da ƙoda biyu ɗin da kitsensu, da cinyar dama, gama ragon na keɓewa ne. 23 Daga cikin kwandon abinci marar yisti da yake a gaban Ubangiji, sai ka ɗauki malmala ɗaya, da waina ɗaya da aka yi da mai, da ƙosai ɗaya. 24 Za ka sa waɗannan duka a hannun Haruna da na 'ya'yansa maza. Sai su kaɗa su domin hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 25 Sa'an nan za ka karɓe su daga hannunsu, ka ƙone su a bisa bagaden kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Ita hadaya ce ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji. 26 “Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka. 27 Za ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa da za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon keɓewa, wanda yake na Haruna da wanda yake na 'ya'yansa maza. 28 Wannan zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza daga wurin Isra'ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra'ilawa za su miƙa wa Ubangiji. 29 “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na 'ya'yansa maza bayan rasuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su. 30 Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga alfarwa ta sujada, domin ya yi aiki a Wuri Mai Tsarki. 31 “Sai ka ɗauki naman ragon keɓewa, ka dafa shi a wuri mai tsarki. 32 Haruna da 'ya'yansa maza za su ci naman da abinci da yake a cikin kwandon a ƙofar alfarwa ta sujada. 33 Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne. 34 Amma idan naman keɓewar ko abincin ya ragu har safiya, sai ka ƙone abin da ya ragu, kada a ci, gama tsattsarka ne. 35 “Haka nan za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa maza bisa ga dukan abin da na umarce ka. Kwana bakwai za ka ɗauka domin keɓewarsu. 36 A kowace rana za ka miƙa bijimi na hadaya domin zunubi ta yin kafara. Za ka tsarkake bagaden lokacin da ka yi kafara dominsa. Ka zuba masa mai, ka keɓe shi. 37 Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”

Hadayu na Yau da Kullum

38 “Wannan shi ne abin da za a miƙa a bisa bagaden kullum, 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya. 39 Za a miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice. 40 Haɗe da rago na fari, za a miƙa mudun gari mai laushi garwaye da rubu'in moɗa na tataccen mai, da rubu'in moɗa na ruwan inabi domin hadaya ta sha. 41 Ɗaya ragon kuma a miƙa shi da maraice. Za a miƙa shi tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha kamar wadda aka yi da safe ɗin domin ta ba da ƙanshi mai daɗi, gama hadaya ce wadda aka ƙone da wuta ga Ubangiji. 42 Wannan hadaya ta ƙonawa za a riƙa yinta dukan zamananku a bakin ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, inda ni zan sadu da kai in yi magana da kai. 43 Nan ne zan sadu da Isra'ilawa in tsarkake wurin da ɗaukakata. 44 Zan tsarkake alfarwa ta sujada da bagaden, zan kuma tsarkake Haruna da 'ya'yansa maza don su zama firistoci masu yi mini aiki. 45 Zan zauna tare da Isra'ilawa, in zama Allahnsu. 46 Za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu wanda ya fisshe su daga Masar don in zauna tare da su. Ni ne Ubangiji Allahnsu.”

Fitowa 30

Bagaden Ƙona Turare

1 “Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya. 2 Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba'i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi. 3 Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya. 4 Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa. 5 Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya. 6 Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai. 7 Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun. 8 Zai kuma ƙona turaren sa'ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku. 9 Ba za a ƙona wani irin turare dabam ba a bisansa, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta gari, ko ta sha, a bisansa ba. 10 Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”

Kuɗin Haikali

11 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, 12 “A sa'ad da za ku ƙidaya Isra'ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su. 13 Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji. 14 Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji. 15 Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba. 16 Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra'ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”

Daron Tagulla na Wanke Hannu

17 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 18 “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki. 19 A wurin ne Haruna da 'ya'yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu. 20 Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su. 21 Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”

Man Keɓewa da Turare

22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 23 “Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, 24 da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun. 25 Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki. 26 Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai. 27 A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare, 28 da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa. 29 Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka. 30 Za ka zuba wa Haruna da ya'yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki. 31 Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku. 32 Ba za a shafa wa kowa ba, ba kuma za a yi wani mai irinsa ba, gama man tsattsarka ne, saboda haka zai kasance tsattsarka a gare ku. 33 Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama'arsa.’ ” 34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida. 35 Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke. 36 A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa'an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki. 37 Irin turaren nan da za ku yi, ba za ku yi wa kanku irinsa ba. Zai zama abu mai tsarki a gare ku, gama na Ubangiji ne. 38 Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama'arsa.”

Fitowa 31

Waɗanda za su Yi alfarwa ta Sujada

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 2 “Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza. 3 Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha, 4 don ya yi fasalin abubuwa na zinariya, da azurfa, da tagulla, 5 da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha. 6 Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka 7 a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da suke cikin alfarwar, 8 da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare, 9 da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, 10 da saƙaƙƙun tufafi, wato, da tsarkakakkun tufafin Haruna da na 'ya'yansa maza domin aikin firistoci, 11 da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”

Ranar Hutawa

12 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 13 “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda yakeɓe ku. 14 Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa. 15 A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi. 16 Domin wannan fa Isra'ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne. 17 Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa, a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.’ ” 18 Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.

Fitowa 32

Ɗan Maraƙin Zinariya

1 Da mutane suka ga Musa ya yi jinkirin saukowa daga dutsen, sai suka taru wurin Haruna, suka ce masa, “Tashi, ka yi mana allahn da zai shugabance mu, gama ba mu san abin da ya faru da Musa ɗin wanda ya fisshe mu daga ƙasar Masar ba.” 2 Haruna ya ce musu, “Ku tuttuɓe zobban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na 'ya'yanku maza da mata, ku kawo mini.” 3 Sai jama'a duka suka tuttuɓe zobban zinariya da suke a kunnuwansu, suka kawo wa Haruna. 4 Ya karɓi zobban a hannunsu, sai ya narkar da su, ya sassaƙa shi da kurfi, ya siffata ɗan maraƙi. Da jama'a suka gani, sai suka ce, “Allahnku ke nan, ya Isra'ila, wanda ya fisshe ku daga Masar.” 5 Sa'ad da Haruna ya gani, ya gina bagade a gaban siffar maraƙin, ya yi shela, ya ce, “Gobe akwai idi ga Ubangiji.” 6 Kashegari da sassafe, suka tashi, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama. Jama'ar kuma suka zauna su ci su sha, suka kuma tashi suna rawa. 7 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu. 8 Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar.’ ” 9 Ya kuma ce wa Musa, “Na ga jama'ar nan suna da taurinkai. 10 Yanzu dai, ka bar ni kawai fushina ya yi ƙuna a kansu, ya cinye su, amma kai zan maishe ka babbar al'umma.” 11 Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar? 12 Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa. 13 Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada.’ ” 14 Ubangiji kuwa ya huce, ya janye niyyarsa ta jawo masifa a kan jama'arsa. 15 Musa ya sauko daga kan dutsen da allunan dutsen nan biyu na shaida a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da baya. 16 Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan. 17 A sa'ad da Joshuwa ya ji hayaniyar jama'ar, sai ya ce wa Musa, “Akwai hargowar yaƙi a zangon.” 18 Musa kuwa ya ce, “Ai, wannan ba hargowar nasara ba ce, ba kuma ta waɗanda yaƙi ya ci ba ce, amma hayaniyar waƙa nake ji.” 19 Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe. 20 Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha. 21 Musa ya ce wa Haruna, “Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo musu babban zunubi?” 22 Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'ar nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta. 23 Sun ce mini, ‘Yi mana allahn da zai shugabance mu, gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.’ 24 Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.” 25 Musa ya ga jama'ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu. 26 Musa ya tsaya a ƙofar zango, ya ce, “Duk wanda yake wajen Ubangiji ya zo wurina.” Sai Lawiyawa suka tattaru a wurinsa. 27 Ya ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Kowane mutum ya rataya takobinsa, ya kai ya kawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango duka, kowa ya kashe ɗan'uwansa, kowa ya kashe zumunsa, kowa ya kashe maƙwabcinsa.’ ” 28 Lawiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa. A ranan nan aka kashe mutum wajen talata (3,000 ). 29 Sai Musa ya ce, “Yau kun ba da kanku ga Ubangiji, gama kowane mutum ya kashe ɗansa da ɗan'uwansa, ta haka kuka jawo wa kanku albarka yau.” 30 Kashegari, Musa ya ce wa mutane, “Kun aikata babban zunubi. Yanzu kuwa zan tafi wurin Ubangiji, watakila zan iya yin kafara domin zunubanku.” 31 Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Kaito, mutanen nan sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya. 32 Amma ina roƙonka ka gafarta zunubansu, in kuwa ba haka ba, ina roƙonka ka shafe sunana daga cikin littafin da ka rubuta.” 33 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ai, dukan wanda ya yi mini zunubi, shi ne zan shafe sunansa daga cikin littafina. 34 Yanzu fa, sai ka tafi, ka bi da mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka, ga shi, mala'ikana zai wuce gabanka. Duk da haka a ranar da zan waiwaye ku, zan hukunta su saboda zunubinsu.” 35 Sai Ubangiji ya aika wa mutanen da annoba saboda ɗan maraƙin da suka sa Haruna ya yi musu.

Fitowa 33

An Ba da Umarni a Kama Tafiya

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama'ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’ 2 Zan kuwa aiki mala'ika a gabanka. Zan kuma kori Kan'aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 3 Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.” 4 Da jama'ar suka ji wannan mugun labari, sai suka yi nadama. Ba wanda ya sa kayan ado. 5 Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku.’ ” 6 Domin haka Isra'ilawa suka tuɓe kayan adonsu tun daga dutsen Horeb har zuwa gaba.

Alfarwa ta Sujada

7 Musa ya ɗauki alfarwa, ya kafa ta a bayan zango, nesa da zango. Ya kuwa sa mata suna, Alfarwa ta Sujada. Duk wanda yake neman Ubangiji, sai ya tafi alfarwa ta sujada, wanda yake a bayan zango. 8 Duk sa'ad da Musa ya tafi wurin alfarwar, jama'a duka sukan tashi tsaye, kowa ya tsaya a ƙofar alfarwarsa, ya kallaci Musa, har ya shiga alfarwar. 9 Sa'ad da Musa ya shiga alfarwar, al'amudin girgije ya sauko ya tsaya bisa ƙofar alfarwar, Ubangiji kuma ya yi magana da Musa. 10 A sa'ad da jama'a suka ga al'amudin girgijen nan na tsaye a ƙofar alfarwar, sai jama'ar duka su tashi su yi sujada, kowa a ƙofar alfarwarsa. 11 Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.

Alkawarin Zatin Ubangiji

12 Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’ 13 Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al'umma jama'arka ce.” 14 Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.” 15 Musa kuwa ya ce masa, “In ba za ka tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan. 16 Yaya zan sani ko na sami tagomashi a wurinka, ni da jama'arka, in ba ka tafi tare da mu ba? Yaya ni da jama'arka, za a bambanta mu da sauran jama'ar da suke a duniya?” 17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.” 18 Musa kuwa ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini kanka.” 19 Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.” 20 Ya kuma ce, “Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu.” 21 Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen. 22 A sa'ad da zatina yake wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har in wuce, 23 sa'an nan in ɗauke hannuna, za ka kuwa ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba.”

Fitowa 34

Allunan Dutse na Biyu

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa. 2 Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina'i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen. 3 Kada wani mutum ya zo tare da kai, kada a ga kowane mutum a ko'ina a kan dutsen, kada a bar garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.” 4 Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina'i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa. 5 Ubangiji kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da shi a can, ya yi shelar sunansa. 6 Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya. 7 Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.” 8 Sai Musa ya hanzarta, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada. 9 Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”

Sabunta Alkawari

10 Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa, a gaban dukan jama'a zan aikata al'ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al'umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku. 11 Ku kiyaye abin da na umarce ku a wannan rana. Ga shi, zan kora muku Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 12 Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai. 13 Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu. 14 “Ba za ku yi wa wani allah sujada ba, sai dai ni, gama sunana Mai Kishi, gama ni Allah mai kishi ne. 15 Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa'ad da suke shagulgulan bidi'arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa. 16 Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu. 17 “Kada ku yi wa kanku alloli na zubi. 18 “Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku. 19 “Kowane ɗan farin mutum, ko na dabba nawa ne, duk da 'ya'yan farin dabbobinku, wato, ɗan farin saniya da na tunkiya. 20 Ɗan farin jaki kuwa za ku fansa da ɗan rago, in kuwa ba za ku fansa da ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Za ku fanshi kowane ɗan fari. Kada a sami wanda ya zo gabana hannu wofi. 21 “Cikin kwana shida za ku yi aiki, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, ko lokacin noma ne, ko lokacin girbi sai ku huta. 22 “Ku kuma kiyaye idin mako, wato, idin girbin nunan fari na alkama, da idin gama tattara amfanin gonaki a ƙarshen shekara. 23 “Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra'ila. 24 Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in fāɗaɗa kan iyakarku. Ba wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokatan nan uku na shekara da kukan hallara a gaban Ubangiji Allahnku. 25 “Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana. 26 “Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.” 27 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Rubuta waɗannan kalmomi, gama daidai suke da kalmomin alkawarin da yake tsakanina, da kai, da Isra'ila.” 28 Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato, dokokin nan goma.

Musa ya Sauko daga Dutsen

29 Sa'ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina'i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. 30 Sa'ad da Haruna da dukan jama'ar Isra'ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi. 31 Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama'ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su. 32 Daga nan jama'ar Isra'ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina'i. 33 Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. 34 Amma duk lokacin da ya je gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila abin da aka umarce shi. 35 Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.

Fitowa 35

Ka'idodin Ranar Hutawa

1 Sai Musa ya tattara dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi. 2 Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi. 3 Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”

Sadaka domin Yin Alfarwa ta Sujada

4 Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, 5 ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla, 6 da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki, 7 da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya, 8 da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa, 9 da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”

Kayayyakin Alfarwa ta Sujada

10 “Bari dukan wanda yake da fasaha a cikinku ya zo, ya yi aikin da Ubangiji ya umarta a yi, 11 wato, aikin alfarwa ta sujada, da alfarwarta da murfinta, da maratayai, da katakanta da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta, 12 da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar. 13 Da tebur da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa, 14 da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila, 15 da bagaden turaren ƙonawa da sandunansa, da man keɓewa mai ƙanshi, da turaren ƙonawa, da labulen ƙofar alfarwa ta sujada, 16 da bagaden ƙona hadaya da ragarsa ta tagulla da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da daro da gammonsa, 17 da labulen farfajiya da dirkokinsa da kwasfansu, da labulen ƙofar farfajiyar, 18 da turakun alfarwa, da turakun farfajiyar, da igiyoyinsu, 19 da saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a Wuri Mai Tsarki, da tsarkakakkun tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza na aikin firist.”

Jama'a sun Kawo Sadaka

20 Sa'an nan dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga wurin Musa. 21 Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi. 22 Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato, da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji. 23 Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su. 24 Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi. 25 Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 26 Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki. 27 Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 28 Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa. 29 Sai dukan mata da maza na Isra'ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

Waɗanda suka yi Aikin Alfarwa ta Sujada

30 Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza. 31 Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki. 32 Domin ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta, waɗanda za a yi da zinariya, da azurfa, da tagulla. 33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. 34 Ubangiji ya ba Bezalel, da Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, hikimar koya wa waɗansu sana'a. 35 Gama ya cika su da hikima ta yin kowane irin aiki na sassaƙa da na zāne-zāne, da na yin ɗinke-ɗinke da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin, da na yin saƙa. Sun iya yin kowane irin aiki da yin zāne-zāne.

Fitowa 36

1 “Da Bezalel da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima, waɗanda Ubangiji ya ba su hikima da basira na sanin yin kowane irin aiki, za su shirya Wuri Mai Tsarki kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

Jama'a sun Kawo Sadaka Mai Yawa

2 Sai Musa ya kirayi Bezalel, da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima wanda Ubangiji ya ba shi hikima a zuciya, da duk wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo, ya yi aikin. 3 Su kuwa suka karɓa daga wurin Musa dukan sadaka ta yardar rai da Isra'ilawa suka kawo don yin aikin alfarwa ta sujada. Jama'a suka yi ta kawo masa sadaka ta yardar rai kowace safiya. 4 Sai masu hikima da suke yin aiki na alfarwa ta sujada suka ɗan dakatar da aiki suka tafi wurin Musa. 5 Suka ce masa, “Jama'a suna ta kawo sadaka fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.” 6 Sai Musa ya umarce su su yi shela a zango cewa, “Kada wata mace ko wani namiji ya sāke kawo sadaka don aikin alfarwa ta sujada.” Sai jama'a suka daina kawowa. 7 Gama abin da aka kawo ya isa yin aikin, har da ragi.

Yin Alfarwa ta Sujada

8 Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma'aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. 9 Tsawon kowane labule kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Dukan labulen girmansu ɗaya ne. 10 Ya ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, haka kuma ya yi da sauran labule biyar. 11 Sai ya sa shuɗɗan hantuna a karbun labule na fari da na biyu. 12 Ya sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Dukan hantunan suna daura da juna. 13 Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labule da juna da maɗauran domin alfarwa ta zama ɗaya. 14 Ya kuma yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki domin ya rufe alfarwa. 15 Tsawon kowane labule kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Labule goma sha ɗayan nan girmansu ɗaya ne. 16 Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya. 17 Sai ya yi hantuna hamsin, ya sa a karbu na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa hantuna hamsin a karbun sama na labule na biyu. 18 Ya kuma yi maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa hantuna da su don alfarwa ta zama ɗaya. 19 Ya yi wa alfarwa murfi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma yi wani abin rufewa da fatuna da aka jeme. 20 Ya kuma yi katakan alfarwa da itacen ƙirya. 21 Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi ne. 22 Kowane katako an fiƙe bakinsa biyu don a harhaɗa su tare, haka ya yi da dukan katakan alfarwa. 23 Yadda ya yi da katakan alfarwa ke nan, ya kafa katakai ashirin a fuskar kudu. 24 Sai ya yi kwasfa arba'in da azurfa domin katakai ashirin. Kowane katako yana da kwasfa biyu saboda bakinsa biyu da aka fiƙe. 25 A fuska ta biyu ta wajen arewa ta alfarwa, ya kafa katakai ashirin. 26 Ya kuma yi kwasfa arba'in na azurfa. Kowane katako yana da kwasfa biyu. 27 Ya yi katakai shida a bayan alfarwa a fuskar yamma. 28 Ya kuma yi katakai biyu don kusurwar baya ta alfarwa. 29 Aka haɗa katakai daga ƙasa har zuwa sama inda aka haɗa su a ƙawanya ta fari, haka ya yi da su a kusurwoyin nan biyu. 30 Akwai katako takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida. Kowane katako yana da kwasfa biyu. 31 Sai ya yi sanduna na itacen ƙirya, sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na alfarwa, 32 sanduna biyar kuma domin katakan ɗaya gefen na alfarwa, biyar kuma domin katakan da yake baya na alfarwa wajen yamma. 33 Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga wannan gefe zuwa wancan gefe. 34 Ya dalaye katakai da zinariya. Ya yi musu ƙawane na zinariya inda za a sarƙafa sandunan. Ya kuma dalaye sandunan da zinariya. 35 Ya kuma yi labule da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. 36 Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya. Sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi musu maratayai da zinariya. Ya yi wa dirkokin nan kwasfa huɗu da azurfa. 37 Ya yi wa ƙofar alfarwa labulen da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Ya yi wa labulen ado. 38 Ya haɗa labulen da dirkokinsa biyar, da maratayansu. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya, amma ya dalaye kwasfansu guda biyar da tagulla.

Fitowa 37

Yin Akwatin Alkawari

1 Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 2 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye da shi. 3 Ya sa masa ƙawanya huɗu na zinariya a kan kusurwoyinsa huɗu, ƙawane biyu a wannan gefe, biyu kuma a wancan gefe. 4 Ya kuma yi sandunan da itacen ƙirya, ya dalaye su da zinariya. 5 Sai ya zura sandunan cikin ƙawanen da ke a gyaffan akwatin don ɗaukarsa. 6 Ya yi murfin da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 7 Ya kuma ƙera siffofin kerubobi biyu da zinariya, ya maƙala su a gefe biyu na murfin. 8 Kerub ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a wancan gefe. Ya yi su a haɗe da murfin a gefe biyu na murfin. 9 Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.

Yin Tebur

10 Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 11 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya. 12 Ya yi masa dajiya mai fāɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya kewaye da ita. 13 Ya yi wa tebur ɗin ƙawane huɗu na zinariya, ya manna ƙawane a kusurwoyi huɗu na ƙafafunsa. 14 Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin. 15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya. 16 Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato, farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.

Yin Alkuki

17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin. 18 Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan. 19 A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni. 20 A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni. 21 Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin. 22 An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe. 23 Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa. 24 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.

Yin Bagaden Ƙona Turare

25 Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba'i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi. 26 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya. 27 Ya sa masa ƙawane biyu na zinariya a gyaffansa a ƙarkashin dajiya daura da juna don a zura sandunan ɗaukarsa. 28 Ya kuma yi sanduna biyu da itacen ƙirya, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.

Yin Man Keɓewa da Turare

29 Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.

Fitowa 38

Bagaden Ƙona Hadaya

1 Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba'i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku. 2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla. 3 Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta. 4 Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya. 5 Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna. 6 Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla. 7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa'an nan ya robe cikinsa.

Yin Daron Wanka

8 Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

Farfajiyar Alfarwa ta Sujada

9 Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne. 10 Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai. 11 Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa. 12 Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa. 13 Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne. 14 Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da dirkokinsu guda uku da kwasfan dirkoki guda uku. 15 Akwai kuma labule mai kamu goma sha biyar a gefe biyu na ƙofar farfajiyar. Labulen yana da dirkoki guda uku da kwasfan dirkoki guda uku. 16 Duk labulen da yake kewaye da farfajiya an yi shi da lallausan zaren lilin. 17 An yi kwasfan dirkoki duka da tagulla, amma maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su da azurfa. An dalaye kawunansu da azurfa. Dirkokin farfajiya duka suna da maɗaurai na azurfa. 18 An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya. 19 An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa. 20 An yi turakun alfarwa ta sujada da na farfajiya duka da tagulla.

Ƙarafan da aka yi Amfani da Su

21 Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist. 22 Sai Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. 23 Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. 24 Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 25 Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama'a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775 ) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 26 Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550 ). 27 An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato, kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan. 28 An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775 ), sa'an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai. 29 Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba'in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400 ). 30 Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden. 31 Da tagullar kuma aka yi kwasfan farfajiya, da kwasfan ƙofar farfajiya, da dukan turakun alfarwar da na farfajiyar.

Fitowa 39

Yin Tufafin Firistoci

1 An yi wa firistoci tufafi masu kyau na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, domin yin aiki a Wuri Mai Tsarki. Suka yi wa Haruna tsarkakan tufafi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 2 Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 3 An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha. 4 Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama. 5 Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 6 Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi. 7 Aka sa su a kan kafaɗun falmaran don su zama duwatsun tunawa da Isra'ila kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 8 Aka kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmaran aiki da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 9 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji murabba'i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya ɗaya ne. 10 Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. 11 A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon. 12 A jeri na uku aka sa yakinta, da idon mage, da ametis. 13 A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya. 14 An zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi. 15 Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 16 Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 17 Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 18 Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba. 19 Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran. 20 Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran. 21 Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 22 Ya kuma saƙa taguwa ta falmaran da shuɗi duka. 23 An yi wa taguwar wuyan wundi kamar sulke, aka daje wuyan don kada ya kece. 24 A karbun taguwar, suka yi fasalin 'ya'yan rumman da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 25 Suka kuma yi ƙararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin fasalin 'ya'yan rumman kewaye da karbun taguwa. 26 An jera su bi da bi, wato, fasalin rumman yana biye da ƙararrawa. Haka aka jera su kewaye da karbun taguwar yin aiki, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 27 Suka saƙa zilaika da lallausan zaren lilin don Haruna da 'ya'yansa. 28 Suka kuma yi rawani, da huluna, da mukurai da lallausan lilin. 29 Sun kuma yi abin ɗamara da lallausan lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi mata ɗinkin ado kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, “MAI TSARKI GA UBANGIJI.” 31 Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Ƙarewar Aikin

32 Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 33 Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato, da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta, 34 da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen, 35 da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa, 36 da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa, 37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila, 38 da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar, 39 da bagade na tagulla da ragarsa ta tagulla, da sandunansa da dukan kayayyakinsa, da daro da gammonsa, 40 da labulen farfajiya da dirkokinta, da kwasfanta, da labulen ƙofarta, da igiyoyinta, da turakunta, da dukan kayayyakin yin aiki a alfarwa ta sujada, 41 da tufafin ado na aiki a Wuri Mai Tsarki, wato, tsarkakan tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza don su yi aikin firistoci. 42 Isra'ilawa sun yi dukan aiki kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 43 Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.

Fitowa 40

Kafawar Alfarwa ta Sujada da Keɓewarta

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, 2 “A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada. 3 Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule. 4 Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa. 5 Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa. 6 Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada, 7 ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki. 8 Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar. 9 “Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya. 10 Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki. 11 Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi. 12 “Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa. 13 Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist. 14 Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi. 15 Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.” 16 Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi. 17 A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa. 18 Sai musa ya kafa alfarwa, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta. 19 Sa'an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 20 Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa. 21 Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 22 Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen. 23 Sa'an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 24 Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa. 25 Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 26 Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen. 27 Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 28 Ya sa labule a ƙofar alfarwa. 29 Ya kuma sa bagade na ƙona hadaya a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da ta gari kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 30 Ya kuma sa daro a tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ya zuba ruwa a ciki don wanka. 31 A cikinsa Musa da Haruna da 'ya'yansa maza sukan wanke hannuwansu da ƙafafunsu, 32 sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada, da sa'ad da sukan kusaci bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 33 Ya kuma yi farfajiya kewaye da alfarwa da bagaden, ya sa labulen ƙofar farfajiyar. Da haka Musa ya gama aikin.

Saukowar Girgije a bisa Alfarwa ta Sujada

34 Sa'an nan girgije ya rufe alfarwa ta sujada, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa. 35 Musa kuwa bai iya shiga alfarwa ta sujada ba domin girgijen yana zaune a bisanta, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa. 36 Cikin tafiyar Isra'ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa'ad da girgijen ya tashi daga kan alfarwa. 37 Idan girgijen bai tashi ba, su kuma ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. 38 Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan alfarwa da rana, da dare kuwa wuta ke cikinsa domin dukan Isra'ilawa su gani.

Littafin Firistoci 1

Hadaya ta Ƙonawa

1 Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce 2 ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki. 3 Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji. 4 Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara. 5 Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi. 6 Sai mai hadayar ya feɗe dabbar, ya yanyanka ta gunduwa-gunduwa. 7 Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar. 8 Su ɗibiya gunduwoyin, da kan, da kitsen bisa itacen da yake cikin wutar da take a kan bagaden. 9 Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 10 Idan hadayarsa ta ƙonawa daga cikin garken tumaki ko kuwa na awaki ne, sai ya ba da namiji marar lahani. 11 Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden. 12 Mai hadayar kuma zai yanyanka shi gunduwa-gunduwa, da kansa, da kitsensa. Firist zai jera su a bisa itacen da yake cikin wutar da take a bagaden. 13 Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 14 Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai. 15 Firist ɗin zai kawo tsuntsun a bagaden, ya murɗe wuyan tsuntsun, sa'an nan ya ƙone kan a bisa bagaden. Za a tsiyaye jini a gefen bagaden. 16 Amma zai ɗauki kururun da gashin ya zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka. 17 Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, ya ƙone shi, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Littafin Firistoci 2

Hadaya ta Gari

1 A sa'ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban. 2 Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 3 Ragowar garin hadayar kuwa, zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadaya ce ta ƙonawa mafi tsarki ga Ubangiji. 4 Sa'ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai. 5 Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai. 6 Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan. 7 Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai. 8 Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa'ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden. 9 Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 10 Ragowar hadayar garin zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadayar ƙonawa ce mafi tsarki ga Ubangiji. 11 A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba. 12 Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi. 13 Sai a sa gishiri a kowace hadaya ta gari, kada a rasa sa gishirin alkawarin Allah a hadaya ta gari. A sa gishiri a dukan hadayu. 14 Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza. 15 Za a zuba masa mai, a barbaɗa masa lubban, gama hadaya ce ta gari. 16 Firist kuwa zai ƙone wani kashi daga cikin ɓarzajjen hatsin a gauraye da man, da dukan lubban don tunawa, gama hadaya ce ta ƙonawa ga Ubangiji.

Littafin Firistoci 3

Hadaya ta Salama

1 Idan mutum zai kawo hadayarsa ta salama daga garken shanu, sai ya kawo mace ko namiji marar lahani ga Ubangiji. 2 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 3 Daga hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsen da yake rufe da kayan ciki, da wanda yake bisana, 4 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare ƙodojin. 5 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 6 Idan kuwa hadayarsa ta salama ga Ubangiji daga garken tumaki, ko na awaki ce, sai ya ba da dabbar, mace ko namiji, marar lahani. 7 Idan ɗan rago ne ya bayar don hadaya, sai ya miƙa shi a gaban Ubangiji. 8 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 9 Daga cikin hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsensa da wutsiyarsa duka mai kitse. Zai yanke ta gab da ƙashin gadon baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki kuwa, da wanda yake bisansa, 10 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin. 11 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. 12 Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji. 13 Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 14 Sa'an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa, 15 da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. 16 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne. 17 Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.

Littafin Firistoci 4

Hadayu domin Zunubi

1 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 2 ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan. 3 Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata. 4 Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji. 5 Shi kuma keɓaɓɓen firist ɗin ya ɗibi jinin bijimin ya kai shi a alfarwa ta sujada. 6 Ya tsoma yatsansa cikin jinin, ya yayyafa jinin sau bakwai a gaban Ubangiji a wajen labulen Wuri Mai Tsarki. 7 Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 8 Zai ɗebe dukan kitsen ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi, da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa, 9 da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama. 10 Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin ya ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya. 11 Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da tarosonsa, 12 da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar. 13 Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi. 14 Amma sa'ad da zunubin da suka aikata ya sanu, taron jama'a za su ba da ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi. Za a kawo shi a gaban alfarwa ta sujada. 15 Sai dattawan jama'a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa'an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji. 16 Sai keɓaɓɓen firist ya ɗibi jinin bijimin, ya kai cikin alfarwa ta sujada. 17 Sa'an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen. 18 Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 19 Zai kwashe kitsensa duka, ya ƙone shi bisa bagaden. 20 Sai ya yi da ɗan bijimin kamar yadda ya yi da ɗan bijimi na hadaya don zunubin firist. Ta haka firist zai yi kafara domin jama'a, za a kuwa gafarta musu. 21 Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama'ar. 22 Idan shugaba ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 23 Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya. 24 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi. 25 Sai firist ya ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 26 Firist ɗin zai ƙona kitsen duka a bisa bagaden kamar yadda akan yi da kitsen hadaya ta salama, ta haka firist zai yi kafara domin zunubin shugaban, za a kuwa gafarta masa. 27 In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 28 Sa'ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa. 29 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa. 30 Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona kadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 31 Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa. 32 Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani. 33 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa. 34 Sai firist ya ɗibi jinin abin yin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden. 35 Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi masa kafara saboda zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta masa.

Littafin Firistoci 5

Hadayu domin Laifi

1 Laifi ne idan mutum ya aikata kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. Idan mutum ya ji ana shelar neman mai laifi, amma ya ƙi fitowa ya ba da shaida, ko da yake ya gani, ko kuma ya san abin da ya faru, ya yi laifi, alhaki yana kansa. 2 Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abu da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba. 3 Ko kuma idan ya taɓa kowace irin ƙazantar mutum wadda akan ƙazantu da ita, ba da saninsa ba, amma in daga baya ya sani, to, laifi ya kama shi. 4 Ko kuma idan mutum ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa, cewa, zai yi mugunta, ko nagarta, ko kowace irin rantsuwa ta garaje da mutane sukan yi, to, laifi ya kama shi bayan da ya gane da rantsuwarsa. 5 In mutum ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan laifofi, sai ya hurta laifin da ya yi. 6 Ya kuma kawo hadaya ga Ubangiji don laifin da ya yi. Sai ya kawo 'yar tunkiya ko akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara don laifin mutumin. 7 Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa. 8 Zai kawo su wurin firist. Da fari firist zai miƙa hadaya don laifi. Zai karye wuyanta, amma ba zai tsinke kan ba. 9 Zai yayyafa jinin hadaya don laifi a gefen bagaden, sauran jinin kuwa zai tsiyaye a gindin bagade, gama hadaya ce don laifi. 10 Sa'an nan zai miƙa ta biyun don hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka ƙayyade. Firist ɗin zai yi kafara saboda laifin da mutumin ya yi, za a kuwa gafarta masa. 11 Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi. 12 Zai kai wa firist garin, firist zai ɗibi garin cike da tafin hannunsa, wannan shi ne kashi na tunawa. Zai ƙone shi bisa bagaden kamar hadaya na ƙonawa ga Ubangiji, gama hadaya ce don laifi. 13 Ta haka firist zai yi kafara don laifin da mutumin ya aikata daga cikin abubuwan nan, za a kuwa gafarta masa. Sauran garin zai zama na firist kamar yadda yakan zama nasa a hadaya ta gari. 14 Sai Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. 15 Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi. 16 Zai kuma biya diyya saboda abu mai tsarki da ya yi laifi a kansa. Zai kuma ƙara humushi a kai, sa'an nan ya ba firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa. 17 Idan wani ya yi laifi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, laifi ya kama shi ko da bai sani ba. Alhakin laifin yana kansa. 18 Sai ya kai wa firist rago marar lahani daga cikin garke. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa. 19 Hadaya ce don laifi, gama ya yi wa Ubangiji laifi.

Littafin Firistoci 6

1 Ubangiji kuma ya ba Musa ka'idodin nan. 2 Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi, 3 ko ya yi tsintuwa, amma ya yi m�su har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4 sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta, 5 ko kowane abu da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa. 6 Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi. 7 Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.

Hadayun da za a Ƙone Ƙurmus

8 Ubangiji kuma ya umarci Musa, 9 ya ba Haruna da 'ya'yansa maza ka'idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe. 10 Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa. 11 Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa'an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta. 12 Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta. 13 Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.

Hadaya ta Gari

14 Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. 'Ya'yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden. 15 Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa. 16 Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada. 17 Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi. 18 Kowane ɗa namiji cikin 'ya'yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka. 19 Sai Ubangiji ya ba Musa waɗannan ka'idodi, 20 domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice. 21 Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa'an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 22 Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada. 23 Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.

Hadayu don Zunubi

24 Sai Ubangiji ya umarci Musa 25 ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki. 26 Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada. 27 Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki. 28 Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa. 29 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki. 30 Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.

Littafin Firistoci 7

Hadaya don Laifi

1 Waɗannan su ne ka'idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka. 2 Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa. 3 Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, 4 da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama wadda za a cire tare da ƙodojin. 5 Firist zai ƙone su a bisa bagaden, gama hadaya ce da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, hadaya ce don laifi. 6 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne. 7 Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka'idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu. 8 Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi. 9 Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya. 10 Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon 'ya'yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.

Hadaya don Zumunta

11 Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji. 12 Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai. 13 Tare da hadayarsa ta salama don godiya, sai ya kawo dunƙulen abincin da aka sa masa yisti. 14 Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama. 15 Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe. 16 Amma idan hadayarsa ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu. 17 Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta. 18 Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi. 19 Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta. Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama. 20 Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa. 21 Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa. 22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 23 ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya. 24 Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci. 25 Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa. 26 Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka. 27 Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa. 28 Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi 29 don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama. 30 Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji. 31 Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza. 32 Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama. 33 Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama. 34 Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa. 35 Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da 'ya'yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji. 36 Ubangiji ya umarci Isra'ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu. 37 Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama. 38 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina'i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra'ilawa su kawo hadayunsu gare shi.

Littafin Firistoci 8

Keɓewar Haruna da 'Ya'yansa Maza

1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti. 3 Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.” 4 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada. 5 Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.” 6 Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka. 7 Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta. 8 Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen. 9 Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 10 Sai Musa ya ɗauki man keɓewa ya shafa wa alfarwa ta sujada da dukan abin da yake cikinta, da haka ya tsarkake su. 11 Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su. 12 Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya keɓe shi. 13 Sai Musa kuma ya kawo 'ya'yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 14 Sa'an nan ya kawo bijimi na yin hadaya don zunubi, Haruna da 'ya'yansa maza, suka ɗibiya hannuwansu a kan kan bijimin. 15 Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa. 16 Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden. 17 Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 18 Sa'an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 19 Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 20 Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen. 21 Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 22 Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 23 Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama. 24 Sai aka kawo 'ya'yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa'an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden. 25 Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama. 26 Daga cikin kwandon abinci marar yisti da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama. 27 Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji. 28 Sa'an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 29 Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 30 Sa'an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu. 31 Sai Musa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi. 32 Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su. 33 Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai. 34 Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku. 35 A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.” 36 Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

Littafin Firistoci 9

Haruna ya Miƙa Hadayu

1 A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da 'ya'yansa maza, da dattawan Isra'ila. 2 Sai ya ce wa Haruna, “Kawo ɗan maraƙi marar lahani na yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ka miƙa su ga Ubangiji. 3 Ka faɗa wa Isra'ilawa su ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa, 4 da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.” 5 Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji. 6 Musa kuma ya ce, “Ubangiji ya umarce ku ku yi dukan wanna, domin ɗaukakar Ubangiji za ta bayyana gare ku.” 7 Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama'a. Ka kuma kawo hadayar jama'a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.” 8 Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. 9 'Ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden. 10 Amma kitsen, da ƙadojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 11 Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon. 12 Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, 'ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa. 13 Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden. 14 Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden. 15 Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin. 16 Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa. 17 Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya. 18 Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 19 Suka cire kitsen bijimin, da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji, da matsarmama. 20 Sai Haruna ya aza kitsen a bisa ƙirjin dabbobin ya ƙone kitsen a bisa bagaden. 21 Amma ya yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin da cinyoyi na dama ga Ubangiji, kamar yadda Musa ya umarta. 22 Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama. 23 Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama'a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama'a duka. 24 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.

Littafin Firistoci 10

Zunubin Nadab da Abihu

1 'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa ko wannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. 2 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji. 3 Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit. 4 Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.” 5 Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.

Nawayar Aikin Firist

6 Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone. 7 Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.

Dokoki don Firistoci

8 Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce, 9 “Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku. 10 Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram. 11 Ku kuma koya wa mutanen Isra'ila dukan dokokin da Ubangiji ya ba su ta hannun Musa.” 12 Musa kuwa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele'azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. 13 Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni. 14 Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da 'ya'yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra'ilwa. 15 Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na 'ya'yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.” 16 Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele'azara da Itamar, 'ya'yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce, 17 “Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama'a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji? 18 Ga shi, ba a shigar da jinin can cikin Wuri Mai Tsarki ba. Ga shi kuwa, ya kamata ku ci kamar yadda na umarta amma ba ku yi ba.” 19 Sai Haruna ya ce wa Musa, “Ga shi, yau suka miƙa hadayarsu don zunubi, da ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?” 20 Da Musa ya ji wannan, sai ya yi na'am da shi.

Littafin Firistoci 11

Dabbobin da suke Halal da na Haram

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi 2 domin Isra'ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya, 3 wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa. 4 Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 5 Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku. 6 Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 7 Alade yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, haram ne a gare ku. 8 Ba za ku ci namansu ba, ba kuwa za ku taɓa mushensu ba, gama haram ne a gare ku. 9 Kwa iya cin waɗannan abubuwa da suke cikin ruwa, kowane abu da yake da ƙege da kamɓori da yake cikin tekuna ko koguna. 10 Amma kowace irin halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, abar ƙyama ce a gare ku. 11 Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne. 12 Kowane irin abu da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku. 13 Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa, 14 da shirwa, da buga zabi, da irinsu, 15 da kowane irin hankaka, 16 da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu, 17 da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe, 18 da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu, 19 da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage. 20 Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne, 21 sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. 22 Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu. 23 Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku. 24 Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana. 25 Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice. 26 Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu. 27 Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice. 28 Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice. 29 Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, 30 da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. 31 Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice. 32 Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka. 33 Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon. 34 Kowane irin abinci da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu. 35 Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku. 36 Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu. 37 Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba. 38 Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku. 39 Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice. 40 Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice. 41 Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba, 42 duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa. 43 Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa. 44 Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne. 45 Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne. 46 Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu. 47 Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.

Littafin Firistoci 12

Tsarkakewar Mata bayan Haihuwa

1 Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan domin jama'ar Isra'ila. 2 Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta. 3 A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya. 4 Sa'an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cike. 5 Amma idan 'ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida. 6 Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi. 7 Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ta haifi ɗa ko 'ya. 8 Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.

Littafin Firistoci 13

Dokoki a kan Kuturta

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi. 2 Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci. 3 Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne. 4 Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai. 5 A rana ta bakwai firist zai ƙara dudduba shi, in ya ga cutar ba ta yaɗu a fatar jikin mutumin ba, sai ya sāke kulle shi waɗansu kwana bakwai kuma. 6 A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa. 7 Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar jikin mutumin bayan da ya nuna kansa ga firist don tsarkakewa, sai ya sāke zuwa gaban firist. 8 Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce. 9 Sa'ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist. 10 Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin, 11 to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne. 12 Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist, 13 firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka. 14 Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki. 15 Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce. 16 Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist. 17 Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka. 18 Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke, 19 idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist. 20 Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin. 21 Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai. 22 Amma idan ƙurjin ya bazu a fatar jikin, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce. 23 Amma idan tabon ya tsaya wuri ɗaya, bai bazu ba, tabon miki ke nan, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne. 24 Ko kuma idan mutum ya ƙuna a fatar jiki, naman wurin ƙunar kuwa ya yi tabo jaja-jaja, da fari-fari, ko fari, 25 sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce. 26 Amma idan firist ya dudduba tabon, ya ga gashin tabon bai zama fari ba, zurfin tabon kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, firist zai kulle shi kwana bakwai. 27 A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce. 28 Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne. 29 Sa'ad da mace ko namiji na da cuta a kai, ko a gemu, 30 sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne. 31 Amma idan firist ya duba mikin, ya ga zurfinsa bai zarce fatar ba, ba kuma baƙin gashi a ciki, sai firist ya kulle mai miki har kwana bakwai. 32 A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba, 33 zai aske kansa, amma ba zai aske mikin ba, sai firist ya sāke kulle mai mikin har waɗansu kwana bakwai. 34 A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan. 35 Amma idan mikin ya bazu bayan tsarkakewarsa, 36 sai firist ya dudduba shi, idan mikin ya bazu a fatar, ba lalle ne ya nemi rawayan gashi ba, shi mutumin marar tsarki ne. 37 Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne. 38 Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai, 39 sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne. 40 Idan gashin kan mutum ya zube, ya zama mai sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne. 41 Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne. 42 Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa. 43 Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa, 44 to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa. 45 Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.” 46 Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango. 47 Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin, 48 ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata, 49 idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist. 50 Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai. 51 A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komenene za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki. 52 Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce. 53 Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba, 54 sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma. 55 Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje. 56 Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin. 57 Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar. 58 Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abu da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan. 59 Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.

Littafin Firistoci 14

1 Ubangiji ya ba Musa 2 waɗannan ka'idodi da za a bi a ranar tsarkakewar mai kuturta. Sai a kawo shi ga firist. 3 Firist ɗin zai fita zuwa bayan zango ya dudduba shi. Idan kuturun ya warke daga cutar kuturtar, 4 firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa. 5 Sai firist ya umarta a yanka tsuntsu ɗaya a kaskon da yake cike da ruwa mai gudu. 6 Ya kuma ɗauki ɗayan tsuntsu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon. 7 Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura. 8 Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai. 9 A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. 10 A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai. 11 Firist ɗin da zai tsarkake mutumin zai kawo wanda za a tsarkake da waɗannan abubuwa a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 12 Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 13 Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki. 14 Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin. 15 Firist kuwa zai ɗibi man, ya zuba shi a tafin hannunsa na hagu. 16 Ya kuma tsoma yatsan hannunsa na dama a cikin man da ka a tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa man da yatsansa sau bakwai a gaban Ubangiji. 17 Sauran man da ya ragu a tafin hannunsa, sai ya shafa shi a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da bisa babban yatsan hannunsa na dama, da na ƙafar dama. Wato, za a shafa man a inda aka shafa jinin hadaya don laifin. 18 Sauran man kuma da ya ragu cikin tafin hannunsa, firist ɗin zai shafa a kan wanda za a tsarkake. Firist zai yi kafara dominsa gaban Ubangiji. 19 Sai firist ya miƙa hadaya don zunubi domin ya yi kafara, don rashin tsarkin mutumin. Daga baya ya yanka hadaya ta ƙonawa. 20 Firist kuma zai miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a bisa bagaden. Da haka zai yi kafara dominsa, shi kuwa zai tsarkaka. 21 Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai, 22 da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. 23 A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji. 24 Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 25 Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama. 26 Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu. 27 Sai ya yayyafa man da yake cikin tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Ubangiji da yatsansa na hannun dama. 28 Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin. 29 Sauran man da yake cikin tafin hannunsa zai zuba a bisa wanda ake tsarkakewar, ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. 30 Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko 'yan tattabarai yadda ya iya, 31 ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar. 32 Wannan ita ce doka a kan mai ciwon kuturta wanda ba shi da isasshen abin bayarwa don yin hadayun tsarkakewarsa. 33 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 34 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar Kan'ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa'an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka'idodi. 35 Mutumin da ya ga kuturta a gidansa, tilas ye je ya faɗa wa firist. 36 Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan. 37 Zai dudduba tabon, idan akwai alamar tabon a bangayen gida kore-kore, ko jaja-jaja, idan an ga tabon ya yi zurfi cikin bangon, 38 sai firist ɗin ya fita daga cikin gidan zuwa ƙofa, ya rufe gidan har kwana bakwai. 39 A kan rana ta bakwai, sai firist ɗin ya komo, ya duba. Idan tabon ya yaɗu a jikin bangayen gidan, 40 sai ya umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar, a zuba a wuri marar tsarki can bayan birnin, 41 ya sa a kankare jikin gidan duka. Shafen da suka kankare kuwa, sai su zubar da shi a wuri marar tsarki can bayan birnin. 42 Sa'an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan. 43 Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe, 44 sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne. 45 Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki. 46 Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice. 47 Wanda kuma ya kwana cikin gidan, sai ya wanke tufafinsa, haka kuma wanda ya ci abinci cikin gidan, zai wanke tufafinsa. 48 Amma idan firist ɗin ya zo, ya dudduba, ya ga tabon bai yaɗu a gidan ba, bayan da an yi wa gidan shafe, sai firist ya hurta, cewa, gidan tsattsarka ne domin tabon ya warke. 49 Don tsarkakewar gidan, sai maigida ya kawo 'yan tsuntsaye biyu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya. 50 Sai a yanka tsuntsu ɗaya a kasko cike da ruwa mai gudu. 51 Zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai. 52 Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini. 53 Sa'an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka. 54 Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da 55 kuturta a tufafi ko a jikin gida, 56 da kumburi, da ɓamɓaroki, ko tabo, 57 don a tabbatar lokacin da suke tsarkakakku da lokacin da ba su da tsarki.

Littafin Firistoci 15

Ƙazanturwar Namiji ko Mace

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi 2 domin jama'ar Isra'ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al'aurarsa, ƙazantacce ne. 3 Ko al'aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne. 4 Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu. 5 Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 6 Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abu da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 7 Wanda kuma ya taɓa jikin mai ɗigar, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 8 Idan mai ɗigar yo tofar da yau a kan wanda yake da tsabta, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 9 Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu. 10 Duk wanda ya taɓa kowane abu da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 11 Duk wanda kuma mai ɗigar ya taɓa da hannunsa da bai wanke ba, sai wanda aka taɓa ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 12 Kaskon da mai ɗigar ya taɓa, sai a fasa shi, amma idan akushi ne sai a wanke shi da ruwa. 13 Sa'ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka. 14 A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist. 15 Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa. 16 Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 17 Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 18 Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice. 19 Sa'ad da mace take haila irin ta ka'ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice. 20 Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu. 21 Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 22 Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abu da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 23 Ko gado ne, ko kuma kowane abu da ta zauna a kai, sa'ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice. 24 Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu. 25 Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta. 26 Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abu da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta. 27 Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 28 Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka. 29 A rana ta takwas sai ta kawo 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. 30 Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta. 31 Ta haka za ka tsarkake jama'ar Isra'ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu. 32 Waɗannan su ne ka'idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne. 33 Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da take ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.

Littafin Firistoci 16

Ranar Kafara

1 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar 'ya'yan Haruna, maza biyu, sa'ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu. 2 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin. 3 Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.” 4 Sa'an nan Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa'an nan ya sa su. 5 Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama'ar Isra'ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa. 6 Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa. 7 Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 8 Sa'an nan ya jefa kuri'a kan bunsuran nan biyu. Kuri'a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel. 9 A wanda kuri'ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji. 10 Amma a wanda kuri'ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel. 11 Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa. 12 Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen. 13 Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu. 14 Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai. 15 Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin. 16 Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra'ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu. 17 Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita. 18 Sa'an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye. 19 Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama'ar Isra'ila. 20 A sa'ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai. 21 Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi. 22 Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji. 23 Sa'an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa'ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan. 24 Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa'an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama'a, domin ya yi kafara don kansa da jama'a. 25 Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden. 26 Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango. 27 Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu. 28 Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon. 29 Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu. 30 Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji. 31 Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada. 32 Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki. 33 Zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden. Sa'an nan kuma ya yi kafara domin firistocin, da dukan taron jama'ar. 34 Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama'ar Isra'ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara. Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

Littafin Firistoci 17

Wuri Ɗaya domin Yin Hadaya

1 Ubangiji ya umarce Musa, 2 ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan mutanen Isra'ila waɗannan ka'idodi. 3 Idan Ba'isra'ile ya yanka sa, ko ɗan rago, ko akuya a cikin zango, ko a bayan zango, 4 bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama'arsa. 5 Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji. 6 Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu. 8 Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka, 9 amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.

An Hana Cin Jini

10 Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a. 11 Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa. 12 Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, kada wani daga cikinsu, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, ya ci jini. 13 Idan kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya tafi farauta, ya kama nama, ko tsuntsu da ake ci, sai ya zub da jininsa, ya rufe da ƙasa. 14 Gama ran dukan nama yana cikin jininsa, saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, faufau ba za su ci jinin kowace dabba ba, gama ran kowace dabba yana cikin jininta. Duk wanda kuwa ya ci shi, za a raba shi da jama'a. 15 Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba'isra'ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa'an nan zai tsarkaka. 16 Amma idan bai wanke su ba, bai kuwa yi wanka ba, alhakinsa yana kansa.

Littafin Firistoci 18

An Haramta yin Lalata

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa 2 ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku. 3 Kada ku yi kamar yadda suke yi a kasar Masar inda kuka fito. Kada ma ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu. 4 Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 5 Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.” 6 Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.” 7 Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa. 8 Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce. 9 Kada ya kwana da 'yar'uwansa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam. 10 Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi. 11 Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce. 12 Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce. 13 Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce. 14 Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce. 15 Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce. 16 Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce. 17 In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa. 18 Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba. 19 Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki. 20 Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa. 21 Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne. 22 Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan. 23 Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu. 24 Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu. 25 Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. 26 Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka'idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu. 27 Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu. 28 Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al'ummar da ta riga su zama a cikinta. 29 Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama'a. 30 Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Littafin Firistoci 19

Dokoki a kan Tsarki da Yin Adalci

1 Ubangiji ya ce wa Musa 2 ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne. 3 Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku. 4 “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku. 5 “Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku. 6 A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta, 7 gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba. 8 Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama'a. 9 “Sa'ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi. 10 Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara 'ya'yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku. 11 “Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya. 12 Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku. 13 “Kada ku zalunci kowa ko ku yi masa ƙwace. Kada kuma ku bar lokacin biyan hakkin ma'aikaci ya kai har gobe. 14 Kada ku zagi kurma, kada kuma ku sa wa makaho abin tuntuɓe, amma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Ni ne Ubangiji. 15 “Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci. 16 Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa'ad da wani yake cikin shari'ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji. 17 “Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi. 18 Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko yo yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji. 19 “Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu. 20 “Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a 'yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba 'yantacciya ba ce. 21 Amma ya kawo rago na yin hadaya don laifinsa ga Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 22 Sai firist ya yi kafara da ragon hadaya don laifi saboda laifin mutumin a gaban Ubangiji. Za a kuwa gafarta masa zunubin da ya yi. 23 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da 'ya'ya na ci, 'ya'yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba. 24 A shekara ta huɗu 'ya'yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji. 25 Amma a shekara ta biyar, sai ku ci 'ya'yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku. 26 “Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri. 27 Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu, 28 ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji. 29 “Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata. 30 Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji. 31 “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku. 32 “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji. 33 “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi. 34 Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku. 35 “Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma'auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa. 36 Sai ma'auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. 37 Sai ku kiyaye, ku aikata dokokina da umarnaina duka. Ni ne Ubangiji.”

Littafin Firistoci 20

Hukunci a kan Rashin Biyayya

1 Ubangiji ya faɗa wa Musa, 2 ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu. 3 Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki. 4 Idan kuwa mutanen ƙasar ba su kashe mutumin nan, wanda ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa ba, 5 ni kaina zan yi gāba da mutumin nan da iyalinsa, da waɗanda suka yarda suka bi Molek tare da shi. Ba zan ƙara ce da su mutanena ba. 6 “Duk wanda yake sha'ani da masu mabiya, ko da bokaye zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa. 7 Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 8 Ku kuma kiyaye dokokina, ku aikata su, gama ni ne Ubangiji wanda yakeɓe ku. 9 “Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa. 10 “Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar. 11 Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 12 Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu. 13 Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 14 Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku. 15 Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar. 16 In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu. 17 “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu. 18 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki. 19 “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi. 20 Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa. 21 Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa. 22 “Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka'idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. 23 Kada ku bi al'adun waɗannan al'ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al'amura, don haka nake ƙyamarsu. 24 Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai. 25 Domin haka sai ku bambanta tsakanin halattattun dabbobi da haramtattun dabbobi, da tsakanin haramtattun tsuntsaye da halattattun tsuntsaye. Kada ku ƙazantar da kanku da haramtattun dabbobi, ko da tsuntsaye, ko da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa, waɗanda na ware su, su zama haramtattu a gare ku. 26 Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa. 27 “Namiji ko mace da ke da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”

Littafin Firistoci 21

Tsarkin Firistoci

1 Ubangiji kuma ya umarce Musa, ya faɗa wa 'ya'yan Haruna, maza, firistoci cewa, “Kada ko wannensu ya ƙazantar da kansa ta wurin gawar mutanensa, 2 sai dai gawar iyalinsa na kurkusa, wato, gawar mahaifiyarsa, da ta mahaifinsa, da ta ɗansa, da ta 'yarsa, da ta ɗan'uwansa, 3 da ta 'yar'uwarsa, budurwa, da take kusa da shi, wadda ba ta yi aure ba tukuna. Saboda su ya iya ƙazantar da kansa. 4 Kada ya ƙazantar da kansa saboda dangantakar aure cikin mutanensa. 5 “Kada su aske kansu ƙwal, ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsaga jikinsu. 6 Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki. 7 Kada firist ya auri karuwa, ko wadda mijinta ya sake ta, gama shi tsattsarka ne gare ni. 8 Dole jama'a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena. 9 'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta. 10 “Firist wanda yake babba cikin 'yan'uwansa da aka zuba masa man keɓewa, aka kuma keɓe shi ya riƙa sa tufafin firist, kada ya bar gashin kansa buzu-buzu, ko kuwa ya kyakketa tufafinsa. 11 Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu. 12 An keɓe shi domina, kada ya ƙazantar da kansa, kada kuwa ya ɓata alfarwa ta sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. 13 Sai ya auri budurwa. 14 Kada ya auri mace wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, ko karuwa, amma ya auri budurwa daga cikin kabilarsa, 15 domin kada ya ƙazantar da 'ya'yansa waɗanda ya kamata su zama tsarkakakku. Ni ne Ubangiji, na kuwa keɓe shi ya zama babban firist.” 16 Sai Ubangiji ya umarce Musa 17 ya faɗa wa Haruna cewa, “Kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani ya kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni har abada. 18 Duk mutumin da yake da lahani na makanta, ko gurguntaka, ka rauni a fuska, ko gaɓar da ta fi wata, 19 ko tauyayye a ƙafa ko a hannu, 20 ko mai ƙusumbi, ko wada, ko mai lahani a ido, ko cuta mai sa ƙaiƙayi, ko kirci, ko dandaƙaƙƙe, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ba. 21 Duk mutumin da yake cikin zuriyar Haruna firist, wanda yake da lahani, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni ba. 22 Amma zai iya ci daga cikin tsattsarkan abincin da aka miƙa mini, da abinci mafi tsarki. 23 Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.” 24 Haka nan kuwa Musa ya faɗa wa Haruna, da 'ya'yan Haruna, maza, da dukan Isra'ilawa.

Littafin Firistoci 22

Hadayu suna da Tsarki

1 Ubangiji kuma ya umarci Musa 2 ya faɗa wa Haruna, da shi da 'ya'yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji. 3 Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji. 4 “Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga, 5 da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta, 6 duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna. 7 To, sa'ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne. 8 Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji. 9 “Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka'idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka. 10 “Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake zama tare da su ne, ko kuwa an ɗauke shi yana yi musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba. 11 Amma idan firist ya sayi bawa da kuɗinsa, bawan ya zama dukiyarsa, bawan zai iya ci, haifaffun gidansa kuma za su iya cin tsattsarkan abincin. 12 Idan kuwa 'yar firist ta auri wani wanda ba firist ba, to, kada ta ci daga cikin tsarkakakkun hadayu. 13 Amma idan 'yar firist ɗin gwauruwa ce, ko sakakkiya, ba ta kuma da ɗa, ta kuwa koma gidan mahaifinta, sai ta ci daga cikin abincin mahaifinta kamar cikin kwanakin ƙuruciyarta. Amma wani dabam ba zai ci ba. 14 “Idan kuwa har wani mutum dabam ya ci daga cikin tsarkakakken abin ba da saninsa ba, to, sai ya maido abin ga firist, da ƙarin humushin tamanin abin. 15 Firist ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun abubuwan nan da jama'ar Isra'ila suke miƙawa ba, 16 da zai bar mutumin da bai cancanta ya ci ba, wannan zai jawo masa hukunci. Ni ne Ubangiji. Ni na tsarkake hadayun.” 17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 18 ya yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Sa'ad da duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune a Isra'ila, ya kawo hadaya ta ƙonawa, ko ta wa'adi ce, ko ta yardar rai, dole ne dabbar ta zama marar lahani. 19 Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu. 20 Kada ku yi hadaya da abin da yake da lahani, gama Ubangiji ba zai karɓa ba. 21 Idan kuwa wani ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji don cika wa'adi, ko don hadaya ta yardar rai, daga cikin garken shanu, ko na tumaki, da na awaki, sai ya zama cikakke, marar lahani, don ya karɓu. 22 Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su. 23 Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba. 24 Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba. 25 “Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.” 26 Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce, 27 “Sa'ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji. 28 Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce. 29 Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓa. 30 A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji. 31 “Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji. 32 Kada ku jawo wa sunana mar tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra'ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku, 33 na kuma fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”

Littafin Firistoci 23

Ƙayyadaddun Idodi

1 Ubangiji ya ba Musa 2 waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada. 3 Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce. 4 Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.

Idin Ƙetarewa da na Abinci Marar Yisti

5 Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji. 6 Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai. 7 Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba. 8 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba. 9 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 10 lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu. 11 Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar. 12 A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani. 13 Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya. 14 Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka'ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.

Idin Girbi

15 Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji. 16 Kwana hamsin za su ƙirga zuwe kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa'an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji. 17 Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji. 18 Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 19 Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama. 20 Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist. 21 A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka. 22 Sa'ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

Idin Sabuwar Shekara

23 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 24 ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada. 25 Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

Ranar Kafara

26 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 27 rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji. 28 Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu. 29 Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama'ar Allah ba. 30 Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi. 31 Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke. 32 Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.

Idin Bukkoki

33 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa, 34 a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji. 35 Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba. 36 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki. 37 Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta. 38 Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa'adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji. 39 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa. 40 A ranar sai su ɗibi 'ya'yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa'an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai. 41 Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka'ida ce a gare su har abada. 42 Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk 'yan ƙasa waɗanda suke Isra'ilawa za su zauna cikin bukkoki. 43 Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu. 44 Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.

Littafin Firistoci 24

Kulawa da Fitila

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa 2 ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum. 3 Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku. 4 Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.

Gurasar da aka Miƙa ga Allah

5 Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari. 6 A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri. 7 Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji. 8 Kullum a kowace ranar Asabar, Haruna zai kintsa su a gaban Ubangiji domin Isra'ilawa saboda madawwamin alkawarin. 9 Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.

Hukunci a kan Saɓo da Biyan Diyya

10 Ɗan wata mace Ba'isra'iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba'isra'ile a cikin zangon. 11 Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwar Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan. 12 Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi. 13 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 14 “Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu. 15 Sa'an nan ka faɗa wa Isra'ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa, 16 za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu. 17 “Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi. 18 Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai. 19 “Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa. 20 Idan ya karya masa ƙashi ne, sai a karya nasa ƙashin, idan ya cire wa wani ido, sai a ƙwaƙule nasa, idan haƙori ya ɓalle, sai a ɓalle nasa. Duk irin raunin da ya ji wa wani haka za a yi masa. 21 Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi. 22 Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.” 23 Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Littafin Firistoci 25

Bikin Kewayowar Shekaru

1 Ubangiji kuwa ya yi wa Musa magana a kan Dutsen Sina'i, ya ce 2 ya faɗa wa Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, ƙasar za ta kiyaye shekara ta bakwai ga Ubangiji. 3 Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu. 4 Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, shekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu. 5 Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar. 6 A shekarar nan ɗin ƙasar za ta tanada musu abinci, da su da bayinsu mata, da maza, da barorinsu na ijara, da baƙon da yake zaune tare da su, 7 har da dabbobinsu na gida da na jeji. Duk albarkar da ƙasar za ta bayar, za ta zama abinci.

Murnar Shekara ta Hamsin

8 Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba'in da tara a gare su. 9 A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka. 10 Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa. 11 Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba. 12 Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar. 13 Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa. 14 In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna. 15 Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 16 Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne. 17 Kada ku cuci juna fa, amma ku ji tsoron Allahnku, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

Matsalolin Shekarar Murna

18 “Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya. 19 Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya. 20 “Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba, 21 ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku. 22 Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”

Fansar Mallaka

23 “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina. 24 “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka. 25 Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar. 26 Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa, 27 to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa. 28 Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa. 29 “Haka nan kuma idan mutum ya jinginar da gida a cikin birni mai garu, yana da izini ya fanshi abinsa a ƙarshen shekara guda. 30 Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba. 31 Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna. 32 Amma a kan biranen Lawiyawa, da gidajen da suke cikin biranen da suka mallaka, Lawiyawa suna da izini su fanshe su a kowane lokaci. 33 Amma idan wani daga cikin Lawiyawa bai fanshi gidansa ba, a shekara ta hamsin ta murna sai a mayar masa da gidan nan na cikin birnin da suka mallaka, gama gidajen da suke cikin biranen Lawiyawa su ne nasu rabo a cikin Isra'ilawa. 34 Ba za a jinginar da hurumin biranensu ba, gama wannan shi ne abin mallakarsu har abada.”

Ba da Rance ga Matalauci

35 “Idan ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce, ya kasa riƙon kansa, sai ka riƙe shi kamar baƙon da yake baƙunci a wurinka. 36 Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya zauna tare da kai. 37 Kada ka ranta masa kuɗi da ruwa, kada kuma ka ba shi abinci don sumun riba. 38 Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fanshe ku daga ƙasar Masar don in ba ku ƙasar Kan'ana, in zama Allahnku.”

'Yantar da Bayi

39 “Idan kuwa ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce har ya sayar da kansa gare ka, to, kada ka bautar da shi kamar bawa. 40 Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 41 Sa'an nan shi da iyalinsa su rabu da kai, ya koma wurin danginsa da mahallin kakanninsa. 42 Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba. 43 Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka. 44 Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da take kewaye da ku. 45 Kwa iya sayen bayi daga baƙin da suke baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku. 46 Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba. 47 “Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan'uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon, 48 bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin 'yan'uwansa ya iya fansarsa. 49 Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa. 50 Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara. 51 Idan shekarun sun ragu da yawa, sai ya fanshi kansa bisa ga adadin kuɗin da aka saye shi. 52 Amma idan shekarun sun ragu kaɗan kafin shekara ta hamsin ta murna, sai ya lasafta, ya biya don fansarsa bisa ga yawan shekarun. 53 Sai baƙon ya mai da shi kamar bara mai aikin ijara, shekara a kan shekara. Amma kada ya tsananta masa. 54 Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da 'ya'yansa. 55 Gama a gare ni Isra'ilawa bayi ne waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Littafin Firistoci 26

Fa'idodin Biyayya

1 Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 2 Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji. 3 “Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, 4 sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu. 5 Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya. 6 “Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba. 7 Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku. 8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi. 9 Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina. 10 Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da s�nā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo. 11 Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba. 12 Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena. 13 Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”

Hukuncin Rashin Biyayya

14 “Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci. 15 Idan kuma kuka yi watsi da dokokina, ba ku kuwa kula da ka'idodina ba, har kuka ƙi kiyaye umarnaina, kuka karya alkawarina, 16 to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci. 17 Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku. 18 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku. 19 Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla. 20 Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba. 21 “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku. 22 Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku. 23 “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini, 24 sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku. 25 Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku. 26 Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba. 27 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini, 28 sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku. 29 Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza. 30 Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku. 31 Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba. 32 Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki. 33 Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace. 34 Sa'an nan ƙasar za ta ji daɗin hutunta muddin tana zaune kango. Sa'ad da kuke a ƙasar maƙiyanku, ƙasar za ta huta, taji daɗin hutunta. 35 Muddin tana zaune kufai za ta sami hutawa, hutawa asabatan da ba ta samu ba a lokacin da kuke zaune cikinta. 36 “Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za sukuwa fāɗi. 37 Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba. 38 Za ku mutu a cikin al'ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku. 39 Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu. 40 “Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini, 41 haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu, 42 sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar. 43 Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka'idodina, suka yi watsi da dokokina. 44 Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu. 45 Amma saboda su zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai domin in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.” 46 Waɗannan su ne dokoki, da ka'idodi, da umarnai waɗanda Ubangiji ya yi tsakaninsa da Isra'ilawa ta hannun Musa a bisa Dutsen Sina'i.

Littafin Firistoci 27

Ka'idodin Keɓewa

1 Ubangiji ya ba Musa 2 waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa'adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi. da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Masu biya Abin da za su biya Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin Mata masu shekara 5-20 Shekel goma Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma 8 Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa'adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa'adin. 9 Idan kuwa dabba ce irin wadda mutane kan miƙa hadaya ga Ubangiji, dukan irin wannan da mutum yakan bayar ga Ubangiji zai zama tsattsarka. 10 Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku. 11 Idan kuwa dabbar marar tsarki ce, irin wadda ba a miƙa ta hadaya ga Ubangiji, sai mutumin ya kai dabbar a wurin firist. 12 Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama. 13 Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta. 14 Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama. 15 Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa. 16 Idan mutum ya keɓe wa Ubangiji wani sashi daga cikin gonarsa ta gādo, sai ka kimanta tamanin gonar daidai da yawan irin da zai rafa. Gonar da za a yafa iri wajen garwa ashirin na sha'ir tamaninta zai zama wajen shekel hamsin. 17 Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba. 18 Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar. 19 Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa. 20 Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba. 21 Sa'ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta. 22 Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba, 23 sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji. 24 A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo. 25 Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 26 Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne. 27 Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta. 28 Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji. 29 Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi. 30 Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji. 31 Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin. 32 Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce. 33 Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba. 34 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sina'i saboda isra'ilawa.

Littafin Ƙidaya 1

Ƙidaya ta Farko a Jejin Sina'i

1 A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sina'i. Ya ce, 2 “Da kai da Haruna ku ƙidaya Isra'ilawa, bisa ga kabilansu da iyalansu. Ku tsara sunayen dukan mazaje 3 daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi. 4 Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.” 5-15 Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa. Kabila Shugaban Kabila Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Naftali Ahira ɗan Enan 16 Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki. 17 Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu, 18 suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta, 19 kamar yadda Ubangiji ya umarta. Musa ya rubuta jama'a a jeji ta Sina'i. masu shekara ashirin ko fi da suka isa yaƙi aka rubuta su suna suna, bisa ga kabilansu da iyalansu, aka fara da kabilar Ra'ubainu, babban ɗan Yakubu. Ga yadda jimillarsu take. Kabila Jimilla Ra'ubainu (46,500 ) Dubu arba'in da shida da ɗari biyar. Saminu (59,300 ) Dubu hamsin da tara da ɗari uku. Gad (45,650 ) Dubu arba'in da biyar da ɗari shida da hamsin. Yahuza (74,600 ) Dubu saba'in da huɗu da ɗari shida. Issaka (54,400 ) Dubu hamsin da huɗu da ɗari huɗu. Zabaluna (57,400 ) Dubu hamsin da bakwai da ɗari huɗu. Ifraimu (40,500 ) Dubu arba'in da ɗari biyar. Manassa (32,200 ) Dubu talatin da biyu da ɗari biyu. Biliyaminu (35,400 ) Dubu talatin da biyar da ɗari huɗu. Dan (62,700 ) Dubu sittin da biyu da ɗari bakwai. Ashiru (41,500 ) Dubu arba'in da ɗaya da ɗari biyar. Naftali (53,400 ) Dubu hamsin da uku da ɗari huɗu. Jimilla duka (603,550 ) dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin.

An Ba Lawiyawa Ikon Alfarwa

47 Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba, 48 gama Ubangiji ya ce wa Musa, 49 “Sa'ad da kake ƙidaya Isra'ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi. 50 A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita. 51 Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi. 52 Sauran Isra'ilawa za su sauka ƙungiya ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa a ƙarƙashin tutarsa. 53 Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.” 54 Sai Isra'ilawa suka aikata kowane abu da Ubangiji ya umarci Musa.

Littafin Ƙidaya 2

Zango da Shugabannin Kabilai

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan umarnai. 2 Duk sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Zangon zai kasance a kewaye da alfarwa ta sujada. kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka, (186,400 ) dubu ɗari da tamanin da shida da ɗari huɗu. Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya. kabilar Ra'ubainu za su sauka su kafa tutarsu a sashin kudu a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur 46,500 Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai 59,300 Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel 45,650 Jimilla duka, (151,450 ) duba ɗari da hamsin da ɗaya, da ɗari huɗu da hamsin. Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su bi bayan na Yahuza. 17 Sa'an nan Lawiyawa ɗauke da alfarwa ta sujada za su kasance a tsakanin ƙungiyoyi biyu na farko da biyun da suke daga ƙarshe. Kowace ƙungiya za ta yi tafiya kamar yadda aka dokace ta ta zauna a zango, wato kowacce ta yi tafiya a ƙarƙashin tutarta a matsayinta. kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabilar Shugaba Jimilla Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500 Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200 Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400 Jimilla duka, (108,100 ) dubu ɗari da takwas, da ɗari ɗaya daidai. Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin. 25-31 Ƙungiyoyin kabilar Dan za su sauka su kafa tutarsu a sashin arewa a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai 62,700 Ashiru Fagiyel ɗan Okran 41,500 Naftali Ahira ɗan Enan 53,400 Jimilla duka, (157,600 ) duba ɗari da hamsin da bakwai, da ɗari shida. Ƙungiyoyin Dan za su bi daga bayan duka. 32 Jimillar yawan Isra'ilawa da aka rubuta su a yadda suke ƙungiya ƙungiya, su dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin ne (603,550 ). 33 Amma kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ba a rubuta Lawiyawa haɗe da sauran Isra'ilawa ba. 34 Saboda haka Isra'ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.

Littafin Ƙidaya 3

Yawan Lawiyawa da Aikinsu

1 Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a bisa Dutsen Sina'i. 2 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 3 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, da aka naɗa firistoci domin su yi aikin firist. 4 Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sina'i, a sa'ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da 'ya'ya, saboda haka Ele'azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna. 5 Ubangiji ya ce wa Musa, 6 “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist. 7 Sai su yi wa firistoci da dukan jama'a aiki a gaban alfarwa ta sujada. 8 Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra'ilawa aiki. 9 Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da 'ya'yansa aiki. 10 Ka sa Haruna da 'ya'yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.” 11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 12 “Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa. 13 Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.” 14 Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sina'i, ya ce masa 15 ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba. 16 Haka Musa ya ƙidaya su bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda ya umarce shi. 17 Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari. 18 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai. 19 Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. 20 Ga kuma 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, da Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawi bisa ga gidajen kakanninsu. 21 Iyalin Libnawa, da na Shimaiyawa su ne iyalan Gershon. 22 Jimillarsa tun daga ɗa namiji mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu bakwai ne da ɗari biyar (7,500 ). 23 Iyalan Gershonawa za su yi zango a bayan alfarwar daga yamma. 24 Eliyasaf, ɗan Layel, shi ne shugaban gidan kakanninsa, Gershonawa. 25 'Ya'yan Gershon, maza, su ne da aikin lura da alfarwa ta sujada da murfinta na ciki da na waje, da labulen ƙofar, 26 da labulen farfajiya da yake kewaye da alfarwar, da bagade, da labulen ƙofar farfajiyar. Su za su lura da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa. 27 Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa. 28 Lissafin mazaje duka, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, su dubu takwas ne da ɗari shida (8,600 ). 29 Iyalan 'ya'yan Kohat za su kafa zangonsu a kudancin alfarwar. 30 Elizafan ɗan Uzziyel shi ne shugaban gidan kakanninsa, Kohatawa. 31 Aikinsu shi ne lura da akwatin alkawari, da tebur, da alkuki, da bagadai, da kayayyakin Wuri Mai Tsarki waɗanda firistoci suke aiki da su, da labule, da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa. 32 Ele'azara, ɗan Haruna, firist, shi zai shugabanci shugabannin Lawiyawa, shi ne kuma zai lura da waɗanda suke aiki a Wuri Mai Tsarki. 33 Iyalan Merari su ne iyalin Maliyawa, da na Mushiyawa. Waɗannan su ne iyalan Merari. 34 Yawan mazajensu duka da aka ƙidaya tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu shida ne da ɗari biyu (6,200 ). 35 Shugaban gidan kakannin iyalan Merari kuwa shi ne Zuriyel, ɗan Abihail. Za su kafa zangonsu a arewacin alfarwar. 36 Aikin da aka danƙa wa 'ya'yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan, 37 da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu. 38 Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi. 39 Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000 ).

An Fanshi 'Ya'yan Fari Maza

40 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu. 41 Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.” 42 Sai Musa ya ƙidaya 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 43 Jimillar 'ya'yan fari maza da aka ƙidaya bisa ga sunayensu tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu ashirin da biyu, da ɗari biyu da saba'in da uku ne (22,273 ). 44 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce, 45 “Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji. 46 'Ya'yan fari maza na Isra'ilawa sun fi Lawiyawa da mutum ɗari biyu da saba'in da uku. Sai a fanshi wannan ragowa. 47 Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 48 Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da 'ya'yansa maza.” 49 Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa. 50 Kuɗin da ya karɓa daga 'ya'yan fari na Isra'ilawa da suka haura yawan Lawiyawa shekel dubu ɗaya da ɗari uku da sittin da biyar (1,365 ) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 51 Musa kuwa ya ba Haruna da 'ya'yansa maza kuɗin fansa bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Littafin Ƙidaya 4

Ayyukan da aka Danƙa wa Iyalin Kohat

1 Ubangiji ya faɗa wa Musa da Haruna, 2 su ƙidaya 'ya'yan Kohat, maza, daga cikin 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, 3 su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada. 4 Wannan shi ne aikin 'ya'yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki. 5 Sa'ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da 'ya'yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi. 6 Sa'an nan kuma su rufe shi da fatun awaki, su kuma shimfiɗa shuɗin zane a bisansa, su zura masa sandunansa. 7 Sai su shimfiɗa shuɗin zane a kan tebur na gurasar ajiyewa, sa'an nan su d�biya faranta, da cokula, da kwanonin, da butocin hadaya ta sha, da gurasar ajiyewa. 8 Sa'an nan su rufe su da jan zane, a kuma rufe su da fatun awaki, sa'an nan su zura masa sandunansa. 9 Su kuma ɗauki shuɗin zane su rufe alkuki, da fitilunsa, da hantsukansa, da farantansa, da dukan kwanonin man da akan zuba masa. 10 Sai su sa alkukin da dukan kayayyakinsa a cikin fatar awaki su naɗe, su sarƙafa shi asandan ɗaukarsa. 11 A rufe bagaden zinariya da shuɗin zane, a kuma rufe shi da fatun awaki, sa'an nan a zura sandunan ɗaukarsa. 12 Su ɗauki dukan kwanonin da ake amfani da su a Wuri Mai Tsarki, su sa su cikin shuɗin zane, sa'an nan su rufe su da fatun awaki, a sarƙafa su a sanda don a ɗauka. 13 Za su kwashe tokar da take cikin bagaden, su rufe bagaden da shunayyan zane. 14 Sa'an nan su sa dukan kayayyakin bagaden a kansa waɗanda ake aiki da su a wurin, wato su farantai don wuta, da cokula masu yatsotsi, da manyan cokula, da daruna da dai dukan kayayyakin bagaden. Su kuma rufe bagaden da fatun awaki, sa'an nan su zura sandunan ɗaukarsa. 15 Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada. 16 Ele'azara kuwa, ɗan Haruna, firist, shi ne zai lura da man fitila, da turare, da hadayar gari ta kullum, da man keɓewa, ya kuma kula da dukan alfarwar, da duk abin da ke cikinta, da Wuri Mai Tsarki, da kayayyakinsa. 17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 18 “Kada ku bar zuriyar Kohat 19 ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da 'ya'yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka. 20 Amma idan Kohatawa suka shiga alfarwar suka tarar firistoci suna shisshirya tsarkakakkun abubuwa don tashi, har dai in sun gani, to za su mutu.”

Ayyukan Gershonawa

21 Ubangiji ya kuma faɗa wa Musa, 22 ya ƙidaya 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu 23 ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada. 24 Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi wajen ɗaukar kaya. 25 Za su ɗauki alfarwa ta sujada, da labule na ciki da na waje, da murfi na fatun tumaki wanda yake a bisa alfarwar, da kuma labulen ƙofar alfarwa ta sujada, 26 da labulen farfajiya, da labulen ƙofar farfajiya wadda ta kewaye alfarwar da bagaden, da igiyoyinsu, da duk kayayyakinsu na yin aiki. Sai su yi dukan abin da ya kamata a yi da su. 27 Haruna ne da 'ya'yansa maza za su nuna wa 'ya'yan Gershonawa irin aikin da za su yi, da kayayyakin da za su ɗauka. Sai a faɗa musu dukan abin da za su yi, da dukan abinda za su ɗauka. 28 Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi zai shugabance su cikin aikin da za su yi.

Ayyukan Merariyawa

29 Ubangiji kuma ya faɗa wa Musa ya ƙidaya Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, 30 ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada. 31 Wannan shi ne abin da aka umarce su su riƙa ɗauka na wajen aikinsu a alfarwa ta sujada, katakan alfarwar, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta, 32 da dirkokin farfajiya wadda take kewaye da alfarwar, da kwasfansu, da turakunsu, da igiyoyi, da dukan kayayyakinsu. Sai ya faɗa wa kowa kayan da zai ɗauka. 33 Wannan shi ne aikin iyalan 'ya'yan Merari, maza. Aikinsu ke nan duka a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi ne zai shugabance su.

Yawan Lawiyawa

34-48 Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750 ), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630 ), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200 ), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580 ). 49 Aka ba kowannensu aikinsa da ɗaukar kaya bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa. Haka kuwa aka ƙidaya su kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Littafin Ƙidaya 5

Ƙazantattun Mutane

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka umarci Isra'ilawa su fitar da kuturu, da mai ɗiga, da wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin zango. 3 Su fitar da mace ko namiji daga cikin zango, don kada su ƙazantar da zangonku inda nake zaune.” 4 Sai Isra'ilawa suka fitar da su daga cikin zango kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Haka mutanen Isra'ila suka yi.

Biyan Diyya saboda Ɓarna

5 Ubangiji kuma ya ba Musa 6 waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan wani ya aikata rashin gaskiya ga Ubangiji, ta wurin saɓa wa wani, 7 sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin. 8 Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa. 9 Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa. 10 Kowane firist zai adana sadakokin da aka ba shi.

Matsalar Miji mai Kishi

11 Ubangiji kuma ya umarci Musa faɗa wa Isra'ilawa waɗannan ka'idodi. Idan mutum yana shayin matarsa kan tana yi masa rashin aminci, har ta ƙazantar da kanta ta wurin kwana da wani mutum, amma mijin bai tabbatar ba, domin ta yi abin a asirce, ba kuwa mai shaida, ba a kuma kama ta tana cikin yi ba, ko kuma mijin ya yi shayinta ko da ba ta aikata irin wannan laifi ba, 15 duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha'ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili. 16 Sai firist ya kawo ta kusa, ya tsai da ita a gaban Ubangiji. 17 Ya ɗebo ruwa mai tsarki a cikin kasko, ya kuma ɗauki ƙurar ƙasar da take a alfarwa ta alkawari ya zuba a ruwan. 18 Sa'an nan firist zai kwance gashin kanta, ya sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi. Ya riƙe ruwan nan mai ɗaci da yake kawo la'ana a hannunsa. 19 Sa'an nan zai sa ta ta yi rantsuwa, ya ce mata, “Idan wani mutum bai kwana da ke ba, to, bari ki kuɓuta daga la'anar da ruwan nan mai ɗaci zai kawo. 20 Amma idan kin kwana da wani mutum wanda ba mijinki ba ne, 21 bari Ubangiji ya sa sunanki ya la'antu cikin jama'arki, ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbure. 22 Bari ruwan nan ya shiga cikinki, ya sa cikinki ya kumbure, cinyarki kuma ta shanye.” Sai matar ta amsa, ta ce, “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka.” 23 Firist ɗin zai rubuta waɗannan la'anoni a cikin littafi sa'an nan ya wanke rubutun da ruwan nan mai ɗaci. 24 Ya sa matar ta shanye ruwa wanda yake kawo la'ana, sai ruwan ya shiga cikinta, ya zama la'ana mai ɗaci. 25 Firist kuma zai karɓi hadaya ta gari don kishi a hannun matar, ya kaɗa ta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ya kai wurin bagade. 26 Sai ya ɗibi garin hadaya cike da tafin hannu don yin hadayar tunawa, ya ƙone shi a bisa bagaden, bayan wannan ya sa matar ta sha ruwan. 27 Bayan da ya sa ta ta sha ruwan, idan ta ƙazantar da kanta, ta kuwa ci amanar mijinta, ruwan nan mai kawo la'ana zai shiga cikinta ya zama la'ana mai ɗaci, cikinta zai kumbure, cinyarta ta shanye, matar kuwa za ta zama la'ananniya cikin jama'arta. 28 Amma idan matar ba ta ƙazantar da kanta ba, ita tsattsarka ce, za ta kuɓuta, har ta haifi 'ya'ya. 29 Wannan ita ce dokar kishi idan mutum yana shayin matarsa, wai wani yana kwana da ita. 30 Matar kuwa za ta tsaya a gaban Ubangiji, firist kuwa zai yi da ita bisa ga wannan doka duka. 31 Mijin zai kuɓuta daga muguntar, amma matar za ta ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.

Littafin Ƙidaya 6

Ka'idodin Zama Keɓaɓɓe

1 Ubangiji kuma ya umarci Musa 2 ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa idan mace ko namiji ya ɗau wa'adi na musamman na zama keɓaɓɓe domin ya keɓe kansa ga Ubangiji, 3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da 'ya'yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun 'ya'yan inabi. 4 A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa. 5 A dukan kwanakin wa'adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo. 6 A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa. 7 Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan'uwansa, ko ta 'yar'uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa. 8 Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa. 9 Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai. 10 A rana ta takwas kuwa zai kawo wa firist 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 11 Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa. 12 Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu. 13 Wannan ita ce ka'idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada, 14 ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama, 15 da kwandon abinci marar yisti da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da ƙosai wanda aka yayyafa masa mai, da hadaya ta gari, da hadayu na sha. 16 Sai firist ɗin ya kai su gaban Ubangiji, ya miƙa hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa. 17 Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha. 18 Sai kuma keɓaɓɓen ya aske sumarsa a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya kwashe sumar, ya zuba cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama. 19 Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa. 20 Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi. 21 Wannan ita ce ka'ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa'adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa'adin da ya ɗauka bisa ga ka'idar keɓewarsa.

Albarkar da Firist zai Sa wa Jama'a

22 Ubangiji ya umarci Musa 23 ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, su sa wa Isra'ilawa albarka haka, su ce musu, 24 “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku. 25 Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri. 26 Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama.” 27 Idan suka sa wa jama'a wannan albarka sa'ad da suke addu'a ga Ubangiji domin Isra'ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.

Littafin Ƙidaya 7

Hadayun Keɓe Bagade

1 A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa. 2 Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya, 3 suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su, 4 sai Ubangiji ya ce wa Musa, 5 “Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.” 6 Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa. 7 Ya ba 'ya'ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu. 8 Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist. 9 Amma bai ba 'ya'ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa. 10 Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden, 11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.” miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Kabila Shugaba Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama. 84-88 Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden: farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗu cokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshi bijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da 'yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawa awaki goma sha biyu domin hadaya don zunubi bijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da 'yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama. 89 Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.

Littafin Ƙidaya 8

Haruna ya Kakkafa Fitilu

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa ya 2 faɗa wa Haruna cewa, “Sa'ad da za ka kakkafa fitilun nan bakwai, sai ka kakkafa su yadda za su haskaka sashin gaba.” 3 Haka kuwa Haruna ya yi. Ya kakkafa fitilun yadda za su haskaka a gaban alkukin, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 4 Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.

Keɓewar Lawiyawa

5 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 6 “Keɓe Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa ka tsarkake su. 7 Ga yadda za ka tsarkake su. Ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa. Su aske jikunansu duka, su kuma a wanke tufafinsu, sa'an nan za su tsarkaka. 8 Su kuma ɗauki maraƙi tare da lallausan garin hadaya kwaɓaɓɓe da mai. Kai kuma ka ɗauki wani maraƙi na yin hadaya don zunubi. 9 Sa'an nan ka gabatar da Lawiyawa a gaban alfarwa ta sujada, ka kira taron Isra'ilawa duka. 10 Sa'ad da ka gabatar da Lawiyawa a gaban Ubangiji, sai Isra'ilawa su ɗibiya hannuwansu bisa Lawiyawa. 11 Haruna kuma zai gabatar da Lawiyawan a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa daga Isra'ilawa domin su zama masu yi wa Ubangiji aiki. 12 Sa'an nan Lawiyawa za su ɗibiya hannuwansu a bisa kawunan maruƙan. Za ka yi hadaya domin zunubi da maraƙi ɗaya, ɗaya kuma ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji domin ka yi kafara saboda Lawiyawa. 13 “Za ka keɓe Lawiyawa su zama kamar hadaya ta kaɗawa gare ni, ka sa Haruna da 'ya'yansa maza su lura da su. 14 Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa su zama nawa. 15 Bayan da ka tsarkake su, ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, za su cancanta su yi aiki a alfarwa ta sujada. 16 Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra'ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato dukan 'ya'yan farin Isra'ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa. 17 A ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa, na mutum, da na dabba. 18 Na kuwa keɓe wa kaina Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. 19 Daga cikin Isra'ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza don su yi wa Isra'ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra'ilawa sa'ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.” 20 Musa da Haruna kuwa da dukan taron Isra'ilawa suka yi wa Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarce Musa, haka kuwa Isra'ilawa suka yi musu. 21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka wanke tufafinsu. Haruna kuwa ya keɓe su, suka zama kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji, ya kuma yi kafara dominsu don ya tsarkake su. 22 Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da 'ya'yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.

Adadin yawan Shekarun Aikin Lawiyawa

23 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 24 “Wannan ita ce ka'idar aikin Lawiyawa, tun daga mai shekara ashirin da biyar zuwa gaba, zai shiga yin aiki a alfarwa ta sujada. 25 Amma daga shekara hamsin, sai su huta daga aiki alfarwa ta sujada. 26 Amma su taimaki 'yan'uwansu da tafiyar da ayyuka a cikin alfarwa ta sujada, sai dai ba za su ɗauki nauyin gudanar da aikin ba. Haka za ka shirya wa Lawiyawa aikinsu.”

Littafin Ƙidaya 9

Idin Ƙetarewa na Biyu

1 Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sina'i a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce, 2 “Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa. 3 A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.” 4 Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa. 5 Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sina'i bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi. 6 Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum, don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar, 7 suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran 'yan'uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?” 8 Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.” 9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa 10 ya faɗa wa Isra'ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji. 11 Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci. 12 Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa. 13 Amma mutumin da yake da tsarki, bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi kiyaye Idin Ƙetarewa, sai a raba wannan mutum da jama'arsa, gama bai miƙa hadayar Ubangiji a ƙayyadadden lokacin yinta ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa. 14 “Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka'idodi na Idin Ƙetarewa. Ka'ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”

Girgijen Wuta

15-16 A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta. 17 A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango. 18 Da umarnin Ubangiji Isra'ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon. 19 Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji. 20 Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji. 21 Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. 22 Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi. 23 Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.

Littafin Ƙidaya 10

Kakaki na Azurfa

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 2 “Ka ƙera kakaki biyu na azurfa don ka riƙa kirawo taron jama'a, don kuma ka riƙa sanashe su lokacin tashi daga zangon. 3 Lokacin da aka busa kakaki biyu ɗin gaba ɗaya, sai taron jama'a duka su tattaru a wurinka a ƙofar alfarwa ta sujada. 4 Amma idan ɗaya kaɗai aka busa, sai shugabannin Isra'ila su tattaru a wurinka. 5 Sa'ad da kuka yi busar faɗakarwa, waɗanda suke zaune a gabashin zangon za su tashi. 6 Sa'ad da kuma kuka yi busar faɗakarwa ta biyu, waɗanda suke a kudancin zangon za su tashi. Sai a yi busar faɗakarwa a kowane lokaci da za su tashi. 7 Amma idan za a kira jama'a ne sai a yi busa da ƙarfi amma banda faɗakarwa. 8 'Ya'yan Haruna, maza, firistoci, su ne za su busa kakakin. “Kakakin za su zama muku ka'ida ta din din din cikin dukan zamananku. 9 Sa'ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku. 10 A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Tashin Isra'ilawa daga Sina'i

11 A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada. 12 Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sina'i. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran. 13 Suka fara tafiyarsu bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa. 14 Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu. 15 Shugaban rundunar kabilar mutanen Issaka Netanel ne, ɗan Zuwar. 16 Shugaban rundunar kabilar mutanen Zabaluna Eliyab ne, ɗan Helon. 17 Sa'an nan aka kwankwance alfarwar, sai 'ya'yan Gershon, da 'ya'yan Merari masu ɗaukar alfarwar suka kama hanya. 18 Tutar zangon kabilar mutanen Ra'ubainu ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Elizur ne, ɗan Shedeyur. 19 Shugaban rundunar kabilar mutanen Saminu kuwa Shelumiyel ne, ɗan Zurishaddai. 20 Shugaban rundunar kabilar mutanen Gad Eliyasaf ne, ɗan Deyuwel. 21 Daganan sai Kohatawa masu ɗauke da kayayyaki masu tsarki suka tashi. Kafin su isa masaukin, an riga an kafa alfarwar. 22 Tutar zangon mutanen Ifraimu ta tashi, ƙungiyoyinsu na biye. Shugaban rundunarsu Elishama ne, ɗan Ammihud. 23 Shugaban rundunar kabilar mutanen Manassa Gamaliyel ne, ɗan Fedazur. 24 Shugaban rundunar kabilar mutanen Biliyaminu Abidan ne, ɗan Gideyoni. 25 A ƙarshe sai ƙungiyar mutanen Dan da take bayan dukan zangon, ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Ahiyezer ne, ɗan Ammishaddai. 26 Shugaban rundunar kabilar mutanen Ashiru Fagiyel ne, ɗan Okran. 27 Shugaban rundunar kabilar mutanen Naftali Ahira ne, ɗan Enan. 28 Wannan shi ne tsarin tafiyar Isra'ilawa bisa ga rundunansu sa'ad da sukan tashi. 29 Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamadayane, surukinsa, “Muna kan hanya zuwa wurin da Ubangiji ya ce zai ba mu, ka zo tare da mu, za mu yi maka alheri, gama Ubangiji ya alkawarta zai yi wa Isra'ila alheri.” 30 Amma ya ce masa, “Ba zan tafi ba, zan koma ƙasata da wurin dangina.” 31 Musa kuwa ya ce masa, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu, gama ka san jejin da muke zango, kai za ka zama idonmu. 32 Idan ka tafi tare da mu, kowane irin alheri da Ubangiji zai yi mana, mu kuma haka za mu yi maka.”

Mutanen suka Kama Hanya

33 Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sina'i, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki. 34 A duk lokacin da suka tashi daga zango, sai girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana. 35 Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.” 36 Sa'ad da akwatin ya sauka kuma, Musa yakan ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubun dubbai na iyalan Isra'ila.”

Littafin Ƙidaya 11

Ubangiji zai Ba su Nama

1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon. 2 Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu. 3 Aka sa wa wurin suna Tabera, wato matoya, domin wutar Ubangiji ta yi ƙuna a cikinsu. 4 Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra'ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci? 5 Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa. 6 Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.” 7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne. 8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai. 9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon. 10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai. 11 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina? 12 Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’ 13 A ina zan samo nama da zan ba wannan jama'a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’ 14 Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina. 15 Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.” 16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai. 17 Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai. 18 Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci. 19 Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba. 20 Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda ke tare da su, suka yi gunaguni a gabansa, suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ” 21 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000 ) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur. 22 Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?” 23 Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”

Shugabanni sun yi Annabci

24 Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama'a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba'in daga cikin jama'ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar. 25 Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba. 26 Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon. 27 Sai wani saurayi ya sheƙa a guje ya faɗa wa Musa, ya ce, “Ga Eldad da Medad suna nan suna annabci a cikin zangon.” 28 Joshuwa ɗan Nun, mai yi wa Musa barantaka, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun, ya ce, “Ya shugabana, Musa, ka hana su.” 29 Amma Musa ya ce masa, “Kishi kake yi domina? Da ma jama'ar Ubangiji duka annabawa ne, har ma ya sa Ruhunsa a cikinsu!” 30 Sai Musa da dattawan Isra'ila suka koma zango.

Ubangiji ya Aiko da Makware

31 Sai iska ta huro daga wurin Ubangiji, ta koro makware daga teku, ta bar su birjik kusa da zango, misalin nisan tafiyar yini guda ta kowace fuska. Tsayin tashinsu daga ƙasa misalin kamu biyu ne. 32 Sai mutane suka tashi suka yi ta tattara makware dukan wannan yini, da dukan dare, har kashegari duka. Wanda ya tattara kaɗan, ya tara garwa metan. Suka shanya abinsu kewaye da zangon. 33 Tun suna cikin cin naman, sai Ubangiji ya husata da mutanensa, ya bugi jama'a da annoba mai zafi. 34 Don haka aka sa wa wurin suna Kibrot-hata'awa, wato makabarta, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita. 35 Daga Kibrot-hata'awa mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.

Littafin Ƙidaya 12

Aka Hukunta Maryamu

1 Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura. 2 Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji. 3 (Musa dai mai tawali'u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.) 4 Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi. 5 Ubangiji kuwa ya zo cikin al'amudin girgije, ya tsaya a ƙofar alfarwar, ya yi kira, “Haruna! Maryamu!” Su biyu fa suka gusa gaba. 6 Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki. 7 Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila. 8 Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?” 9 Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su. 10 Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa. 11 Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta. 12 Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.” 13 Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.” 14 Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.” 15 Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon. 16 Bayan wannan jama'a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.

Littafin Ƙidaya 13

'Yan Leƙen Asirin Ƙasa

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 2 “Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan'ana wadda nake ba Isra'ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.” kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu. Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza. Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu. Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan. Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru. Nabi ɗan Wofsi, daga kabilar Naftali. Geyuwel ɗan Maci, daga kabilar Gad. 16 Waɗannan su ne mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar. Amma Musa ya ba Hosheya, ɗan Nun, suna Joshuwa. 17 Sa'ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan'ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai, 18 ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanenta ƙarfafa ne, ko raunana ne, ko su kima ne, ko kuwa suna da yawa, 19 ko ƙasa tasu mai ni'ima ce, ko babu, ko biranensu marasa garu ne, ko masu garu ne, 20 ko ƙasar tana da wadata, ko matalauciya ce, ko ƙasar kurmi ce, ko fili. Ku yi jaruntaka, ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Gama lokacin farkon nunan inabi ne.) 21 Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat. 22 Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.) 23 Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da 'ya'ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure. 24 Aka kira wurin Kwarin Eshkol, wato “Nonon inabi,” saboda nonon inabi wanda 'yan leƙen ƙasa suka yanko a wurin. 25 Bayan sun yi kwana arba'in suna leƙen asirin ƙasar, sai suka komo. 26 Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo. 27 Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar. 28 Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can. 29 Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.” 30 Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.” 31 Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.” 32 Haka suka kawo wa 'yan'uwansu, Isra'ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne. 33 Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”

Littafin Ƙidaya 14

Mutane suka yi Yaji

1 Sai dukan taron jama'a suka yi kuka da babbar murya dukan dare saboda wahala. 2 Dukan Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji. 3 Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?” 4 Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.” 5 Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa. 6 Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda ke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu. 7 Suka ce wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske. 8 Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita. 9 Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da ke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.” 10 Amma taron jama'a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra'ila daga cikin alfarwa ta sujada. 11 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu? 12 Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al'umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.” 13 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka. 14 Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta. 15 Idan kuwa ka kashe jama'ar nan gaba ɗaya, sai al'umman da suka ji labarinka, su ce, 16 ‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama'ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’ 17 Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa, 18 ‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’ 19 Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama'a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.” 20 Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta. 21 Amma, hakika, na rantse da zatina, kamar yadda ɗaukakata za ta cika duniya duka, 22 dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba, 23 ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba, 24 sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai. 25 Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan'aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”

Ubangiji ya Hukunta Jama'ar saboda Gunaguni

26 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, 27 “Har yaushe wannan mugun taron jama'a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra'ilawa suka yi a kaina. 28 Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku. 29 Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, 30 ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun. 31 Amma 'yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina. 32 Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin. 33 'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin. 34 Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba. 35 Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama'a da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ” 36 Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama'a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, 37 mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji. 38 Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.

Ƙoƙarin Cin Ƙasar na Farko ya Kāsa

39 Da Musa ya faɗa wa Isra'ilawa abin da Ubangiji ya ce, sai jama'a suka yi baƙin ciki ƙwarai. 40 Suka tashi da sassafe, suka hau kan tudu, suna cewa, “Ga shi, a shirye muke mu tafi wurin da Ubangiji ya ambata, gama mun yi kuskure.” 41 Amma Musa ya ce, “Me ya sa kuke karya umarnin Ubangiji? Yin haka ba zai kawo nasara ba. 42 Kada ku haura domin kada ku sha ɗibga a gaban maƙiyanku, gama Ubangiji ba ya tare da ku. 43 Gama akwai Amalekawa da Kan'aniyawa a gabanku, za su kashe ku da takobi domin kun bar bin Ubangiji, don haka Ubangiji ba zai kasance tare da ku ba.” 44 Amma sai suka yi izgili, suka haura kan tudun, amma akwatin alkawari da Musa ba su bar zangon ba. 45 Sai Amalekawa da Kan'aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.

Littafin Ƙidaya 15

Ka'idodin Yin Hadayu

1 Ubangiji ya ba Musa 2 waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa su kiyaye su a ƙasar da zai ba su. 3 Sa'ad da za su yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji daga cikin garken shanu, ko na tumaki da awaki, ko hadaya ta ƙonawa ce, ko ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, ko ta ƙayyadaddun idodinsu ce, don a ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, 4 sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu'in moɗa na mai. 5 Ya kuma shirya hadaya ta sha, rubu'in moɗa ta ruwan inabi domin kowane ɗan rago na hadaya ta ƙonawa. 6 Idan kuwa da rago ne, a shirya hadaya ta gari humushi biyu na garwa, a kwaɓa da sulusin moɗa na mai. 7 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 8 Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa'adi, ko ta salama ga Ubangiji, 9 sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai. 10 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 11 Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru. 12 Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu. 13 Haka dukan waɗanda suke 'yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 14 Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko kowanene da ke tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi. 15 Ka'ida ɗaya ce domin taron jama'a da kuma baƙin da ke zaune tare da su. Ka'ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake. 16 Ka'ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da suke baƙunci a cikinsu. 17 Ubangiji ya ba Musa 18 waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa su kiyaye a ƙasar da zai ba su. 19 Sa'ad da suke cin amfaninta, sai su miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. 20 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari sai su yi wainar da za su ɗaga don yin hadaya da amfanin masussuka. 21 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari, sai su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa a dukan zamanansu. 22 Amma idan sun yi kuskure, ba su kiyaye dukan umarnan nan waɗanda Ubangiji ya faɗa wa Musa ba, 23 wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu, 24 idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi. 25 Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama'ar Isra'ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu. 26 Za a gafarta wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi. 27 Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi. 28 Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa. 29 Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu. 30 Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi, 31 gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

Jajjefewar Wanda ya Ɓata Ranar Asabar

32 Sa'ad da Isra'ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar. 33 Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'a. 34 Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna. 35 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama'a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.” 36 Dukan taron jama'a suka kai shi bayan zangon, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Dokoki a kan Tuntayen Riguna

37 Ubangiji ya umarci Musa ya ce, 38 “Ka faɗa wa Isra'ilawa su yi wa shafin rigunansu tuntaye a dukan zamananku. A kan kowane tuntu, su sa shuɗin zare. 39 Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha'awar idanunsu yadda suka taɓa yi. 40 Da haka za su riƙa tunawa, su aikata dukan umarnaina su zama tsarkakakku gare ni. 41 Gama ni ne Ubangiji Allahnku, na fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Littafin Ƙidaya 16

Tayarwar Kora, da Datan, da Abiram

1-2 Sai Kora, ɗan Izhara, na kabilar Lawi, iyalin Kohat, ya yi ƙarfin hali ya tayar wa Musa. Waɗansu uku kuma daga kabilar Ra'ubainu suka haɗa kai da shi, su ne Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, da On, ɗan Felet, da waɗansu Isra'ilawa su ɗari biyu da hamsin, sanannun shugabanni da jama'a suka zaɓa. 3 Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama'a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama'ar Ubangiji?” 4 Da Musa ya ji wannan, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu'a. 5 Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade. 6 Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare. 7 Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!” 8 Musa ya ci gaba da magana da Kora. “Ku Lawiyawa ku kasa kunne! 9 Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra'ila ya keɓe ku daga cikin jama'ar Isra'ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu aiki? 10 Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan 'yan'uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist! 11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!” 12 Musa kuwa ya aika a kirawo Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, “Ba za mu zo ba! 13 Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu? 14 Banda wannan kuma, ga shi, ba ka kai mu zuwa cikin ƙasa mai yalwar abinci ba, ba ka ba mu gonaki da gonakin inabi domin mu gāda ba, yanzu kuwa kana so ka ruɗe mu, to, ba za mu zo ba sam!” 15 Musa kuwa ya husata ƙawarai da gaske, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace ko jakinsu ba, ban kuwa cuce su ba.” 16 Musa ya ce wa Kora, “Kai da ƙungiyarka duka ku hallara a gaban Ubangiji gobe, da kai, da su, da Haruna. 17 Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.” 18 Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna. 19 Sai Kora ya tara dukan taron jama'a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama'ar. 20 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, 21 “Ku ware kanku daga cikin taron jama'ar nan, ni kuwa in hallaka su nan take.” 22 Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?” 23 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 24 “Ka faɗa wa jama'a su tashi, su nisanci alfarwar Kora, da ta Datan, da ta Abiram.” 25 Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa. 26 Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.” 27 Sai jama'a suka tashi daga inda Kora, da Datan, da Abiram suke zama. Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofar alfarwansu tare da matansu da 'ya'yansu, da 'yan ƙananansu. 28 Sai Musa ya ce, “Da haka za ku sani Ubangiji ne ya aiko ni, in yi waɗannan ayyuka, ba da nufin kaina na yi su ba. 29 Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane ke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba. 30 Amma idan Ubangiji ya aikata wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara zuwa cikin lahira a raye, sa'an nan za ku sani mutanen nan sun raina Ubangiji.” 31 Musa ya rufe bakinsa ke nan, sai wurin da Datan da Abiram suke tsaye, ƙasar ta dāre 32 ta haɗiye su tare da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan mallakarsu. 33 Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai. 34 Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu, kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.” 35 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare. 36 Ubangiji ya ce wa Musa, 37 “Ka faɗa wa Ele'azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne. 38 Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.” 39 Sai Ele'azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su. 40 Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.

Haruna ya Ceci Jama'a

41 Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.” 42 Da taron jama'ar suka haɗa kai gāba da Musa da Haruna, sai suka fuskanci alfarwa ta sujada. Ga girgije yana rufe da alfarwar, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana. 43 Sai Musa da Haruna suka tafi wajen ƙofar alfarwa ta sujada. 44 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa, ya ce, 45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzun nan zan hallaka su.” Sai suka fāɗi rubda ciki. 46 Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki farantin turare, ka cika shi da wuta daga bagade, ka zuba turaren wuta a ciki, ka tafi da sauri wurin taron, ka yi kafara dominsu, gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko, an fara annoba.” 47 Sai Haruna ya ɗauko farantin turaren, ya yi yadda Musa ya ce. Ya sheƙa a guje a tsakiyar taron jama'a. Amma an riga an fara annobar a cikin jama'a. Sai ya zuba turare, ya yi kafara domin jama'a. 48 Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya. 49 Waɗanda annoba ta kashe mutum dubu goma sha huɗu ne da ɗari bakwai (14,700 ), banda waɗanda suka mutu a sanadin Kora. 50 Sai Haruna ya koma wurin Musa a ƙofar alfarwa ta sujada, gama annobar ta ƙare.

Littafin Ƙidaya 17

Sandan Haruna

1 Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce, 2 “Ka faɗa wa Isra'ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa. 3 Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu. 4 Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai. 5 Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra'ilawa suke yi a kaina ya ƙare.” 6 Musa kuwa ya yi magana da Isra'ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan. 7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji cikin alfarwa ta sujada. 8 Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi 'ya'yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa. 9 Musa kuwa ya fito wa Isra'ilawa da dukan sandunan da aka ajiye a gaban Ubangiji. Suka duba, kowanne ya ɗauki sandansa. 10 Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.” 11 Haka kuwa Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. 12 Isra'ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace. 13 Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”

Littafin Ƙidaya 18

Ayyukan Lawiyawa da Firistoci

1 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da 'ya'yanka, da gidan mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi alfarwa ta sujada. Kai da 'ya'yanka kuma za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci. 2 Ka kawo 'yan'uwanka tare da kai, wato kabilar Lawi, kakanka, don su yi muku aiki sa'ad da kai da 'ya'yanka kuke gaban alfarwa ta sujada. 3 Za su taimake ku, su kuma yi dukan ayyukan alfarwa. Amma fa, ba za su kusaci kayayyakin Wuri Mai Tsarki, ko bagade ba, don kada su, har da ku, ku mutu. 4 Za su haɗa kai da ku su lura da alfarwa ta sujada da dukan aikace-aikace na cikin alfarwar. Kada wani dabam ya kusace ku. 5 Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra'ilawa. 6 Ga shi, ni na ɗauki 'yan'uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada. 7 Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”

Rabon Firistoci

8 Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra'ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na 'ya'yanka har abada. 9 Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na 'ya'yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi. 10 A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka. 11 “Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra'ilawa ke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da 'ya'yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci. 12 “Duk mai mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan fari, waɗanda suke bayarwa ga Ubangiji, na ba ku. 13 Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa. 14 “Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra'ila zai zama naka. 15 “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. 16 Sai ka fanshe su suna 'yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 17 Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji. 18 Naman kuwa zai zama naka, duk da ƙirji na kaɗawa da cinyar dama da aka miƙa su hadaya ta kaɗawa. 19 “Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra'ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da 'ya'yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.” 20 Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra'ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra'ilawa.”

Rabon Lawiyawa

21 Ubangiji ya ce, “Na ba Lawiyawa kowace zaka ta Isra'ilawa gādo saboda aikinsu da suke ya a alfarwa ta sujada. 22 Nan gaba kada Isra'ilawa su zo kusa da alfarwa ta sujada don kada su yi zunubi, su mutu. 23 Gama Lawiyawa ne kaɗai za su yi aikin alfarwa ta sujada, wannan alhakinsu ne. Wajibi ne kuma ga zuriyarsu a kowane lokaci. Lawiyawa ba su da gādo tare da Isra'ilawa. 24 Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra'ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra'ilawa.”

Zaka

25 Ubangiji ya ce wa Musa, 26 “Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa'ad da suka karɓi zaka daga Isra'ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa. 27 Za a lasafta hadayarku ta ɗagawa kamar hatsinku ne da kuka sussuka a masussuka, da kuma kamar cikakken amfanin ruwan inabin da kuka samu a wurin matsewar inabinku. 28 Haka za ku miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji daga cikin dukan zakar da kuke karɓa daga wurin Isra'ilawa. Daga ciki za ku ba da hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji ta hannun Haruna, firist. 29 Daga dukan kyautar da ake kawo muku, za ku ba Ubangiji hadaya ta ɗagawa daga mafi kyau da kuke samu. 30 Domin haka kuwa sai ka ce musu, ‘Sa'ad da kuka ɗaga mafi kyau daga cikinta duka, sai ragowar ta zama ta Lawiyawa kamar abin da ya fito daga masussuka, da wurin matsewar inabinsu. 31 Za ku iya cinta ko'ina da kuka ga dama, ku da iyalan gidajenku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a alfarwa ta sujada. 32 Ba kuwa za ta zama muku sanadin zunubi ba, in dai har kuka ɗaga mafi kyau duka. Ba za ku ɓata tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa ba, don kada ku mutu.’ ”

Littafin Ƙidaya 19

Tsarkakewar Marasa Tsarki

1 Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce, 2 “Wannan ita ce ka'ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra'ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba. 3 Sai ka ba Ele'azara firist ita, sa'an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa. 4 Ele'azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada. 5 Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta. 6 Firist zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar. 7 Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice. 8 Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice. 9 Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama'ar Isra'ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi. 10 Shi kuma wanda ya tara tokar karsanar, sai ya wanke tufafinsa zai ƙazantu har maraice. Wannan ka'ida ce ta har abada ga Isra'ilawa da baƙin da ke zama tare da su.”

Taɓa Gawa

11 “Duk wanda ya taɓa gawa zai ƙazantu har kwana bakwai. 12 A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba. 13 Duk wanda ya taɓa gawa, bai kuwa tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, ba za a lasafta shi cikin mutanen Allah ba, domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba. 14 “Wannan ita ce ka'ida a kan wanda ya rasu a alfarwa, duk wanda ya shiga alfarwar, da duk wanda yake cikin alfarwar zai ƙazantu har kwana bakwai. 15 Kowace buɗaɗɗiyarsa kuma wadda ba a rufe ba, za ta ƙazantu. 16 Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai. 17 “Don a tsarkake ƙazantar, sai a ɗiba daga cikin tokar hadaya don zunubi a cikinsa, sa'an nan a zuba ruwa mai gudu. 18 Tsarkakakken mutum zai ɗauki ɗaɗɗoya ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar, da bisa kan dukan kayayyakin da suke ciki, da a kan mutanen da suke a wurin, da kan wanda ya taɓa ƙashin, ko ya taɓa wanda aka kashe, ko ya taɓa gawa, ko kabari. 19 A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka. 20 “Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama'ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba. 21 Wannan zai zama musu ka'ida har abada. Wanda ya yayyafa ruwan tsarkakewa, sai ya wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa zai zama marar tsarki har maraice. 22 Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa zai ƙazantu, duk wanda kuma ya taɓa abin da marar tsarkin ya taɓa zai ƙazantu har maraice.”

Littafin Ƙidaya 20

Ruwa daga cikin Dutse

1 Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka zo jejin Zin a watan fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Maryamu ta rasu, a nan kuma aka binne ta. 2 Da jama'a suka rasa ruwa, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna. 3 Suka ce wa Musa, “Da ma mun mutu kamar yadda 'yan'uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji. 4 Don me ka fito da taron jama'ar Ubangiji zuwa cikin wannan jeji don mu mutu a nan, mu da dabbobinmu? 5 Don me kuma ka sa muka fito daga masar, ka kawo mu a wannan mugun wuri inda babu hatsi, ko ɓaure, ko inabi, ko rumman, ko ruwan da za a sha ma?” 6 Sai Musa da Haruna suka bar taron jama'a, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada, suka fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana a gare su. 7 Ubangiji ya ce wa Musa, 8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.” 9 Musa kuwa ya ɗauki sanda daga gaban Ubangiji kamar yadda ya umarce shi. 10 Sai Musa da Haruna suka sa jama'a su taru a gaban dutsen, sa'an nan Musa ya ce musu, “Ku kasa kunne, ku 'yan tawaye, za mu fito muku da ruwa daga cikin dutsen nan?” 11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama'a tare da garkunansu suka sha. 12 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da ya ke ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra'ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama'ar nan a ƙasar da na ba su ba.” 13 Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra'ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.

Sarkin Edom ya Hana Isra'ilawa Wucewa

14 Sai Musa ya aika manzanni daga Kadesh zuwa wurin Sarkin Edom, su ce masa, “In ji ɗan'uwanka, Isra'ila, ka dai san dukan wahalar da ta same mu, 15 yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu. 16 Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka. 17 Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.” 18 Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.” 19 Amma mutanen Isra'ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.” 20 Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su. 21 Da haka Edomawa suka hana Isra'ilawa ratsa ƙasarsu. Sai Isra'ilawa suka kauce musu.

Haruna ya Rasu

22-23 Sai taron jama'ar Isra'ila suka kama tafiya daga Kadesh, suka je Dutsen Hor, a kan iyakar ƙasar Edom. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna a can, 24 “Haruna ba zai shiga ƙasar da na alkawarta zan ba Isra'ila ba, zai mutu, gama ku biyun nan kuka tayar wa umarnina a Meriba. 25 Ka kawo Haruna da ɗansa, Ele'azara, bisa Dutsen Hor. 26 Ka tuɓe wa Haruna rigunansa na firist, ka sa wa ɗansa, Ele'azara. Haruna zai mutu can.” 27 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau bisa Dutsen Hor a idon dukan taron jama'a. 28 Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele'azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa'an nan Musa da Ele'azara suka sauko daga kan dutsen. 29 Sa'ad da dukan jama'a suka ga Haruna ya rasu, sai duka suka yi makoki dominsa har kwana talatin.

Littafin Ƙidaya 21

An ci Kan'aniyawa da Yaƙi

1 Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu. 2 Sai Isra'ilawa suka yi wa'adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.” 3 Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.

Macijin da aka Yi da Tagulla

4 Isra'ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama'a suka ƙosa da hanyar. 5 Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.” 6 Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama'a, suka sassari Isra'ilawa, da yawa kuwa suka mutu. 7 Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar. 8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.” 9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.

Tafiya zuwa Kwarin Mowabawa

10 Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya, suka yi zango a Obot. 11 Suka kama hanya daga Obot, suka yi zango a kufafen Abarim a cikin jeji daura da Mowab wajen gabas. 12 Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered. 13 Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda yake cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Gama Arnon shi ne kan iyakar Mowabawa da Amoriyawa. 14 Saboda haka aka faɗa a Littafin Yaƙoƙi na Ubangiji cewa, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na Kogin Arnon, 15 da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.” 16 Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, wato rijiya wadda Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane wuri ɗaya, zan kuwa ba su ruwa.” 17 Sai Isra'ilawa suka raira waƙa, suka ce, “Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwa Mu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta! 18 Rijiyar da hakimai suka haƙa, Shugabannin jama'a suka haƙa, Da sandan sarauta, Da kuma sandunansu.” Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana. 19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot. 20 Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.

Mutanen Isra'ila sun Ci Sihon

21 Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa, 22 “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.” 23 Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa. 24 Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa. 25 Isra'ilawa kuwa suka ci dukan waɗannan birane, suka zauna a biranen Amoriyawa, wato a Heshbon da ƙauyukanta duka. 26 Gama Heshbon ita ce birnin Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon. 27 Domin haka mawaƙa sukan ce, “Ku zo Heshbon, bārin sarki Sihon! Muna so mu ga an sāke gina an kuma fanso shi. 28 Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta, A wannan birni na Heshbon, Sun cinye Ar ta Mowab, Ta murƙushe tuddan Arnon. 29 Kaitonku, ku mutanen Mowab! Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace! Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira, Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su. 30 Amma yanzu an hallaka zuriyarsu, Tun daga Heshbon har zuwa Dibon, Har da Nofa kusa da Medeba.”

Isra'ilawa sun Ci Og

31 Haka fa Isra'ilawa suka zauna a ƙasar Amoriyawa. 32 Sai Musa ya aika a leƙo asirin ƙasar Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawan da suke can. 33 Suka juya suka haura ta hanyar Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa suka fita, suka yi yaƙi da su a Edirai. 34 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama'arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.” 35 Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.

Littafin Ƙidaya 22

Balak ya Sa a Kirawo masa Bal'amu

1 Isra'ilawa suka kama tafiya, suka yi zango a filayen Mowab a hayin Urdun daura da Yariko. 2 Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra'ilawa suka yi wa Amoriyawa. 3 Sai Mowabawa suka firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra'ilawa ya kama su. 4 Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin, 5 ya aiki manzanni zuwa wurin Bal'amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni. 6 Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la'anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu, wanda kuwa ka la'anta, zai la'antu.” 7 Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak. 8 Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal'amu. 9 Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?” 10 Sai Bal'amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini, 11 ‘Ga jama'a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la'anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ” 12 Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.” 13 Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.” 14 Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.” 15 Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā. 16 Suka je wurin Bal'amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina, 17 gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la'anta mini wannan jama'a.’ ” 18 Amma Bal'amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba. 19 Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.” 20 Sal Allah ya je wurin Bal'amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”

Mala'ika da Jakar Bal'amu

21 Da safe sai Bal'amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab. 22 Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala'ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu. 23 Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar. 24 Sai mala'ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi. 25 Sa'ad da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal'amu ga bangon, sai ya sāke bugunta. 26 Mala'ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu. 27 Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa. 28 Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal'amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?” 29 Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.” 30 Sai jakar ta ce wa Bal'amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?” Ya ce, “A'a.” 31 Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal'amu, ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki. 32 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka har sau uku? Na fito ne don inhana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana. 33 Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da ba ta kakuce mini ba, lalle da na kashe ka, in bar ta da rai.” 34 Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.” 35 Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.

Balak ya Marabci Bal'amu

36 Sa'ad da Balak ya ji Bal'amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab. 37 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?” 38 Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.” 39 Sai Bal'amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot. 40 Can ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal'amu da dattawan da suke tare da shi. 41 Kashegari, sai Balak ya ɗauki Bal'amu ya kai shi kan Bamotba'al, daga can ya ga rubu'in mutanen.

Littafin Ƙidaya 23

1 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai guda bakwai a nan, ka kawo mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 2 Balak ya yi yadda Bal'amu ya faɗa masa. Balak da Bal'amu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade. 3 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.

Bal'amu ya sa wa Isra'ila Albarka

4 Da Ubangiji ya sadu da Bal'amu, sai Bal'amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.” 5 Ubangiji kuwa ya sa magana a bakin Bal'amu ya ce, “Koma wurin Balak, ka faɗa masa abin da na faɗa maka.” 6 Sai ya koma wurin Balak, ya same shi da dukan dattawan Mowab suna tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa. 7 Bal'amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce “Tun daga Aram Balak ya kawo ni, Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu. ‘Zo, la'anta mini Yakubu, Zo, ka tsine wa Isra'ila!’ 8 Ƙaƙa zan iya la'anta wanda Allah bai la'antar ba? Ƙaƙa zan iya tsine wa wanda Ubangiji bai tsine wa ba? 9 Gama daga kan duwatsu na gan su, Daga bisa kan tuddai na hange su, Jama'a ce wadda take zaune ita kaɗai, Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al'ummai. 10 Wa zai iya ƙidaya yawan Isra'ilawa da suke kamar ƙura? Yawansu ya fi gaban lasaftawa. Bari ƙarshena ya zama kamar ɗaya daga cikin mutanen Allah, Bari in mutu cikin salama kamar adalai.” 11 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka domin ka la'anta abokan gābana, ga shi, sai albarka kake sa musu!” 12 Bal'amu kuwa ya ce, “Ai, ba tilas ne in hurta abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?” 13 Sai Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su. Waɗanda suka fi kusa kaɗai ne za ka gani, amma ba za ka iya ganinsu duka ba. Ka la'anta mini su daga can.” 14 Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa'an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade. 15 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.” 16 Ubangiji kuwa ya sadu da Bal'amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.” 17 Sai Bal'amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?” 18 Sai Bal'amu ya faɗi jawabinsa, ya ce, “Tashi, Balak, ka ji, Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor. 19 Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika. 20 Ga shi, an umarce ni in sa albarka. Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba. 21 Bai ga mugunta ga Yakubu ba, Bai kuma ga wahala a Isra'ilawa ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su, Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne. 22 Allah ne ya fisshe shi daga Masar, Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna. 23 Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’ 24 Ga shi, jama'ar Isra'ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki, Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa. Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.” 25 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Kada ka la'anta su, kada kuma ka sa musu albarka.” 26 Bal'amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?” 27 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “In ka yarda ka zo in kai ka wani wuri, watakila Allah zai yarda ka la'anta mini su a can.” 28 Balak kuwa ya kai Bal'amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada. 29 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai bakwai, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 30 Balak ya yi yadda Bal'amu ya faɗa masa. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

Littafin Ƙidaya 24

1 Da Bal'amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra'ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji, 2 ya ta da idanunsa ya ga Isra'ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa. 3 Sai ya yi annabcinsa, ya ce. “Faɗar Bal'amu ɗan Beyor, Faɗar mutumin da idonsa ke a buɗe. 4 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah, Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki, Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke. 5 Alfarwan Isra'ilawa suna da kyan gani! 6 Kamar dogon jerin itatuwan dabino, Kamar gonaki a gefen kogi, Kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa, Kamar kuma itatuwan al'ul a gefen ruwaye. 7 Sojojin Isra'ilawa za su sa al'ummai rawar jiki, Za su yi mulkin jama'a mai yawa Sarkinsu zai fi Agag girma, Za a ɗaukaka mulkinsa. 8 Allah ne ya fisshe su dada Masar, Kamar kutunkun ɓauna yake a gare su, Yakubu zai cinye maƙiyansa, Zai kakkarya ƙasusuwansu, ya mummurɗe kibansu. 9 Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”

Annabcin Bal'amu

10 Sai Balak ya husata da Bal'amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal'amu, “Na kirawo ka don ka la'anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka. 11 Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika, na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.” 12 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ashe, ban faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni ba? 13 Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.” 14 Bal'amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.” 15 Sai ya hurta jawabinsa, ya ce, “Faɗar Bal'amu ɗan Beyor, Faɗar mutumin da idonsa ke buɗe, 16 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah, Wanda ya san hikimar Maɗaukaki, Wanda yake ganin wahayin Mai Iko Dukka, Yana durƙurshe, amma idanunsa a buɗe suke. 17 Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka. 18 Za a mallaki Edom, Hakka kuma za a mallaki Seyir abokiyar gābanta, Isra'ila za ta gwada ƙarfi. 19 Yakubu zai yi mulki, Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.” 20 Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce, “Amalek na fari ne cikin al'ummai, amm ƙarshensa hallaka ne.” 21 Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce, “Wurin zamanku mai ƙarƙo ne, Gidajenku kuma suna cikin duwatsu. 22 Duk da haka za a lalatar da Keniyawa. Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?” 23 Sai kuma ya hurta jawabinsa, ya ce, “Kaito, wa zai rayu sa'ad da Allah ya yi wannan? 24 Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim, Za su wahalar da Assuriya da Eber, Su kuma da kansu za su lalace.” 25 Sai Bal'amu ya tashi ya koma garinsu, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

Littafin Ƙidaya 25

Isra'ilawa sun yi Sujada ga Ba'al-feyor

1 Sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa. 2 Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra'ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka. 3 Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa. 4 Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.” 5 Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra'ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba'al-feyor.” 6 Sai ga wani Ba'isra'ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama'ar Isra'ila a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada. 7 Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi. 8 Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa. 9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000 ). 10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 11 “Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra'ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra'ilawa saboda kishina ba. 12 Domin haka ina yi masa alkawarin da ba zai ƙare ba. 13 Alkawarin zai zama nasa da na zuriyarsa, wato alkawarin zama firist din din din, domin ya yi kishi saboda Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin Isra'ilawa.” 14 Sunan Ba'isra'ilen da aka kashe tare da Bamadayaniyar, Zimri ɗan Salu, shi ne shugaban gidan Saminawa. 15 Sunan Bamadayaniya kuwa, Kozbi, 'yar Zur. Shi ne shugaban mutanen gidan ubansa a Madayana. 16 Ubangiji kuma ya umarci Musa, ya ce, 17 “Ku fāɗa wa Madayanawa ku hallaka su. 18 Gama sun dame ku da makircinsu da suka yaudare ku a kan al'amarin Feyor da na Kozbi 'yar'uwarsu, 'yar shugaban Madayana, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor.”

Littafin Ƙidaya 26

Ƙidaya ta Biyu

1 Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele'azara, ɗan Haruna, firist, 2 “Ku ƙidaya dukan taron jama'ar Isra'ila tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba bisa ga gidajen ubanninsu. Ku ƙidaya duk wanda ya isa zuwa yaƙi a cikin Isra'ilawa.” 3 Sai Musa da Ele'azara, firist, suka yi musu magana a filayen Mowab daura da Yariko, suka ce, 4 “A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.” Isra'ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan. 5 Ra'ubainu shi ne ɗan fari na Yakubu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, su ne Hanok, da Fallu, 6 da Hesruna, da Karmi. 7 Waɗannan yawansu ya kai dubu arba'in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730 ). 8 Fallu ya haifi Eliyab. 9 'Ya'yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama'ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji. 10 Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa. 11 Amma 'ya'yan Kora ba su mutu ba. 12 'Ya'yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, 13 da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu. 14 Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200 ). 15 Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, 16 da Ezbon, da Eri, 17 da Arodi, da Areli. 18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500 ). 19 Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana). 20 Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera, 21 da Hesruna, da Hamul. 22 Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500 ). 23 Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa, 24 da Yashub, da Shimron. 25 Waɗannan su ne iyalan kabilar Issaka. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da huɗu da ɗari uku (64,300 ). 26 Kabilar Zabaluna ke nan bisa ga iyalansu, Sered, da Elon, da Yaleyel. 27 Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500 ). 28 Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu. 29 Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad. 30 'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek, 31 da Asriyel, da Shekem, 32 da Shemida, da Hefer. 33 Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 34 Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700 ). 35 Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat. 36 Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne. 37 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500 ). 38 Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram, 39 da Shuffim, da Huffim. 40 Iyalin Adar da na Na'aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne. 41 Waɗannan su ne 'ya'yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari shida (45,600 ). 42 Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan. 43 Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400 ). 44 Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya. 45 Iyalin Beriya kuwa su Eber, da Malkiyel, suna lasafta kansu a zuriyar Beriya. 46 Sunan 'yar Ashiru Sera. 47 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400 ). 48 Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni, 49 da Yezer, da Shallum. 50 Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari huɗu (45,400 ). 51 Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730 ).

An Raba Ƙasa ta Hanyar Kuri'a

52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 53 “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila. 54 Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta. 55 Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a. 56 Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”

Kabilar Lawi

57 Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. 58 Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram, 59 wanda ya auri Yokabed 'yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, 'yar'uwarsu. 60 Haruna yana da 'ya'ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 61 Amma Nadab da Abihu sun mutu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji. 62 Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000 ). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.

Joshuwa da Kalibu kaɗai suka Ragu

63 Waɗannan su ne Isra'ilawa waɗanda Musa da Ele'azara, firist, suka ƙidaya a filayen Mowab wajen Kogin Urdun daura da Yariko. 64 Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra'ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sina'i. 65 Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

Littafin Ƙidaya 27

Roƙon 'Ya'yan Zelofehad Mata

1 Sai 'ya'yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen 'ya'ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 2 Da suka tafi, suka tsaya a gaban Musa da Ele'azara, firist, da gaban shugabanni, da dukan taron jama'a, suka ce, 3 “Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da 'ya'ya maza. 4 Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da 'yan'uwan mahaifinmu.” 5 Musa ya kai maganarsu a gaban Ubangiji. 6 Ubangiji ya ce wa Musa, 7 “Maganar 'ya'yan Zelofehad, mata, daidai ce, saika ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu. Za ka sa gādon mahaifinsu ya zama nasu. 8 Sai kuma ka shaida wa Isra'ilawa, ka ce, ‘Idan mutum ya rasu ba shi da ɗa, sai 'yarsa ta ci gādonsa. 9 Idan kuwa ba shi da 'ya, sai a ba 'yan'uwansa gādonsa. 10 Idan kuma ba shi da 'yan'uwa, sai a ba 'yan'uwan mahaifinsa gādonsa. 11 Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka'ida ga Isra'ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”

An Zaɓi Joshuwa ya Gāji Musa

12 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra'ilawa. 13 Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi, 14 domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.) 15 Musa kuwa ya ce wa Ubangiji, 16 “Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan 'yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama'ar, 17 mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.” 18 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka, 19 ka sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron, sa'an nan ka keɓe shi a gabansu. 20 Ka danƙa masa ikonka don taron jama'ar Isra'ila su yi masa biyayya. 21 Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.” 22 Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron. 23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.

Littafin Ƙidaya 28

Hadaya na Kullum

1 Sai Ubangiji ya umarce Musa, 2 ya dokaci Isra'ilawa su tabbatar cewa sun miƙa wa Allah hadaya ta abinci tare da hadayun da za a yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci bisa ga yadda ake bukata. 3 Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu 'yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani. 4 A miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice, 5 da kuma mudun lallausan gari, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa. 6 Hadaya ce ta ƙonawa kullum, wadda aka kafa a Dutsen Sina'i, don daɗin ƙanshi, hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji. 7 Hadaya ta sha za ta zama rubu'in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade. 8 Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice, tare da hadaya ta gari kamar ta safe, da hadayarsa ta sha. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Hadayu na Ranar Asabar

9 A rana Asabar kuwa za a miƙa 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha. 10 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.

Hadayu na Ɗaya ga Wata

11 A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, 12 hadaya ta gari kuma, a kwaɓa gari humushi uku na garwa da man zaitun don kowane bijimi, da gari humushi biyu na garwa don rago, 13 da kuma gari humushin garwa don ɗan rago. Waɗannan su ne hadayu na abinci na ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 14 Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu'in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara. 15 A kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi ga Ubangiji tare da hadaya ta ƙonawa, da hadayarta ta sha.

Hadayu na Idin Abinci Marar Yisti

16 Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari. 17 Kashegari kuwa za a fara idin kwana bakwai. A kwanakin nan, sai a riƙa cin abinci marar yisti. 18 Za ku yi tsarkakakken taro a ranar fari ta idin, ba za a yi aiki ba. 19 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya ga Ubangiji. Dukansu su zama marasa lahani. 20 Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago, 21 gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago. 22 Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara. 23 Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya. 24 Haka za a miƙa abinci na hadaya ta ƙonawa kowace rana har kwana bakwai, domin daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Za a kuma riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta sha. 25 A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.

Hadayun Idin Girbi

26 Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba. 27 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 28 Za a miƙa hadaya ta gāri tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da mai, gari humushi uku na garwa, za a miƙa tare da kowane bijimi, humushi biyu na garwa don rago, 29 da humushin garwa don kowane ɗan rago. 30 Za a miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi, domin a yi kafara. 31 Banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, sai a miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha. Dabbobin su zama marasa lahani.

Littafin Ƙidaya 29

Hadayu na Idin Watan Bakwai

1 A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni. 2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin za su zama marasa lahani. 3 Tare da dabbobin za a kuma miƙa hadaya ta lallausan gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimin, humushi biyu na garwa kuma tare da ragon. 4 Za a miƙa humushin garwa na gāri tare da kowane ɗan rago. 5 Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara. 6 Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Hadaya a Ranar Kafara

7 Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba. 8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi ɗaya, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani. 9 Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon, 10 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago. 11 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.

Hadayu na Idin Bukkoki

12 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai. 13 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da 'yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani. 14 Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago, 15 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago. 16 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 17 A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani. 18 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 19 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gari, da hadayarsu ta sha. 20 A rana ta uku ta idin za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 21 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 22 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 23 A rana ta huɗu ta idin za a miƙa bijimai goma, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 24 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 25 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 26 A rana ta biyar ta idin za a miƙa bijimai tara, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 27 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 28 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 29 A rana ta shida ta idin za a miƙa bijimai takwas, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 30 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 31 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya taƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 32 A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 33 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 34 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 35 A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba. 36 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani. 37 Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 38 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha. 39 Waɗannan su ne hadayun da za a miƙa wa Ubangiji a lokacin idodinsu, duk da hadayunsu na wa'adi, da na yardar rai, da na ƙonawa, da na gāri, da na sha, da na salama. 40 Musa kuwa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila kome da kome kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

Littafin Ƙidaya 30

Doka a kan Wa'adodin Mata

1 Musa ya kuma ce wa shugabannin kabilan Isra'ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.” 2 Idan mutum ya yi wa'adi ga Ubangiji, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, ko kuwa ba zai yi wani abu ba, to, kada ya warware maganarsa, amma sai ya aikata abin da bakinsa ya hurta. 3 Idan kuma mace ta yi wa'adi ga Ubangiji, ta kuma ɗaure kanta da rantsuwa tun tana yarinya a gidan mahaifinta, 4 idan mahaifinta ya ji wa'adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata. 5 Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa'adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba. 6 Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa'adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje, 7 idan mijinta ya ji wa'adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata. 8 Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta. 9 Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa'adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata. 10 Idan macen aure ta yi wa'adi ko alkawari ba za ta yi wani abu ba, 11 idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata. 12 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa'adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta. 13 Mijinta yana da iko ya tabbatar, ko kuwa ya rushe kowane wa'adi da kowane irin alkawarin da ta ɗauka. 14 Idan mijinta ya yi shiru, bai ce mata kome ba, to, dole ta cika kowane abu da ta yi wa'adi da wanda kuma ta ɗauki alkawarinsa. Shirun da ya yi ya yardar mata. 15 Amma idan ya ji, sa'an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukunci a maimakon matar. 16 Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba Musa a kan wa'adodin matar aure da na wadda ba ta yi aure ba, wato matar da take zaune a gidan mahaifinta.

Littafin Ƙidaya 31

Yaƙin Jihadi da Madayanawa

1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka ɗaukar wa Isra'ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.” 3 Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu. 4 Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila zuwa wurin yaƙi.” 5 Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000 ) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra'ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila. 6 Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele'azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas. 7 Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 8 Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor. 9 Isra'ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima. 10 Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta. 11 Da mutum da dabba sun kwashe su ganima. 12 Suka kawo bayin da ganimar a wurin Musa, da Ele'azara firist, da taron jama'ar Isra'ila a zango a filayen Mowab a Kogin Urdun daura da Yariko.

Sojoji Sun Komo

13 Sai Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar Isra'ila suka fita zango su tarye su. 14 Musa kuwa ya husata da shugabannin sojoji waɗanda ke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga wurin yaƙi. 15 Ya tambaye su ya ce, “Don me kuka bar dukan mata da rai? 16 Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji. 17 Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji. 18 Amma dukan 'yan mata da ba su san maza ba, sai ku bar wa kanku. 19 A cikinku duk wanda ya kashe mutum ko ya taɓa gawa, sai ya zauna a bayan zango kwana bakwai don ya tsarkake kansa tare da bayin a rana ta uku da ta bakwai. 20 Za ku tsarkake kowace riga, da kowane abu da aka yi da fata, da kowane kaya da aka yi da gashin awaki, da kowane abu da aka yi da itace.” 21 Ele'azara firist kuwa, ya ce wa sojojin da suka tafi yaƙi, “Waɗannan su ne ka'idodin da Ubangiji ya ba Musa. 22 Zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma, 23 da dukan abin da wuta ba ta ci ba, su ne za ku tsarkake su da wutar tsarkakewa, duk da haka za a kuma tsarkake shi da ruwa. Amma abin da wuta takan ci, sai a tsarkake shi da ruwa kawai. 24 Ku wanke tufafinku a rana ta bakwai don ku tsarkaka, bayan haka ku shiga zangon.”

Raba Ganima

25 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 26 “Da kai, da Ele'azara firist, da shugabannin gidajen kakannin taron jama'a, ku lasafta yawan mutane, da dabbobin da aka kwaso ganima. 27 Ku kasa ganima kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗayan kuwa ku ba taron jama'ar. 28 Sai ka karɓi na Ubangiji daga cikin kashin ganimar da aka baiwa sojojin da suka tafi yaƙi. Ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakai ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar. 29 Ka ba Ele'azara firist. Wannan hadaya ta ɗagawa ce ga Ubangiji. 30 Daga cikin rabin ganimar da aka ba Isra'ilawa, sai ka ɗauki ɗaya ɗaya daga cikin mutum hamsin, da shanu hamsin, da jakai hamsin, da tumaki hamsin, da dukan dabbobin. Ka ba da su ga Lawiyawa waɗanda suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji.” 31 Musa da Ele'azara firist, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. 32 Yawan ganimar da sojoji suka kawo ke nan, tumaki dubu ɗari shida da dubu saba'in da dubu biyar (675,000 ), 33 shanu dubu saba'in da dubu biyu (72,000 ), 34 jakai dubu sittin da dubu ɗaya (61,000 ), 35 'yan mata dubu talatin da dubu biyu (32,000 ) waɗanda ba su san namiji ba. 36 Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi ne nan, tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari biyar (337,500 ). 37 Daga ciki aka fitar da tumaki ɗari shida da saba'in da biyar domin Ubangiji. 38 Shanu kuma dubu talatin da dubu shida (36,000 ), daga ciki aka fitar da shanu saba'in da biyu domin Ubangiji. 39 Jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500 ), daga ciki aka fitar da jakai sittin da ɗaya domin Ubangiji. 40 'Yan mata dubu goma sha shida (16,000 ), daga ciki aka fitar da 'yan mata talatin da biyu domin Ubangiji. 41 Sai Musa ya ba Ele'azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 42 Wannan shi ne kashin da aka ba jama'ar Isra'ila cikin kashin da aka ware daga na waɗanda suka tafi yaƙin. 43 Tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari bayar (337,500 ), 44 shanu dubu talatin da dubu shida (36,000 ), 45 jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500 ), 46 'yan mata dubu goma sha shida (16,000 ). 47 Daga rabin kashi na jama'ar Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na 'yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 48 Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa. 49 Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da ke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu. 50 Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da 'yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.” 51 Musa da Ele'azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka. 52 Dukan zinariya da shugabanni suka bayar hadaya ga Ubangiji, nauyinta ya kai shekel dubu goma sha shida da ɗari bakwai da hamsin (16,750 ). 53 Kowane soja ya kwashi ganimarsa. 54 Musa da Ele'azara firist kuwa, suka karɓi zinariya da shugabanni suka bayar, suka kai su cikin alfarwa ta sujada don ta zama abin tunawa da jama'ar Isra'ila a gaban Ubangiji.

Littafin Ƙidaya 32

Kabilai a Gabashin Urdun

1 Kabilan Ra'ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu, 2 sai suka je wurin Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar, 3 suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon, 4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama'a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa. 5 Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.” 6 Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai 'yan'uwanku su yi ta yaƙi, ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko? 7 Don me za ku karya zuciyar jama'ar Isra'ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su? 8 Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar. 9 Gama sa'ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama'a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su. 10 Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa'adi ya ce, 11 ‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba. 12 Sai dai Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, da Joshuwa ɗan Nun, domin su ne kaɗai suka bi ni sosai.’ 13 Saboda Ubangiji ya husata da isra'ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba'in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare. 14 Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa. 15 Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.” 16 Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don 'ya'yanmu a nan. 17 'Ya'yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra'ilawa, har mu kai su wuraren zamansu. 18 Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba'isra'ile ya sami gādonsa. 19 Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.” 20 Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji, 21 kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa, 22 har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji. 23 Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku. 24 To, sai ku gina wa 'ya'yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.” 25 Sai Gadawa da Ra'ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta. 26 'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad. 27 Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.” 28 Sai Musa ya yi wa Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra'ila kashedi a kansu, 29 ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra'ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu. 30 Amma idan ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo tare da ku a cikin ƙasar Kan'aniyawa.” 31 Gadawa da Ra'ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi. 32 Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan'aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.” 33 Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkina Amoriyawa, da mulin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu. 34 Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower, 35 da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha, 36 da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi. 37 Ra'ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim, 38 da Nebo, da Ba'al-meyon, da Sibma. 39 Mutanen Makir, ɗan Manassa, suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke cikinta. 40 Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki. 41 Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir. 42 Noba kuma ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya ba ta suna Noba bisa ga sunansa.

Littafin Ƙidaya 33

Tafe-tafe daga Masar zuwa Mowab

1 Waɗannan su ne wuraren da Isra'ilawa suka yi zango sa'ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna. 2 Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan. 3 Sun tashi daga Ramases a rana ta goma sha biyar ga watan fari. A kashegarin Idin Ƙetarewa ne suka fita gabagaɗi a gaban dukan Masarawa. 4 Masarawa suna ta binne gawawwakin 'ya'yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda 'ya'yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu. 5 Isra'ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot. 6 Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin. 7 Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba'al-zefon suka sauka a gaban Migdol. 8 Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara. 9 Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can. 10 Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya. 11 Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin. 12 Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka. 13 Daga Dofka suka tafi Alush. 14 Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha. 15 Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sina'i. 16 Da suka tashi daga jejin Sina'i, sai suka sauka a Kibrot-hata'awa. 17 Suka tashi daga Kibrot-hata'awa suka sauka a Hazerot. 18 Da suka tashi daga Hazerot, sai suka sauka a Ritma. 19 Suka tashi daga Ritma suka sauka a Rimmon-farez. 20 Suka tashi daga Rimmon-farez, suka sauka a Libna. 21 Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa. 22 Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata. 23 Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer. 24 Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada. 25 Da suka tashi daga Harada, suka sauka a Makelot. 26 Suka tashi daga Makelot suka sauka a Tahat. 27 Suka tashi daga Tahat suka sauka a Tara. 28 Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka. 29 Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona. 30 Daga Hashmona suka sauka a Moserot. 31 Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya'akan. 32 Suka tashi daga Bene-ya'akan suka sauka a Hor-hagidgad. 33 Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata. 34 Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona. 35 Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber. 36 Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh. 37 Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom. 38 Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar. 39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa'ad da ya rasu a Dutsen Hor. 40 Sai Sarkin Arad, Bakan'ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan'ana, ya ji zuwan Isra'ilawa. 41 Isra'ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona. 42 Daga Zalamona suka sauka a Funon. 43 Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot. 44 Suka kuma kama hanya daga Obot suka sauka a Abarim a karkarar Mowab. 45 Suka tashi daga nan suka sauka a Dibon-gad. 46 Suka tashi daga Dibon-gad suka sauka a Almon-diblatayim. 47 Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo. 48 Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko. 49 Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.

Umarni kafin su Haye Urdun

50 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce 51 ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana, 52 sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu. 53 Sa'an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta. 54 Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar. 55 Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi. 56 Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”

Littafin Ƙidaya 34

Iyakokin Ƙasar

1 Ubangiji ya ba Musa 2 waɗannan umarnai domin jama'ar Isra'ila. Sa'ad da suka shiga ƙasar Kan'ana ga yadda iyakokin ƙasashensu za su zama. 3 Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas. 4 Sa'an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa'an nan ta miƙa zuwa Hazar'addar, ta zarce ta bi ta Azemon. 5 Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar. 6 Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma. 7 Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor. 8 Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad. 9 Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa. 10 Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam. 11 Sa'an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas. 12 Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita. 13 Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri'a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi. 14 Gama kabilar Ra'ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo. 15 Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”

Shugabannin da za su Rarraba Kasa

16 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 17 “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun. 18 Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar. 19 Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza. 20 Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu. 21 Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu. 22 Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan. 23 Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa, 24 da Kemuwel ɗan Shiftan daga kabilar Ifraimu. 25 Elizafan ɗan Farnak daga kabilar Zabaluna. 26 Faltiyel ɗan Azzan daga kabilar Issaka. 27 Ahihud ɗan Shelomi daga kabilar Ashiru. 28 Fedahel ɗan Ammihud daga kabilar Naftali.” 29 Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba wa jama'ar Isra'ila gādon ƙasar Kan'ana.

Littafin Ƙidaya 35

Biranen Lawiyawa

1 A filayen Mowab a wajen Urdun daura da Yariko, Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce, 2 “Ka umarci jama'ar Isra'ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen. 3 Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu. 4 Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin. 5 A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya. 6 A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida su zama na mafaka, inda za a yarda wa mai kisankai ya gudu zuwa can. Banda biranen mafaka guda shida, za a kuma ba su birane arba'in da biyu. 7 Wato dukan biranen da za a ba Lawiyawa guda arba'in da takwas ne tare da huruminsu. 8 Isra'ilawa za su ba Lawiyawa biranen nan bisa ga girman mallakarsu. Manyan kabilai za su ba su birane da yawa, amma ƙananan kabilai za su ba su birane kaɗan.”

Biranen Mafaka

9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa, 10 ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar Kan'ana, 11 sai ku keɓe wa kanku biranen mafaka domin wanda ya yi kisankai da kuskure, ba da niyya ba, ya gudu zuwa can. 12 Biranen za su zamar muku mafaka daga hannun mai bin hakkin jini, don kada a kashe mai kisankai tun bai riga ya tsaya a gaban shari'a ba. 13 Sai ku zaɓi birane shida. 14 Biranen mafaka uku a hayin gabashin Urdun, birane uku kuma a ƙasar Kan'ana. 15 Waɗannan birane shida za su zama wuraren mafaka ga jama'ar Isra'ila, da baƙi, da baren da yake zaune tare da su, domin duk wanda ya kashe wani ba da niyya ba, ya tsere zuwa can. 16 “Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi. 17 Idan kuwa ya jefe shi da dutsen da ya isa a yi kisankai da shi, har ya mutu, ya yi kisankai ke nan, to, sai a kashe shi. 18 Idan kuwa ya buge shi da makami na itace da ya isa a yi kisankai da shi, har kuwa ya mutu, ya yi kisankai ka nan, sai a kashe shi. 19 Sai mai bin hakkin jinin ya kashe mai kisankan sa'ad da ya iske shi. 20 “Idan saboda ƙiyayya ya laɓe, ya soke shi, ko ya jefe shi har ya mutu, 21 ko kuma saboda ƙiyayya ya naushe shi da hannu har ya mutu, sai a kashe shi, gama ya yi kisankai ke nan. Wanda yake bin hakkin jinin, zai kashe wanda ya yi kisankai sa'ad da ya iske shi. 22 “Amma idan bisa ga tsautsayi ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuwa idan ya jefe shi da kowane abu, ba a laɓe ba, 23 ko ya jefe shi da dutsen da ya isa a kashe mutum da shi, ba da saninsa ba, shi kuwa ba maƙiyinsa ba ne, bai kuwa yi niyya ya cuce shi ba, amma ga shi kuwa, ya kashe shi, 24 to, sai taron jama'a su hukunta tsakanin mai kisankan da mai bin hakkin jinin bisa ga waɗannan ka'idodi. 25 Taron jama'a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu. 26 Amma idan a wani lokaci mai kisankan ya fita kan iyakar birnin mafaka inda yake, 27 idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan iyakar birnin, ya kashe shi, bai yi laifi ba. 28 Gama dole ne mai kisankan ya zauna cikin birnin mafaka inda yake, sai bayan rasuwar babban firist. Bayan rasuwar babban firist, mai kisankan yana iya komawa ƙasarsa.”

Ka'idodin Shaidu da Fansa

29 “Waɗannan ka'idodi sun shafe ku da zuriyarku a duk inda kuke. 30 Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba. 31 Kada ku karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, dole ne a kashe shi. 32 Hakanan kuma kada ku karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don ya koma ya zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba. 33 Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin. 34 Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”

Littafin Ƙidaya 36

Gādon Matan Aure

1 Sai shugabannin gidajen iyalan 'ya'yan Gileyad, ɗan Makir, jikan Manassa, ɗan Yusufu, suka zo suka yi magana da Musa da sauran shugabanni. 2 Suka ce, “Ubangiji ya umarce ka ka raba wa Isra'ilawa gādon ƙasar ta hanyar jefa kuri'a. Ubangiji kuwa ya umarce ka ka ba 'ya'ya mata na Zelofehad, ɗan'uwanmu, gādo. 3 Amma idan suka auri waɗansu daga waɗansu kabilan jama'ar Isra'ila, wato za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura, wato ka ga an ɗebe daga cikin namu gādo ke nan. 4 Sa'ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra'ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.” 5 Musa kuwa ya umarci Isra'ilawa bisa ga faɗar Ubangiji ya ce, “Abin da mutanen kabilar 'ya'yan Yusufu suka faɗa daidai ne. 6 Abin da Ubangiji ya umarta a kan 'ya'ya mata na Zelofehad ke nan, ‘A bar su su auri wanda suka ga dama, amma sai a cikin iyalin kabilar kakansu. 7 Ba za a sāke gādon Isra'ilawa daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowane mutum na cikin jama'ar Isra'ila zai riƙe gādonsa na kabilar kakanninsa. 8 Kowace 'ya mace wadda ta ci gādo a wata kabilar Isra'ila, sai ta yi aure a cikin kabilar kakanta domin kowane Ba'isra'ile ya ci gādon kakanninsa. 9 Ta yin haka ba za a sāke gādo daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowace kabilar Isra'ila za ta riƙe gādonta.’ ” 10 Sai 'ya'yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 11 Suka auri 'ya'yan 'yan'uwan mahaifinsu. 12 Sun yi aure a cikin iyalan 'ya'yan Manassa, ɗan Yusufu. Gādonsu kuwa bai ɓalle daga cikin kabilar iyalin kakansu ba. 13 Waɗannan su ne umarnai da ka'idodi waɗanda Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila ta wurin Musa a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.

Maimaitawar Shari’a 1

Musa ya Jaddada wa Isra'ilawa Alkawarin Ubangiji a Horeb

1 Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab. 2 Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir. 3 A shekara ta arba'in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra'ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu. 4 A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai. 5 A hayin Urdun, cikin ƙasar Mowab, Musa ya yi niyya ya fassara waɗannan dokoki. Ya ce, 6 “Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa. 7 Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan'aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis. 8 Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”

Sa shugabanni

9 “A wancan lokaci ne na yi magana, na ce, ‘Ba zan iya ɗaukar nawayarku ba, 10 gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama. 11 Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku! 12 Ƙaƙa ni kaɗai zan iya ɗaukar nawayarku da wahalarku da kuma faɗace-faɗacenku? 13 Ku zaɓi masu hikima, da masu ganewa daga cikin kabilanku, waɗanda suka saba da zaman jama'a, ni kuwa in sa su zama shugabanninku!’ 14 Kuka amsa mini, kuka ce, ‘I, daidai ne kuwa mu bi shawarar nan da ka kawo mana.’ 15 Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku. 16 “A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari'a tsakanin 'yan'uwanku, tsakanin mutum da ɗan'uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi. 17 Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’ 18 A wancan lokaci na umarce ku da dukan abin da ya kamata ku yi.”

An Aiki 'Yan Leƙen Asirin Ƙasa

19 “Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya. 20 Sa'an nan na faɗa muku cewa, ‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu. 21 Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’ 22 “Sa'an nan sai dukanku kuka zo wurina, kuka ce, ‘Bari mu aika da mutane, su je su leƙo mana asirin ƙasar tukuna, domin su shawarce mu ta hanyar da za mu bi, da kuma irin biranen da za mu shiga.’ 23 “Na ga al'amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila. 24 Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar. 25 Da hannunsu suka ɗebo daga cikin amfanin ƙasar, suka gangaro mana da shi. Suka kuma faɗa mana cewa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu, mai kyau ce. 26 “Amma kuka ƙi ku haura, kuka ƙi bin umarnin Ubangiji Allahnku. 27 Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, ‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu. 28 Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’ 29 “Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita. 30 Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku. 31 Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’ 32 Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba. 33 Shi wanda ya bishe ku, ya nuna muku inda za ku yi zango. Da dare yakan nuna muku hanya da wuta, da rana kuma yakan bi da ku da girgije.”

Hukuncin Allah a kan Isra'ilawa

34 “Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce, 35 ‘Daga cikin mutanen wannan muguwar tsara ba wanda zai ga ƙasan nan mai albarka wadda na rantse zan ba kakanninku, 36 sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da 'ya'yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’ 37 Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba. 38 Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra'ilawa, har su amshi ƙasar, su gāje ta.’ 39 “Sa'an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma 'ya'yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta. 40 Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.’ ”

An Ci Isra'ilawa da Yaƙi a Horma

41 “Sa'an nan kuka amsa mini, kuka ce, ‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.’ Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai. 42 “Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku. 43 Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai. 44 Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma. 45 Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba. 46 Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”

Maimaitawar Shari’a 2

Shekarun da suka Yi a Jeji

1 “Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir. 2 “Sai Ubangiji ya ce mini. 3 ‘Ai, kun daɗe kuna ta gewaya waɗannan tuddai. Ku juya, ku nufi arewa. 4 Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali, 5 kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir. 6 Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu. 7 Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’ 8 “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda sike zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab. 9 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ” 10 (Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā. 11 Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa. 12 Hakanan kuma a dā Horiyawa ne suke zaune a ƙasar Seyir, amma mutanen zuriyar Isuwa suka zo, suka kore su, suka karkashe su, suka zauna a wurin, daidai kamar yadda Isra'ilawa suka yi da ƙasar mallakarsu, wadda Ubangiji ya ba su.) 13 “ ‘Yanzu, ku tashi ku haye rafin Zered da kanku.’ Sai kuwa muka haye. 14 Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu. 15 Hakika kuwa ikon Ubangiji ya buge su har suka hallaka ƙaƙaf. 16 “Sa'ad da dukan waɗanda suka isa yaƙi suka mutu, 17 sai Ubangiji ya yi mini magana, ya ce, 18 ‘Yau za ku ratsa kan iyakar ƙasar Mowab a Ar. 19 Sa'ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.’ ” 20 (Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta. 21 Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu, 22 daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa'ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau. 23 Hakanan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.) 24 “Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi. 25 A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”

Isra'ilawa sun Ci Sihon

26 “Sa'an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce, 27 ‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba. 28 Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku. 29 Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’ 30 “Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau. 31 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa a gare ku. Ku fara fāɗa wa ƙasarsa da yaƙi don ku mallake ta.’ 32 Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza. 33 Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa. 34 Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba. 35 Sai dabbobi ne kaɗai da dukiyar garuruwan da muka ci, su ne muka kwashe ganima. 36 Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu. 37 Amma ba ku kusaci ƙasar Ammonawa ba, wato ƙasar da take a kwarin kogin Yabbok, da garuruwan ƙasar tuddai, da wuraren da Ubangiji Allahnmu ya hana mu.”

Maimaitawar Shari’a 3

Isra'ilawa sun Ci Og na Bashan

1 “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama'arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai. 2 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama'arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’ 3 “Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai. 4 Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan. 5 Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu. 6 Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara. 7 Amma muka riƙe dabbobi da dukiyar da muka kwaso daga garuruwan, ganima. 8 “A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.” 9 (Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.) 10 “Wato dukan garuruwa na ƙasar tudu, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Bashan har zuwa Salka da Edirai, garuruwa na mulkin Og ke nan cikin ƙasar Bashan.” 11 (Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)

Ra'ubainu da Gad, da Rabin Kabilar Manassa sun Zauna a Gabashin Urdun

12 “Sa'ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta. 13 Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.” (Duk dai yankin ƙasar nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.” 14 (Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.) 15 “Na ba Makir Gileyad. 16 Na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar da ta tashi daga Gileyad har zuwa kwarin Arnon, tsakiyar kwarin shi ne iyakar har zuwa kwarin kogin Yabbok wanda ya yi iyaka da Ammonawa. 17 Na kuma ba su Araba, Urdun shi ne iyaka daga Kinneret, har zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas. 18 “A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa. 19 Amma matanku, da 'ya'yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku, 20 har lokacin da Ubangiji ya zaunar da 'yan'uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa'an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’ 21 “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Hakanan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu. 22 Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”

Ba a Yarda wa Musa ya Shiga Kan'ana Ba

23 “Sa'an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce, 24 ‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka. 25 Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasar nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.’ 26 “Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al'amari. 27 Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba. 28 Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’ 29 “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”

Maimaitawar Shari’a 4

Musa ya Gargaɗi Isra'ilawa su yi Biyayya

1 “Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku yake ba ku. 2 Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su. 3 Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba'al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba'al-feyor. 4 Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau. 5 “Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta. 6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al'ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa'ad da al'ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al'umma tana da hikima da ganewa.’ 7 “Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi. 8 Ko kuwa, da akwai wata babbar al'umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”

An Tuna wa Isra'ilawa abin da ya Same su a Horeb

9 “Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su, 10 da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’ 11 “Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa'ad da dutsen yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen. 12 Ubangiji kuwa ya yi magana da ku ta tsakiyar wuta. Kuka ji hurcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji. 13 Shi ne ya hurta muku shari'ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu. 14 Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”

Faɗakarwa a kan Gumaka

15 “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta. 16 Don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji, 17 ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama, 18 ko siffar kowane abu mai jan ciki bisa ƙasa, ko siffar kifin da yake cikin ruwa ƙarƙashin ƙasa. 19 Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai. 20 Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau. 21 Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasar nan wadda yake ba ku abar gādo ba. 22 Gama a nan ƙasar zan mutu, ba zan haye Urdun ba, amma ku za ku haye, ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa. 23 Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku. 24 Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne. 25 “Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi, 26 to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf. 27 Ubangiji zai warwatsa ku cikin al'ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al'ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku. 28 Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana. 29 Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku. 30 Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya. 31 Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba. 32 “Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa? 33 Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu? 34 Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka? 35 An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma. 36 Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar. 37 Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma. 38 Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau. 39 Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma. 40 Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”

Biranen Mafaka a Hayin Gabashin Urdun

41 Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun, 42 domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa. 43 Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.

Gabatarwa a kan Maimaita Dokoki

44 Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra'ilawa, 45 su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar, 46 a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar. 47 Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun. 48 Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon, 49 da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.

Maimaitawar Shari’a 5

Dokoki Goma

1 Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai. 2 Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb. 3 Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau. 4 Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta. 5 Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba. “Ubangiji ya ce, 6 ‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta. 7 “ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni. 8 “ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa. 9 Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni. 10 Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina. 11 “ ‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba. 12 “ ‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. 13 Kwana shida za ka yi aikinka duka. 14 Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka. 15 Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar. 16 “ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka. 17 “ ‘Kada ka yi kisankai. 18 “ ‘Kada ka yi zina. 19 “ ‘Kada ka yi sata. 20 “ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka. 21 “ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’ 22 “Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”

Mutane suka Ji Tsoro

23 “Sa'ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina, 24 suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu. 25 Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu. 26 Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu? 27 Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’ 28 “Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama'ar nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne. 29 Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada. 30 Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu. 31 Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.’ 32 “Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu. 33 Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”

Maimaitawar Shari’a 6

Babban Umarni

1 “Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta, 2 don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai. 3 Don haka, ku ji, ya Isra'ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku. 4 “Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku. 7 Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama. 9 Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”

Faɗakarwa a kan Rashin Biyayya

10 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba, 11 da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, 12 to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 13 Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa. 14 Kada ku bi waɗansu alloli na al'umman da suke kewaye da ku, 15 gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya. 16 “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha. 17 Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su. 18 Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku. 19 Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta. 20 “Idan nan gaba 'ya'yanku suka tambaye ku ma'anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su, 21 sai ku amsa wa 'ya'yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir'auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko. 22 A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu'ujizai gāba da Masarawa, da Fir'auna, da dukan gidansa. 23 Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu. 24 Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau. 25 Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.’ ”

Maimaitawar Shari’a 7

Tsattsarkar Jama'a ta Ubangiji

1 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi. 2 Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai. 3 Kada ku yi aurayya da su. Kada ku aurar wa ɗansu da 'yarku, kada kuma ku auro wa ɗanku 'yarsu. 4 Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri. 5 Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu. 6 Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa. 7 “Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai. 8 Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar. 9 Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa. 10 Amma a fili Ubangiji yakan yi ramuwa a kan maƙiyansa, yakan hallaka su. Ba zai yi jinkirin yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili. 11 Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”

Albarkun Biyayya

12 “Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku. 13 Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa 'ya'yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da 'yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 14 Za ku fi kowace al'umma samun albarka. Ba za a iske mutum ko mace marar haihuwa a cikinku ba, ko a cikin garkenku. 15 Ubangiji zai kiyaye ku daga dukan cuce-cuce. Ba zai wahalshe ku da mugayen cuce-cuce na Masar ba, waɗanda kuka sani, amma zai wahalar da duk maƙiyanku da waɗannan mugayen cuce-cuce. 16 Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko. 17 “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Waɗannan al'ummai sun fi mu yawa, ta ƙaƙa za mu iya ƙorarsu?’ 18 Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir'auna da dukan Masarawa. 19 Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu'ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Hakanan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al'umman nan da kuke jin tsoronsu. 20 Banda wannan kuma Ubangiji Allahnku zai aiko da zirnako a cikinsu su hallaka sauran da suka ragu, suka ɓuya. 21 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana. 22 Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku. 23 Ubangiji Allahnku zai bashe su a gare ku, zai firgitar da su har ya hallakar da su. 24 Zai ba da sarkunansu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Ba wanda zai iya tasar muku har kun ƙare su. 25 Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu. 26 Kada ku kawo abin ƙyama a gidajenku don kada ku zama abin ƙyama kamarsa. Lalle sai ku ƙi shi, ku ji ƙyamarsa, gama haramtacce ne.”

Maimaitawar Shari’a 8

Ƙasar da za ku Mallaka Mai Albarka Ce

1 “Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku. 2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu. 3 Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji. 4 A shekarun nan arba'in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba. 5 Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya. 6 Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa. 7 Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu. 8 Ƙasa mai alkama, da sha'ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma. 9 Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta. 10 Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”

Faɗakarwa kada a Manta da Ubangiji

11 “Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau. 12 Sa'ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki, 13 garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa'ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, 14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta. 15 Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. 16 Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali'u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya. 17 Kada ku ce a zuciya, ‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.’ 18 Sai ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne ya ba ku ikon samun wadata domin ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku kamar yadda yake a yau. 19 Idan kun manta da Ubangiji Allahnku, kuka bi gumaka, kuka bauta musu, kuka yi musu sujada, to, yau ina faɗakar da ku, cewa lalle za ku hallaka 20 kamar al'umman da Ubangiji ya hallakar a gabanku. Haka za ku hallaka domin ba ku kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku ba.”

Maimaitawar Shari’a 9

Ubangiji zai Hallaka Al'umman Ƙasar Kan'ana

1 “Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu. 2 Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?’ 3 Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku. 4 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku. 5 Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 6 Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasar nan don ku mallake ta ba, gama ku jama'a ce mai taurinkai.”

Tayarwar Isra'ilawa a Horeb

7 “Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji. 8 A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku. 9 Sa'ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba'in da yini arba'in ban ci ba, ban sha ba. 10 Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron. 11 Bayan dare arba'in da yini arba'in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, wato alluna na alkawarin. 12 “Sa'an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’ 13 “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘Na ga mutanen nan suna da taurinkai. 14 Bari in hallaka su, in shafe sunansu daga duniya, sa'an nan in maishe ka wata al'umma wadda ta fi su iko da kuma yawa.’ 15 “Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta. 16 Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi. 17 Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku. 18 Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi. 19 Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci. 20 Ubangiji kuma ya husata da Haruna, har ya so ya kashe shi, amma na yi roƙo dominsa a lokacin. 21 Sa'an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen. 22 “Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata'awa. 23 Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba. 24 Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne. 25 “Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku. 26 Na roƙi Ubangiji, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama'arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka. 27 Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama'ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu 28 Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.” 29 Amma su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fito da su da ikonka mai girma da dantsenka mai iko.’

Maimaitawar Shari’a 10

Allunan Dutse na Biyu

1 “A lokacin nan kuwa Ubangiji ya ce mini, ‘Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka hau zuwa wurina a bisa dutsen, ka kuma yi akwati na itace. 2 Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.’ 3 “Sai na yi akwati da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko. Sai na hau dutsen da alluna biyu a hannuna. 4 Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su. 5 Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.” 6 (Isra'ilawa suka kama tafiya daga rijiyoyin Bene-ya'akan suka zo Mosera. Nan ne Haruna ya rasu, aka binne shi. Sai ɗansa Ele'azara, ya gāje shi a matsayinsa na firist. 7 Daga nan suka tafi Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa. 8 A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau. 9 Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.) 10 “Na sāke yin dare arba'in da yini arba'in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu'ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku. 11 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama'ar nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”

Abin da Ubangiji yake So

12 “Yanzu fa, ya Isra'ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku. 13 Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku. 14 Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. 15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al'umma, kamar yadda yake a yau. 16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. 17 Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci. 18 Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari'a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura. 19 Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. 20 Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa. 21 Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al'amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku. 22 Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”

Maimaitawar Shari’a 11

Girman Ubangiji

1 “Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum. 2 Yau fa ku sani ba da 'ya'yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa, 3 da alamunsa, da ayyukan da ya yi a kan Fir'auna Sarkin Masar, da dukan ƙasar, 4 da irin abin da ya yi wa sojojin Masar, da dawakansu, da karusansu, da yadda ya sa ruwan Bahar Maliya ya haɗiye su, a sa'ad da suke bin sawunku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf, 5 da abin da ya yi muku a jeji kafin ku iso wannan wuri, 6 da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, 'ya'yan Eliyab, ɗan Ra'ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra'ilawa ta haɗiye su da dukan 'ya'yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai da yake tare da su. 7 Amma idanunku sun ga manyan ayyukan nan da Ubangiji ya aikata.”

Albarkun Ƙasar Alkawari

8 “Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka, 9 domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da take da yalwar abinci. 10 Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa'an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu. 11 Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita. 12 Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta. 13 “Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku, 14 zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku. 15 Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi. 16 Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada, 17 don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku. 18 “Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku. 19 Za ku koya wa 'ya'yanku su, ku yi ta haddace su, sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 20 Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da bisa ƙofofinku, 21 don kwanakinku da kwanakin 'ya'yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya. 22 “Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa, 23 sa'an nan Ubangiji zai kori al'umman nan duka a gabanku. Za ku kori al'umman da suka fi ku yawa da ƙarfi. 24 Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum. 25 Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku. 26 “Ga shi, yau, na sa albarka da la'ana a gabanku. 27 Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau. 28 Za ku zama la'anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba. 29 Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la'anar kuma a Dutsen Ebal. 30 Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan'aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More. 31 Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa'ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki, 32 sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”

Maimaitawar Shari’a 12

A Wuri ɗaya kaɗai za a Yi Sujada

1 “Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya. 2 Sai ku hallaka dukan wuraren da al'umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu. 3 Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan. 4 “Ba haka za ku yi wa Ubangiji Allahnku ba. 5 Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa. 6 A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. 7 A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi. 8 “Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama. 9 Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna. 10 Amma sa'ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa'ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, 11 sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa. 12 Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku. 13 Ku lura, kada ku miƙa hadayunku na ƙonawa ko'ina, 14 amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku. 15 “Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar tsarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri. 16 Amma ba za ku ci jinin ba, sai ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. 17 Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa. 18 Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi. 19 Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku. 20 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa'an nan ku ce, ‘Ina so in ci nama,’ saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so. 21 Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunsansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku. 22 Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman. 23 Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman. 24 Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa. 25 Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji. 26 Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa. 27 Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman. 28 Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”

Faɗakarwa a kan Gumaka

29 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al'umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa'ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu, 30 to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, ‘Ƙaƙa waɗannan al'ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.’ 31 Kada ku yi wa Ubangiji Allahnku haka, gama sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji yake ƙi, har sun ƙona wa gumakansu 'ya'yansu mata da maza. 32 “Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.

Maimaitawar Shari’a 13

1 “Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza, 2 idan alamar ko mu'ujizar ta auku, idan kuma ya ce, ‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu,’ gumakan da ba ku san su ba, 3 kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku. 4 Sai ku bi Ubangiji Allahnku, ku yi tsoronsa, ku kiyaye umarnansa, ku kasa kunne ga muryarsa, shi ne za ku bauta masa, ku manne masa kuma. 5 Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. 6 “Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’ 7 wato gumakan al'umman da suke kewaye da ku, ko suna kusa da ku, ko suna nesa da ku, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, 8 kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi. 9 Hannunku ne zai fara jifansa, sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi, har ya mutu. 10 Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta. 11 Da hakanan dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba. 12-13 “Idan kuka ji akwai 'yan ashararu a wani gari wanda Ubangiji Allahnku ya ba ku ku zauna a ciki, sun fito daga cikinku, suka rikitar da mazaunan garin suna cewa, ‘Ku zo mu bauta wa gumaka,’ waɗanda ba ku san su ba, 14 to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. Idan hakika gaskiya ne, mugun abu haka ya faru a cikinku, 15 sai ku karkashe dukan mazaunan garin da takobi, ku kuma karkashe dabbobin da suke cikinsa. Za ku hallaka garin ƙaƙaf. 16 Ku tattara dukan ganimar garin a dandali, ku ƙone garin da dukan ganimar, hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji Allahnku. Garin zai zama kufai har abada, ba za a ƙara gina shi ba. 17 Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku, 18 in dai za ku yi wa Ubangiji Allahnku biyayya, ku kiyaye dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, ku kuma ku aikata abin da yake daidai ga Ubangiji Allahnku.”

Maimaitawar Shari’a 14

Al'adar Makokin da aka Hana

1 “Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu. 2 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”

Halattattun Dabbobi da Haramtattu

3 “Kada ku ci abin da yake haram. 4 Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya, 5 da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse. 6 Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa. 7 Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku. 8 Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu. 9 “Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki. 10 Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku. 11 “Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye. 12 Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa, 13 da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa, 14 da kowane irin hankaka, 15 da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho, 16 da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi, 17 da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo, 18 da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura. 19 “Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su. 20 Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne. 21 “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”

Dokar Zakar

22 “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara. 23 Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada. 24 Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa'ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka, 25 to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, 26 ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku. 27 “Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku. 28 A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku. 29 Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”

Maimaitawar Shari’a 15

Shekarar Yafewa

1 “A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi. 2 Ga yadda za ku yafe. Sai kowane mai bin bashi ya yafe wa maƙwabcinsa, kada ya karɓi kome a hannun maƙwabcinsa ko ɗan'uwansa, gama an yi shelar yafewa ta Ubangiji. 3 Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa. 4 “Ba za a sami matalauci a cikinku ba, da yake Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, ku mallaka, 5 muddin kun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye wannan umarni da na umarce ku da shi yau. 6 Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka kamar yadda ya alkawarta. Za ku ba al'ummai da yawa rance, amma ba za ku bukaci rance don kanku ba. Za ku mallaki al'ummai da yawa, amma su ba za su mallake ku ba. 7 “Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci. 8 Amma ku ba shi hannu sake, ku ranta masa abin da yake so gwargwadon bukatarsa. 9 Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. 10 Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi. 11 Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”

Yadda za a Yi da Bayi

12 “Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi. 13 Idan kuma kun 'yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi. 14 Sai ku ba shi hannu sake daga cikin tumakinku, da awakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Ku ba shi kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka. 15 Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya 'yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau. 16 “Amma idan ya ce muku, ‘Ba na so in rabu da ku,’ saboda yana ƙaunarku da iyalinku, tun da yake yana jin daɗin zama tare da ku, 17 to, sai ku ɗauki basilla ku huda kunnensa har ƙyauren ƙofa, zai zama bawanku har abada. Haka kuma za ku yi da baiwarku. 18 Sa'ad da kuka 'yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin dukan abin da kuke yi.”

Keɓewar 'Ya'yan Fari

19 “Sai ku keɓe wa Ubangiji Allahnku dukan 'yan fari maza waɗanda aka haifa muku daga cikin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. Kada ku yi aiki da ɗan farin shanunku, kada kuma ku sausayi ɗan farin tunkiyarku. 20 Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa. 21 Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku. 22 Sai ku ci shi a gida. Mai tsarki da marar tsarki a cikinku za su iya ci, kamar barewa ko mariri. 23 Sai dai kada ku ci jinin, amma ku zubar a ƙasa kamar ruwa.”

Maimaitawar Shari’a 16

Idin Ƙetarewa

1 “Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare. 2 Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa. 3 Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku. 4 Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya. 5 “Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 6 Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar. 7 Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku. 8 Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.

Idin Makonni

9 “Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da yake tsaye. 10 Sa'an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku. 11 Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da yake zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku. 12 Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.

Idin Bukkoki

13 “Za ku yi Idin Bukkoki kwana bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku, da wurin matsewar ruwan inabinku. 14 Sai ku yi murna a cikin idin, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku. 15 Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna. 16 “Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi. 17 Kowane mutum zai kawo irin abin da ya iya, gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa masa.”

Yin Shari'ar Gaskiya

18 “Sai ku naɗa alƙalai da shugabanni domin garuruwanku waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku bisa ga kabilanku. Sai su yi wa jama'a shari'a da adalci. 19 Kada ku ɓata shari'a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali. 20 Adalci ne kaɗai za ku sa gaba domin ku rayu, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 21 “Kada ku dasa kowane irin itace na tsafi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku, wanda za ku gina. 22 Kada kuma ku kafa al'amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”

Maimaitawar Shari’a 17

1 “Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya da sa ko da tunkiya da take da lahani ko naƙasa, gama wannan abar ƙyama ce ga Ubangiji Allahnku. 2 “Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa, 3 har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana, 4 idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra'ilawa, 5 to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba. 7 Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu. 8 “Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa. 9 Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari'a. 10 Sai ku yanke shari'ar yadda suka faɗa muku daga wurin da Ubangiji ya zaɓa. Ku lura fa, ku yi yadda suka faɗa muku. 11 Dole ne ku yi yadda suka koya muku, da yadda suka yanke shari'ar. Kada ku kauce dama ko hagu daga maganar da suka faɗa muku. 12 Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra'ilawa. 13 Sa'an nan duk jama'a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”

Ka'idodin Zaman Sarki

14 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa'an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al'umman da suke kewaye da ku, 15 to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba. 16 Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’ 17 Kada kuma ya auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace. Kada kuma ya tattara wa kansa kuɗi da yawa. 18 Sa'ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci. 19 Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai, 20 don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi 'yan'uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da 'ya'yansa su daɗe, suna mulki a Isra'ila.”

Maimaitawar Shari’a 18

Gādon Firistoci da Lawiyawa

1 “Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra'ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu. 2 Ba za su sami gādo tare da 'yan'uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu. 3 “To, ga rabon da jama'a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin. 4 Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya. 5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da 'ya'yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada. 6 “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra'ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa. 7 Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran 'yan'uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can. 8 Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”

Faɗakarwa a kan Ayyukan Arna

9 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al'ummai. 10 Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa 'yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri, 11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha'ani da matattu. 12 Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al'ummai a gabanku. 13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.

Allah ya yi Alkawari zai Ta da wani Annabi kamar Musa

14 “Gama waɗannan al'ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba. 15 “Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama'arku, sai ku saurare shi. 16 “Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, ‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,’ 17 Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Abin da suka faɗa daidai ne. 18 Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin 'yan'uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi. 19 Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi. 20 Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’ 21 “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Ƙaƙa za mu san maganar da Ubangiji bai faɗa ba?’ 22 Sa'ad da annabi ya yi magana da sunan Ubangiji, idan abin da ya faɗa bai faru ba, bai zama gaskiya ba, to, wannan magana ba Ubangiji ne ya faɗa ba. Wannan annabi ya yi izgili ne kawai, kada ku ji tsoronsa.”

Maimaitawar Shari’a 19

Biranen Mafaka, Iyakoki na Dā

1 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya hallaka al'ummai waɗanda zai ba ku ƙasarsu, sa'ad da kuka kore su, kuka zauna cikin garuruwansu da gidajensu, 2 sai ku keɓe garuruwa uku a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka. 3 Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can. 4 Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā, 5 misali, idan mutum ya tafi jeji, shi da abokinsa don su saro itace. Da ya ɗaga gatari don ya sari itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar, ya sari abokinsa har ya mutu. Irin wannan mai kisankai zai gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen don ya tsira, 6 don kada mai bin hakkin jini ya bi shi da zafin fushinsa, ya cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā. 7 Domin haka na umarce ku, ku keɓe wa kanku garuruwa uku. 8 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta wa kakanninku, har ya ba ku dukan ƙasar da ya alkawarta zai ba kakanninku, 9 in dai kun lura, kun kiyaye umarnin da nake umartarku da shi yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa kullum, sa'an nan sai ku ƙara garuruwa uku a kan waɗannan uku ɗin kuma, 10 don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku. 11 “Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa'an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan, 12 sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa'an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi. 13 Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya. 14 “A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”

Doka a kan Ba da Shaida

15 “Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum. 16 Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani, 17 sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. 18 Sai alƙalan su yi bincike sosai. Idan ɗan sharrin ya ba da shaidar zur a kan ɗaya mutumin, 19 to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. 20 Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba. 21 Kada ku ji tausayi, zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”

Maimaitawar Shari’a 20

Dokoki a kan Yaƙi

1 “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku. 2 Sa'ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist ya zo gaba, ya yi magana da jama'a, 3 ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su. 4 Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.’ 5 “Sa'an nan shugabanni za su yi magana da jama'a, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar. 6 Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani wani dabam ya ci amfaninta. 7 Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.’ 8 “Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.’ 9 Sa'ad da shugabannin yaƙi suka daina yi wa jama'a jawabi, sai a zaɓi jarumawan sojoji don su shugabanci mutane. 10 “Sa'ad da kuka kusaci gari don ku yi yaƙi, sai ku fara neman garin da salama. 11 In ya yarda da salamar, har ya buɗe muku ƙofofinsa, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su bauta muku. 12 Amma idan ya ƙi yin salama da ku, amma ya yi yaƙi da ku, sai ku kewaye shi da yaƙi. 13 Idan Ubangiji Allahnku ya bashe shi a hannunku, sai ku karkashe dukan mazaje da takobi. 14 Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku. 15 Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al'umman da suke kusa da ku ba. 16 “Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo. 17 Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku, 18 don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi. 19 “Sa'ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da suke cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi. 20 Sai dai itatuwan da kuka sani ba su ba da 'ya'ya, su ne za ku sassare, ku yi kagara da su saboda garin da kuke yaƙi da shi har ku ci garin.”

Maimaitawar Shari’a 21

Yadda za a yi da Laifin Kisankai da ba a San wanda ya yi Ba

1 “Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba, 2 sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da suke kewaye da gawar. 3 Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba. 4 Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar. 5 Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci. 6 Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin. 7 Sa'an nan su ce, ‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba. 8 Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’ 9 Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”

Yadda za a yi da Matan da aka Kama wurin Yaƙi

10 “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi, 11 in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha'awarta, to, ka iya aurenta. 12 Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta, 13 ta tuɓe tufafin bauta. Sa'an nan sai ta zauna a gida tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta har wata ɗaya cif. Bayan haka ka iya shiga wurinta, ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka. 14 In ka ji ba ka bukatarta, sai ka sake ta ta tafi inda take so, amma kada ka sayar da ita, kada kuma ka wahalshe ta, tun da yake ka riga ka ƙasƙantar da ita.”

Ka'ida a kan Gādon Ɗan Fari

15 “Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi 'ya'ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari, 16 to, a ranar da zai yi wa 'ya'yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin, 17 Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”

Gagararren Ɗa

18 “Idan mutum yana da gagararren ɗa wanda ba ya jin maganar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa, sun kuma hore shi, duk da haka bai ji ba, 19 sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari. 20 Sai su faɗa wa dattawan garinsu, su ce, ‘Wannan ɗanmu ne, gagararre, ba ya yi mana biyayya. Shi mai zari ne, mashayi!’ 21 Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”

Waɗansu Dokoki

22 “Idan mutum ya yi laifin da ya isa mutuwa, aka rataye shi a itace har ya mutu, 23 kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”

Maimaitawar Shari’a 22

1 “Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi. 2 Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa'an nan ku ba shi. 3 Hakanan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su. 4 “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi. 5 “Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. 6 “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da 'ya'yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa 'ya'yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan. 7 Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe 'ya'yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai. 8 “Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa. 9 “Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku. 10 “Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare. 11 “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin. 12 “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.

Dokoki a kan Hana Lalata

13 “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa'an nan ya ƙi ta, 14 yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa'ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’ 15 sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin. 16 Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum 'yata aure, amma ya ƙi ta. 17 Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske 'yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin 'yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan. 18 Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala, 19 su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra'ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa. 20 “Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba, 21 sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. 22 “Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila. 23 “Idan a cikin gari wani ya iske budurwar da ake tashinta, ya kwana da ita, 24 sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. 25 “Amma idan a saura wani ya fāɗa wa yarinyar da ake tashinta, har ya kwana da ita ƙarfi da yaji, sai a kashe wannan mutum. 26 Amma ita yarinyar ba za a yi mata kome ba, domin ba ta yi laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan shari'a daidai take da ta mutumin da ya faɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi. 27 Gama sa'ad da ya same ta a saura, ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta. 28 “Idan wani ya iske yarinyar da ba a tashinta, ya kama ta, ya kwana da ita, aka kuwa same su, 29 to, sai wanda ya kwana da ita ya ba mahaifinta shekel hamsin na azurfa, ita kuwa za ta zama matarsa, gama ya ci mutuncinta. Ba zai sake ta ba muddin ransa. 30 “Kada mutum ya auri matar mahaifinsa, kada kuma ya kware fatarinta, gama na mahaifinsa ne.”

Maimaitawar Shari’a 23

Waɗanda za a Ware daga cikin Taron Jama'a

1 “Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. 2 “Shege ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba. 3 “Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba, 4 domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku. 5 Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal'amu, sai Ubangiji ya juyar da la'anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku. 6 Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata. 7 “Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa. 8 'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”

Kiyaye Sansanin Yaƙi da Tsabta

9 “Sa'ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu. 10 Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin. 11 Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa'ad da rana ta faɗi. 12 “Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa. 13 Sai ku ɗauki abin tona ƙasa tare da makamanku. Lokacin da za ku zagaya garin yin najasa, sai ku tsuguna ku tona rami da abin tona ƙasa sa'an nan ku rufe najasar da kuka yi. 14 Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”

Waɗansu Dokoki

15 “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa. 16 Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi. 17 “Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini. 18 Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa'adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. 19 “Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa. 20 Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta. 21 “Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba. 22 Idan kun nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba. 23 Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta. 24 “Sa'ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin 'ya'yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku. 25 Sa'ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”

Maimaitawar Shari’a 24

Dokar Kisan Aure

1 “Idan mutum ya sami wata mata ya aura, amma idan ba ta gamshe shi ba saboda ya iske wani abu marar kyau game da ita, har ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, 2 ta kuwa fita gidansa, idan ta je ta auri wani mutum dabam, 3 idan shi kuma ya ƙi ta, ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, ko kuma idan ya mutu ne, 4 to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda. 5 “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”

Waɗansu Dokoki

6 “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne. 7 “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku. 8 “Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su. 9 Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar. 10 “Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina. 11 Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar. 12 Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne. 13 Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku. 14 “Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku. 15 Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku. 16 “Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata. 17 “Kada ku karkatar da shari'ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina. 18 Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan. 19 “Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku. 20 Sa'ad da kuka kakkaɓe 'ya'yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske. 21 Sa'ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske. 22 Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”

Maimaitawar Shari’a 25

1 “Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin, 2 idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi. 3 Za a iya yi masa bulala arba'in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku. 4 “Kada ku yi wa takarkari takunkumi sa'ad da yake tattaka hatsinku.”

Gādon Aure

5 “Idan 'yan'uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan'uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi. 6 Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra'ila. 7 Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’ 8 Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’ 9 sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.’ 10 Za a kira sunan gidansa cikin Isra'ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”

Waɗansu Dokoki

11 “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta, 12 sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi. 13 “Kada ku riƙe ma'aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami. 14 Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami. 15 Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16 Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”

A Karkashe dukan Amalekawa

17 “Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar. 18 Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba. 19 Domin haka sa'ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”

Maimaitawar Shari’a 26

Abin da za a Yi da Nunan Fari da Zaka

1 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta, 2 to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. 3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’ 4 “Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku. 5 Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa. 6 Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu. 7 Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana. 8 Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu'ujizai. 9 Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci. 10 Ga shi, yanzu mun kawo nunan fari na amfanin ƙasar, da kai, ya Ubangiji, ka ba mu.’ “Sai ku ajiye shi a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi sujada a gaban Ubangiji Allahnku. 11 Ku yi murna kuma, ku da Lawiyawa, da baƙin da suke zaune tare da ku, saboda dukan alherin da Ubangiji Allah ya yi muku, ku da gidanku. 12 “Sa'ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku. 13 Sa'an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, ‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba. 14 Ban ci kome daga cikin zakar sa'ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa'ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni. 15 Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama'arka, Isra'ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.’ ”

Tsattsarkar Jama'a ta Ubangiji

16 “Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku. 17 Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya. 18 Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama'arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa. 19 Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”

Maimaitawar Shari’a 27

Za a Rubuta Dokoki a Dutsen Ebal

1 Musa da dattawan Isra'ila suka umarci jama'a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau. 2 Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa. 3 Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku. 4 Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa. 5 Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba. 6 Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. 7 Za ku kuma miƙa hadayu na salama ku ci a wurin, ku yi ta murna a gaban Ubangiji Allahnku. 8 Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.” 9 Sai Musa da Lawiyawan da suke firistoci, suka ce wa Isra'ilawa, “Ku ji. Yau kun zama jama'ar Ubangiji Allahnku. 10 Sai ku saurari muryar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa, da dokokinsa waɗanda muke umartarku da su yau.”

La'ana a kan Dutsen Ebal

11 A wannan rana kuma Musa ya umarci jama'a, ya ce, 12 “Sa'ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama'a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu. 13 Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la'anta, wato kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali. 14 Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa: 15 “ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 16 “ ‘La'ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 17 “ ‘La'ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 18 “ ‘La'ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 19 “ ‘La'ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari'a ta rashin gaskiya.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 20 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 21 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da dabba.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 22 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 23 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 24 “ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 25 “ ‘La'ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ 26 “ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”

Maimaitawar Shari’a 28

Albarkun Biyayya

1 “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma. 2 Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku. 3 “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara. 4 “'Ya'yanku za su zama masu albarka, hakanan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku. 5 “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku. 6 “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita. 7 “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku. 8 “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku. 9 “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa. 10 Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku. 11 Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da 'ya'ya, da 'ya'yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 12 Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba. 13 Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su, 14 idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”

Sakamakon Rashin Biyayya

15 “Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku. 16 “La'anannu za ku zama a gari da karkara. 17 “La'anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku. 18 “La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku. 19 “Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita. 20 “Ubangiji zai aiko muku da la'ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni. 21 Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 22 Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace. 23 Samaniya da yake bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe. 24 Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka. 25 “Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. 26 Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su. 27 Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba. 28 Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali. 29 Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku. 30 “Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin. 31 Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku. 32 A idonku za a ba da 'ya'yanku mata da maza ga wata al'umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome. 33 Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum. 34 Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata. 35 Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku. 36 “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu. 37 Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku. 38 “Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye. 39 Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi. 40 Za ku sami itatuwan zaitun ko'ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama 'ya'yan za su kakkaɓe. 41 Za ku haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta. 42 Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku. 43 “Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya. 44 Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya. 45 “Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba. 46 Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada. 47 Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace, 48 domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku. 49 Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba, 50 al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara. 51 Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku. 52 Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 53 Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi. 54 Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu, 55 domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku. 56 Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta. 57 A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani. 58 “Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafin ba, domin ku ji tsoron sunana nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku, 59 to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa. 60 Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku. 61 Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka. 62 Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba. 63 Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, hakanan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka. 64 “Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba. 65 Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al'ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66 Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku. 67 Da safe za ku ce, ‘Da ma maraice ne.’ Da maraice kuma za ku ce, ‘Da ma safiya ce,’ saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani. 68 Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”

Maimaitawar Shari’a 29

Alkawarin Ubangiji da Isra'ilawa a Ƙasar Mowab

1 Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra'ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb. 2 Sai Musa ya kira dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir'auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar. 3 Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu'ujizai masu girma. 4 Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba. 5 Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba. 6 Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku. 7 Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su. 8 Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda. 9 Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi. 10 “Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila, 11 da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa. 12 Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau. 13 Don ya mai da ku jama'arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 14 Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba, 15 amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu. 16 “Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al'ummai muka wuce. 17 Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya. 18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci. 19 Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anar nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya. 20 Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya. 21 Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra'ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la'anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki. 22 “Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato 'ya'yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata. 23 Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa. 24 Dukan al'ummai za su ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya sa ya yi fushi mai tsanani haka?’ 25 Sa'an nan jama'a za su ce, ‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa'ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar. 26 Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba. 27 Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la'anar da aka rubuta a wannan littafin. 28 Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’ 29 “Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da 'ya'yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.”

Maimaitawar Shari’a 30

Sharuɗan Komar da Mutane, da kuma Sa musu Albarka

1 “Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku, 2 kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau, 3 sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku. 4 Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku. 5 Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku. 6 Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta 'ya'yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu. 7 Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la'ana. 8 Sa'an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau. 9 Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da 'ya'yanku da 'ya'yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku, 10 idan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa da dokokinsa waɗanda suke rubuce a littafin dokokin nan, idan kuma kun juyo wurin Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku. 11 “Gama wannan umarni da na yi muku yau, bai fi ƙarfinku ba, bai kuma yi nisa da ku ba. 12 Ba cikin Sama yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai hau zuwa sama, ya sauko mana da shi don mu ji, mu kiyaye?’ 13 Ba kuma a hayin teku yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai haye mana wannan teku don ya kawo mana shi don mu ji, mu kiyaye?’ 14 Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi. 15 “Ga shi yau, na sa rai da nagarta a gabanku, da mutuwa da mugunta. 16 Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 17 Amma idan zuciyarku ta kangare kun ƙi ku saurara, amma zuciyarku ta janye ku kun yi wa gumaka sujada, kuka bauta musu, 18 to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba. 19 Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la'ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku. 20 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

Maimaitawar Shari’a 31

Joshuwa zai Gāji Musa

1 Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra'ilawa magana. 2 Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’ 3 Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al'ummar da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 4 Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa'ad da ya hallaka su. 5 Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku. 6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.” 7 Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo. 8 Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”

A Karanta Dokokin kowace Shekara ta Bakwai

9 Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra'ila. 10 Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki, 11 sa'ad da dukan Isra'ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu. 12 Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, 13 domin 'ya'yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”

Umarnin Ƙarshe da Ubangiji ya Yi wa Musa

14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada. 15 Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al'amudin girgije. Al'amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar. 16 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su. 17 A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’ 18 Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka. 19 “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙar nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa. 20 Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina. 21 Sa'ad da yawan masifun nan da wahalar nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.” 22 Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama'ar Isra'ila. 23 Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.” 24 Sa'ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin, 25 sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce, 26 “Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku, 27 gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata. 28 Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu. 29 Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”

Waƙar Musa

30 Sa'an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama'ar Isra'ila har ƙarshensu.

Maimaitawar Shari’a 32

1 “Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana, Bari duniya ta ji maganar bakina. 2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, Maganata ta faɗo kamar raɓa, Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa, Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye. 3 Gama zan yi shelar sunan Ubangiji, In yabi girman Allahnmu! 4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma. 5 Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya, 6 Haka za ku sāka wa Ubangiji, Ya ku wawaye, mutane marasa hikima? Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba, Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku? 7 “Ku fa tuna da kwanakin dā, Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki, Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku, Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku, 8 Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu, Sa'ad da ya raba 'yan adam, Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa. 9 Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa, Yakubu shi ne rabon gādonsa. 10 “Ya same shi daga cikin hamada, A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya kewaye shi, ya lura da shi, Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa. 11 Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta, Tana rufe da 'yan tsakinta, Ta buɗe fikafikanta, ta kama su, Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta. 12 Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi, Ba wani baƙon allah tare da shi. 13 “Ya sa shi ya hau kan tuddai, Ya ci amfanin ƙasa, Ya sa shi ya sha zuma daga dutse, Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara. 14 Ya sami kindirmo daga shanu, Da madara daga garken tumaki da na awaki, Da kitse daga 'yan raguna, da raguna, Da bijimai, da bunsurai daga Bashan, Da alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau. 15 “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska, Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul. Ya rabu da Allahn da ya yi shi, Ya raina Dutsen Cetonsa. 16 Suka sa shi kishi, saboda gumaka, Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama. 17 Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba, Ga gumakan da ba su sani ba, Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya, Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba. 18 Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku, Kun manta da Allahn da ya ba ku rai. 19 “Ubangiji ya gani, ya raina su, Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa. 20 Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci. 21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma. 22 Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu. 23 “ ‘Zan tula musu masifu, Zan ƙare kibauna a kansu, 24 Za su lalace saboda yunwa, Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su. Zan aika da haƙoran namomi a kansu, Da dafin abubuwa masu jan ciki. 25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, A cikin ɗakuna kuma tsoro, Zai hallaka saurayi da budurwa, Da mai shan mama da mai furfura. 26 Na ce, “Zan watsar da su, In sa a manta da su cikin mutane.” 27 Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi, Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara. Ai, ni ne na yi wannan.’ 28 “Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara, Ba su da ganewa. 29 Da suna da hikima, da sun gane wannan, Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama! 30 Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su? 31 Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, Ko abokan gabanmu ma sun san haka. 32 Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma ne Da gonakin Gwamrata. 'Ya'yan inabinsu dafi ne, Nonnansu masu ɗaci ne. 33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne. Da mugun dafin kumurci. 34 “Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba, A ƙulle kuma a taskokina? 35 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne, A lokacin ƙafarsu za ta zame, Gama ranar masifarsu ta kusa, Hallakarsu za ta zo da sauri. 36 Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa, Zai ji ƙan bayinsa, Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa, Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa. 37 Sa'an nan zai ce, ‘Ina gumakansu, Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi, 38 Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu, Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha? Bari su tashi su taimake ku, Bari su zama mafaka! 39 “ ‘Ku duba fa, ni ne shi, Ba wani Allah, banda ni, Nakan kashe, in rayar, Nakan sa rauni, nakan kuma warkar, Ba wanda zai cece su daga hannuna. 40 Na ɗaga hannuna sama, Na rantse da madawwamin raina, 41 Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya, Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci, Zan ɗauki fansa a kan magabtana Zan sāka wa maƙiyana. 42 Zan sa kibauna su bugu da jini, Takobina zai ci nama, Da jinin kisassu da na kamammu, Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’ 43 “Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”

Gargaɗin Musa na Ƙarshe

44 Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a. 45 Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila, 46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai. 47 Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”

An Yarda wa Musa ya Hangi Ƙasar Kan'ana

48 A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa, 49 “Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan'ana wadda zan ba Isra'ilawa su mallaka. 50 Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya. 51 Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba. 52 Za ka ga ƙasar da nake ba jama'ar Isra'ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”

Maimaitawar Shari’a 33

Musa ya Sa wa Kabilan Isra'ila Albarka

1 Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu. 2 Ya ce, “Ubangiji ya taho daga Sina'i, Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka, Ya taho tare da dubban tsarkakansa, Da harshen wuta a damansa. 3 Hakika, yana ƙaunar jama'arsa, Dukan tsarkaka suna a ikonka, Suna biye da kai, Suna karɓar umarninka. 4 Musa ya ba mu dokoki, Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu. 5 Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun, Sa'ad da shugabanni suka taru, Dukan kabilan Isra'ila suka taru. 6 “Allah ya sa Ra'ubainu ya rayu, kada ya mutu, Kada mutanensa su zama kaɗan.” 7 A kan Yahuza ya ce, “Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji, Ka kawo shi wurin jama'arsa. Ka yi yaƙi da ikonka dominsu, Ka taimake shi a kan maƙiyansa.” 8 A kan Lawi ya ce, “Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka, Shi wanda ka jarraba a Masaha, Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba, 9 Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, ‘Ban kula da ku ba.’ Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne. Ya kuma ƙyale 'ya'yansa, Domin sun kiyaye maganarka, Sun riƙe alkawarinka. 10 Suna koya wa Yakubu farillanka, Suna koya wa Isra'ila dokokinka. Suna ƙona turare a gabanka, Suna ƙona hadaya ta ƙonawa a bagadenka. 11 Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu, Ka karɓi aikin hannuwansu, Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu, Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.” 12 A kan Biliyaminu, ya ce, “Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne, Yana zaune lafiya kusa da shi, Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini, Yana zaune a kan kafaɗunsa.” 13 A kan Yusufu, ya ce, “Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka, Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa, Da ruwan da yake a ƙasa, 14 Da kyawawan kyautan da rana yake bayarwa, Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa, 15 Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā, Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai. 16 Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, Da alherin wanda yake zaune a jeji. Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu, A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa. 17 Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take, Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke, Da su yake tunkwiyin mutane, Zai tura su zuwa ƙurewar duniya, Haka fa rundunan Ifraimu za su zama, Haka kuma dubban Manassa za su zama.” 18 A kan Zabaluna ya ce, “Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna, Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka. 19 Za su kira mutane zuwa dutse, Can za su miƙa hadayu masu dacewa, Gama za su ɗebo wadatar tekuna, Da ɓoyayyun dukiyar yashi.” 20 A kan Gad, ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad, Gad yana sanɗa kamar zaki, Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai. 21 Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau, Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba. Ya zo wurin shugabannin mutane, Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji, Ya kiyaye farillansa.” 22 A kan Dan, ya ce, “Dan ɗan zaki ne, Mai tsalle daga Bashan.” 23 A kan Naftali, ya ce, “Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri, Cike kake da albarkar Ubangiji. Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.” 24 A kan Ashiru, ya ce, “Ashiru mai albarka ne fiye da sauran 'yan'uwansa, Bari ya zama abin ƙauna ga 'yan'uwansa, Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai. 25 Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla, Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.” 26 “Babu wani kamar Allahn Yeshurun, Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka, Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa. 27 Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka, Madawwaman damatsansa suna tallafarka, Yana kore maka maƙiyanka, Ya ce, ‘Ka hallaka su!’ 28 Da haka Isra'ila yana zaune lafiya, Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗai A ƙasa mai hatsi da ruwan inabi, Wurin da raɓa yake zubowa daga sama. 29 Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”

Maimaitawar Shari’a 34

Rasuwar Musa

1 Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan, 2 da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum, 3 da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar. 4 Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.” 5 Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 6 Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau. 7 Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba. 8 Isra'ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa'an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare. 9 Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa. 10 Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska. 11 Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa. 12 Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.

Joshuwa 1

Shirin da aka Yi don Cin Ƙasar Kan'ana

1 Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki, 2 “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'ar nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa. 3 Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa. 4 Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku. 5 Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba. 6 Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu. 7 Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da hakanan za ka arzuta cikin dukan harkokinka. 8 Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara. 9 Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.” 10 Sai Joshuwa ya umarci shugabannin jama'a, ya ce, 11 “Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ” 12 Joshuwa kuma ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, 13 “Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.’ 14 Da matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da 'yan'uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su, 15 har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.” 16 Su kuwa suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Iyakar abin da ka umarce mu za mu yi, duk inda ka aike mu kuma za mu tafi. 17 Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya a kowane abu hakanan za mu yi maka biyayya, Ubangiji Allahnka dai ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance tare da Musa. 18 Duk wanda ya ƙi bin umarninka, bai kuwa yi biyayya da maganarka da dukan irin abin da ka umarce shi ba, za a kashe shi. Kai dai ka dāge, ka yi ƙarfin hali.”

Joshuwa 2

Joshuwa ya Aiki 'Yan Leken Asirin Ƙasa zuwa Yariko

1 Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka. 2 Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da dad dare domin su bincike ƙasar.” 3 Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.” 4 Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba, 5 da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.” 6 Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin. 7 Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin. 8 Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin, 9 ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku. 10 Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa'ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai. 11 Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa. 12 Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama. 13 Ku ceci mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan'uwana mata da maza, da dukan abin da yake nasu, ku ceci rayukanmu daga mutuwa.” 14 Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.” 15 Sa'an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne. 16 Sai ta ce musu, “Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa'an nan ku kama hanyarku.” 17 Mutanen suka ce mata, “Za mu kuɓuta daga rantsuwarki wadda kika rantsar da mu. 18 A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki. 19 Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu. 20 Amma idan kika tone al'amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu.” 21 Sai ta ce, “Bisa ga maganarku ya zama haka.” Sa'an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar. 22 Sai suka tafi, suka shiga tsaunuka, suka yi zamansu a can kwana uku har masu bin sawun suka koma, gama masu bin sawun suka yi ta nema ko'ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba. 23 Mutanen nan biyu suka sauko daga tsaunuka, suka haye zuwa wurin Joshuwa ɗan Nun, suka faɗa masa dukan abin da ya same su. 24 Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”

Joshuwa 3

Isra'ilawa sun Haye Urdun

1 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye. 2 Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango, 3 suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi, 4 domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.” 5 Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.” 6 Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a. 7 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai. 8 Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ” 9 Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.” 10 Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku. 11 Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun. 12 Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila. 13 A sa'ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.” 14-15 (Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe, 16 sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko. 17 A sa'ad da Isra'ilawa duka suke tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.

Joshuwa 4

Duwatsu Goma Sha Biyu da aka Ɗauka Tsakiyar Urdun

1 Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, 2 “Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila. 3 Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.” 4 Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila. 5 Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila. 6 Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?’ 7 Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.” 8 Sai Isra'ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su. 9 Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau. 10 Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi. Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye. 11 Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar. 12 Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su. 13 Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000 ), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko. 14 A ranar nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa. 15 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, 16 “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.” 17 Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun. 18 Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā. 19 Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko. 20 Joshuwa ya kafa duwatsun nan goma sha biyu da suka ɗauko daga Urdun a Gilgal. 21 Sai ya ce wa Isra'ilawa, “Sa'ad da wata rana 'ya'yanku suka tambayi ubanninsu ma'anar duwatsun nan, 22 sa'an nan za ku sanar da 'ya'yanku cewa Isra'ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa! 23 Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye, 24 domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”

Joshuwa 5

Yin Kaciya da Kiyaye Idin Ƙetarewa a Gilgal

1 Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa. 2 A lokacin kuwa Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu, ka yi wa mazajen Isra'ila kaciya.” 3 Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha'aralot, wato dutsen kaciya. da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu. 6 Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da yake mai yalwar abinci. 7 'Ya'yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba. 8 Da aka gama yi wa al'ummar duka kaciya, sai suka zauna a zango har suka warke. 9 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar. 10 Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko. 11 A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba. 12 Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra'ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan'ana.

Joshuwa da Mutumin da yake Riƙe da Takobi

13 Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?” 14 Sai mutumin ya ce, “A'a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji.” Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, “Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?” 15 Sarkin yaƙin rundunar Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Cire takalmanka da suke a ƙafafunka, gama wurin da kake tsaye tsattsarka ne.” Haka kuwa Joshuwa ya yi.

Joshuwa 6

Faɗuwar Yariko

1 Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa. 2 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka. 3 Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida. 4 Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni. 5 Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.” 6 Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, “Ɗauki akwatin alkawarin, sa'an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji.” 7 Ya kuma ce wa jama'a, “Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji.” 8 Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su. 9 Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni. 10 Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu.” 11 Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana. 12 Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji. 13 Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, 'yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni. 14 A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa'an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida. 15 A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai. 16 A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin. 17 Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwar nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika. 18 Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa. 19 Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji.” 20 Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin. 21 Sa'an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai. 22 Sa'an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, “Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata.” 23 Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa. 24 Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji. 25 Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra'ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko. 26 A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce, “La'ananne ne mutum a gaban Ubangiji Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko. A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa, A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.” 27 Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.

Joshuwa 7

Zunubin Akan

1 Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa. 2 Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai. 3 Da suka komo wurin Joshuwa, sai suka ce masa, “Kada dukan mutane su tafi, amma a bar mutum wajen dubu biyu ko uku su tafi su bugi Ai, kada a sa dukan mutane su sha wahalar zuwa can, domin su kima ne.” 4 Sai mutum wajen dubu uku daga cikin jama'a suka tafi, amma mutanen Ai suka kore su. 5 Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra'ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra'ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa. 6 Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu. 7 Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'ar nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun. 8 Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra'ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu? 9 Gama Kan'aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?” 10 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki? 11 Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya. 12 Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku. 13 Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku. 14 Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum. 15 Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ” 16 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza. 17 Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi. 18 Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza. 19 Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.” 20 Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra'ila zunubi. Ga abin da na yi. 21 A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.” 22 Joshuwa ya aika da manzanni, suka sheƙa a guje zuwa alfarwar, suka tarar da abubuwan a binne cikin alfarwarsa da azurfa a ƙarƙashi. 23 Sai suka kwaso suka kawo wa Joshuwa da dukan Isra'ilawa, suka ajiye su a gaban Ubangiji. 24 Joshuwa kuwa tare da dukan Isra'ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da 'ya'yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor. 25 Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta. 26 Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.

Joshuwa 8

An Ci Ai da Yaƙi

1 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka. 2 Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.” 3 Joshuwa kuwa tare da dukan mayaƙa suka yi shirin tashi zuwa Ai. Sai Joshuwa ya zaɓi jarumawa ƙarfafa dubu talatin (30,000 ), ya aike su da dad dare. 4 Ya umarce su, ya ce, “Ku tafi, ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birni da yawa, amma dukanku ku kasance da shiri sosai. 5 Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa'ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su. 6 Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudunmu kamar dā.’ Haka fa, za mu gudu daga gare su. 7 Ku kuwa ku tashi daga kwanto, ku ci birnin, gama Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku. 8 A sa'ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.” 9 Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama'a. 10 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra'ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai. 11 Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari. 12 Ya kuma zaɓi mutum wajen dubu biyar (5,000 ) ya sa su yi kwanto tsakanin Betel da Ai, yamma da birnin. 13 Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na 'yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin. 14 A sa'ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra'ilawa, amma bai san akwai 'yan kwanto a bayan birnin ba. 15 Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji. 16 Saboda haka aka kira dukan mutanen da suke cikin birnin, su fafare su. Da suka fafari Joshuwa, sai aka janye su nesa da birnin. 17 Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra'ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra'ilawa. 18 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa 19 'yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta. 20 Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu. 21 Sa'ad da Joshuwa da dukan Isra'ilawa suka ga 'yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su. 22 Sauran Isra'ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra'ilawa gaba da baya. Isra'ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere. 23 Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa. 24 Sa'ad da Isra'ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra'ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta. 25 A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000 ). 26 Joshuwa bai janye hannunsa da riƙon mashin ba, sai da ya hallaka mazaunan Ai sarai. 27 Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra'ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa. 28 Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau. 29 Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa'ad da rana yake faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.

An Karanta Albarka da La'ana a Dutsen Ebal

30 Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal. 31 Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra'ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama. 32 A nan, a idon Isra'ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun. 33 Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka. 34 Bayan haka ya karanta dukan zantuttukan shari'a, da na albarka da na la'ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura. 35 Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.

Joshuwa 9

Munafuncin Gibeyonawa

1 Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari, 2 sai suka tattaru, suka haɗa kansu domin su yaƙi Joshuwa da Isra'ilawa. 3 Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai, 4 sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki. 5 Suka kuma sa tsofaffin takalma waɗanda suka sha gyara, da tsofaffin tufafi. Dukan guzurinsu ya bushe, ya yi fumfuna. 6 Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.” 7 Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?” 8 Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.” Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?” 9 Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar, 10 da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot. 11 Dattawanmu da dukan mazaunan ƙasarmu suka ce mana mu ɗauki guzuri a hannunmu don tafiya, mu tafi taryarku, mu ce muku, ‘Mu bayinku ne, yanzu dai sai ku yi mana alkawari.’ 12 Wannan abinci, da ɗuminsa muka ɗauko shi daga gidajenmu a ranar da muka fito zuwa gare ku, amma ga shi, yanzu ya bushe ya yi fumfuna. 13 Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!” 14 Sai Isra'ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba. 15 Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu. 16 Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maƙwabtansu ne, suna zaune a cikinsu. 17 Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim. 18 Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin. 19 Amma shugabanni suka ce wa dukan jama'a, “Mun riga mun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, don haka yanzu ba shi yiwuwa mu taɓa su. 20 Abin da za mu yi musu ke nan, a bar su da rai saboda rantsuwar da muka rantse musu don kada mu jawo wa kanmu fushin Ubangiji!” 21 Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.” 22 Joshuwa kuwa ya kirawo su, ya ce musu, “Me ya sa kuka ruɗe mu da cewa, ‘Muna nesa da ku ƙwarai,’ ga shi kuwa, a tsakiyarmu kuke zaune? 23 Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.” 24 Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka. 25 Yanzu dai muna a hannunka, ka yi yadda ka ga ya yi maka kyau.” 26 Haka kuwa ya yi musu, ya cece su daga hannun Isra'ilawa, har ba su kashe su ba. 27 Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

Joshuwa 10

An Ci Amoriyawa da Yaƙi

1 Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra'ilawa, har suna zama cikinsu. 2 Sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne. 3 Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce, 4 “Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra'ilawa.” 5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta. 6 Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.” 7 Sai Joshuwa ya tashi daga Gilgal da dukan mayaƙa, da dukan jarumawa tare da shi. 8 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.” 9 Sai Joshuwa ya tafi ya auka musu ba labari, gama daga Gilgal ya bi dare zuwa can. 10 Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Ber-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda. 11 Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi. 12 Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.” 13 Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, Har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu. Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda. 14 Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa. 15 Sa'an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra'ilawa. 16 Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda. 17 Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.” 18 Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa'an nan ku sa mutane su yi tsaronsu. 19 Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a Hannunku.” 20 Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu. 21 Sa'an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra'ilawa. 22 Sa'an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.” 23 Suka yi hakanan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon. 24 Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu. 25 Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.” 26 Sa'an nan Joshuwa ya buga su, ya kashe su, ya kuma rataye kowane ɗayansu a bisa itace. Suka yini a rataye har maraice. 27 Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa'an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan. 28 A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da Yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko. 29 Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra'ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna. 30 Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko. 31 Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra'ilawa duka, zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata. 32 Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra'ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna. 33 Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu. 34 Joshuwa kuma ya zarce tare da dukan Isra'ilawa daga Lakish zuwa Eglon, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata. 35 A ran nan suka cinye ta, suka buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi. Ya hallakar da su a wannan rana kamar yadda ya yi wa Lakish. 36 Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra'ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata. 37 Suka cinye ta, suka buge ta, da sarkinta, da garuruwanta, da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta. 38 Sai Joshuwa ya juya tare da dukan Isra'ilawa zuwa Debir, ya auka mata. 39 Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta. 40 Hakanan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta. 41 Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon. 42 Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi yaƙi domin Isra'ilawa. 43 Sa'an nan Joshuwa ya komo tare da dukan Isra'ilawa zuwa zango a Gilgal.

Joshuwa 11

An Ci Yabin da Magoya Bayansa

1 Sa'ad da Yabin Sarkin Hazor ya ji labari, ya aika wa Yobab, Sarkin Madon, da Sarkin Shimron, da Sarkin Akshaf, 2 da sarakunan da suke arewacin ƙasar tuddai, da cikin Araba a kudancin Kinneret, da cikin filayen kwari, da cikin Dor a yamma. 3 Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa. 4 Sai suka fita tare da dukan mayaƙansu, babbar runduna mai yawa kamar yashi a bakin teku, da dawakai, da karusai da yawa ƙwarai. 5 Da sarakunan nan duka suka haɗa ƙarfinsu, sai suka je suka kafa sansaninsu a wuri ɗaya a bakin ruwayen Merom domin su yi yaƙi da Isra'ilawa. 6 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.” 7 Sai Joshuwa, tare da dukan mayaƙansa, suka je suka mame su, suka auka musu a bakin ruwayen Merom. 8 Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf. 9 Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu. 10 A wannan lokaci Joshuwa ya koma da baya ya ci Hazor, ya kashe sarkinta da takobi, gama a lokacin Hazor ita ce masarautar mulkokin nan. 11 Suka kashe dukan waɗanda suke cikinta da takobi, suka hallakar da su ƙaƙaf, ba wanda ya ragu. Joshuwa kuwa ya ƙone Hazor. 12 Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta. 13 Amma mutanen Isra'ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da suke bisa tuddai ba, sai Hazor kaɗai Joshuwa ya ƙone. 14 Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba. 15 Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

Joshuwa ya Cinye Ƙasar Duka

16 Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasar nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra'ila da filayen kwarinta, 17 tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba'al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su. 18 Joshuwa ya daɗe yana yaƙi da su. 19 Ba wani birnin da ya yi amana da Isra'ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi. 20 Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 21 A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra'ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu. 22 Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu. 23 Hakanan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.

Joshuwa 12

Sarakunan da Musa ya Ci da Yaƙi

1 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas, 2 Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa, 3 daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga, 4 da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai. 5 Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon. 6 Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.

Sarakunan da Joshuwa ya Ci da Yaƙi

7 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu, 8 da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 9 Sunayen sarakunan su ne, Sarkin Yariko, da Sarkin Ai, da yake kusa da Betel, 10 da Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, 11 da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, 12 da Sarkin Eglon, da Sarkin Gezer, 13 da Sarkin Debir, da Sarkin Geder, 14 da Sarkin Horma, da Sarkin Arad, 15 da Sarkin Libna, da Sarkin Adullam, 16 da Sarkin Makkeda, da Sarkin Betel, 17 da Sarkin Taffuwa, da Sarkin Hefer, 18 da Sarkin Afek, da Sarkin Lasharon, 19 da Sarkin Madon, da Sarkin Hazor, 20 da Sarkin Shimron-meron, da Sarkin Akshaf, 21 da Sarkin Ta'anak, da Sarkin Magiddo, 22 da Sarkin Kedesh, da Sarkin Yakneyam a Karmel, 23 da Sarkin Dor a bakin teku, da Sarkin Goyim na Gilgal, 24 da Sarkin Tirza. Sarakuna talatin da ɗaya ke nan.

Joshuwa 13

Ƙasar da ta Ragu da za a Mallaka

1 Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa. 2 Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa, 3 daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai sarakuna biyar na Filistiyawa da suke a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa, 4 da dukan ƙasar Kan'aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa, 5 da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat, 6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka. 7 Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”

Yankin Ƙasar da aka ba Manassa da Ra'ubainu da Gad

8 Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan, 9 daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon, 10 da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa, 11 da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka, 12 da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su. 13 Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau. 14 Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa. 15 Musa ya riga ya ba Ra'ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu. 16 Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba, 17 da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon, 18 da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat, 19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin, 20 da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot. 21 Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar. 22 Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi. 23 Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama'ar Ra'ubainu. Wannan shi ne gādon Ra'ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu. 24 Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu. 25 Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba, 26 daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir, 27 da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun. 28 Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu. 29 Musa kuma ya ba rabin jama'ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu. 30 Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan, 31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu. 32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun daura da Yariko. 33 Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra'ila, shi ne rabon gādonsu.

Joshuwa 14

An Rarraba Ƙasar kan'ana ta Hanyar Kuri'a

1 Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra'ilawa suka karɓa a ƙasar Kan'ana, wanda Ele'azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra'ila suka ba su. 2 Kabilar nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri'a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 3 Gama Musa ya riga ya ba kabilar nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba. 4 Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu. 5 Jama'ar Isra'ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri'a.

An Ba Kalibu Hebron

6 Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina. 7 Ina da shekara arba'in sa'ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata. 8 Amma 'yan'uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama'ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci. 9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana ya ce, ‘Hakika duk inda ƙafafunka suka taka a ƙasar nan zai zama gādonka, kai da 'ya'yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahnka sosai!’ 10 Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba'in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne. 11 Ga shi kuwa, har wa yau ina da ƙarfi kamar ran da Musa ya aike ni. Kamar yadda ƙarfina yake a dā, haka yake a yanzu domin yaƙi, da kuma kai da kawowa. 12 Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranar nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.” 13 Joshuwa ya sa wa Kalibu, ɗan Yefunne, albarka. Ya ba shi Hebron ta zama gādonsa. 14 Domin haka Hebron ta zama gādon Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, har wa yau, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila sosai. 15 A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.

Joshuwa 15

Yankin Ƙasar da aka Ba Yahuza

1 Rabon da aka ba jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa. 2 Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu. 3 Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka. 4 Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu. 5 Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun. 6 Iyakar ta bi zuwa Ber-hogla, ta zarce zuwa arewa da Bet-araba, ta haura zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 7 Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel. 8 Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa. 9 Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim. 10 Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna. 11 Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku. 12 Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.

Kalibu ya Ci Hebron da Debir da Yaƙi

13 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyatarba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak. 14 Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak. 15 Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne. 16 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.” 17 Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure. 18 Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?” 19 Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.

Biranen Kabilar Yahuza

20 Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu. 21 Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur, 22 da Kina, da Dimona, da Adada, 23 da Kedesh, da Hazor, da Yitnan, 24 da Zif, da Telem, da Beyalot, 25 da Hazor-hadatta, da Kiriyot-hesruna, wato Hazor, 26 da Amam, da Shema, da Molada, 27 da Hazar-gadda, da Heshmon, da Bet-felet, 28 da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba, da Biziyotaya, 29 da Ba'ala, da Abarim, da Ezem, 30 da Eltola, da Kesil, da Horma, 31 da Ziklag, da Madmanna, da Sansanna, 32 da Labayot, da Shilhim, da Ayin, da Rimmon. Birane ashirin da tara ke nan da ƙauyukansu. 33 Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna, 34 da Zanowa, da En-ganim, da Taffuwa, da Enayim, 35 da Yarmut, da Adullam, da Soko, da Azeka, 36 da Shayarim, da Aditayim, da Gedera, da Gederotayim. Birane goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. 37 Da kuma Zenan, da Hadasha, da Migdal-gad, 38 da Dileyan, da Mizfa, da Yokteyel, 39 da Lakish, da Bozkat, da Eglon, 40 da Kabbon, da Lahmam, da Kitlish, 41 da Gederot, da Bet-dagon, da Na'ama, da Makkeda, birane goma sha shida ke nan da ƙauyukansu. 42 Da kuma Libna, da Eter, da Ashan, 43 da Yifta, da Ashna, da Nezib, 44 da Kaila, da Akzib, da Maresha, birane tara ke nan da ƙauyukansu. 45 Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta. 46 Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod. 47 Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta. 48 Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne Shamir, da Yattir, da Soko, 49 da Danna, da Kiriyat-sanna, wato Debir, 50 da Anab, da Eshtemowa, da Anim, 51 da Goshen, da Holon, da Gilo. Birane goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu. 52 Da kuma Arab, da Duma, da Eshan, 53 da Yanim, da Bet-taffuwa, da Afeka, 54 da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu. 55 Da kuma Mawon, da Karmel, da Zif, da Yutta, 56 da Yezreyel, da Yokdeyam, da Zanowa, 57 da Kayin, da Gebeya, da Timna, birane goma ke nan da ƙauyukansu. 58 Halhul, da Bet-zur, da Gedor, 59 da Ma'arat, da Bet-anot da Eltekon, birane shida ke nan da ƙauyukansu. 60 Da kuma Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu. 61 Biranen da suke a jeji kuwa su ne Bet-araba, da Middin, da Sekaka, 62 da Nibshan, da Birnin Gishiri, da En-gedi, birane shida ke nan da ƙauyukansu. 63 Amma jama'ar Yahuza ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zaune a Urushalima ba, don haka Yebusiyawa suka yi zamansu da jama'ar Yahuza cikin Urushalima har wa yau.

Joshuwa 16

Yankin Ƙasar da aka Ba Ifraimu da Manassa

1 Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel. 2 Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa. 3 Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa'an nan ya gangara a teku. 4 A nan ne jama'ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo. 5 Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu. 6 Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa. 7 Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa'an nan ta gangara a Urdun. 8 Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa'an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu, 9 tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama'ar Manassa. 10 Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa suka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.

Joshuwa 17

1 Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ƙan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne. 2 Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne 'ya'yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu. 3 Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ƙan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 4 Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji. 5 Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun, 6 domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad. 7 Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan Entaffuwa. 8 Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa. 9 Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum. 10 Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas. 11 A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat. 12 Amma mutanen Manassa ba su iya su mallaki waɗannan birane ba, don haka Kan'aniyawa suka yi zamansu a wuraren. 13 Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi sai suka tilasta su su yi musu aikin dole, amma ba su iya korarsu ba. 14 Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama'a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.” 15 Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama'a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.” 16 Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.” 17 Joshuwa kuma ya ce wa jama'ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama'a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba, 18 amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan'aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”

Joshuwa 18

Rarraba Ƙasa a Shilo

1 Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada. 2 Har yanzu akwai sauran kabila bakwai na Isra'ila waɗanda ba su sami gādonsu ba tukuna. 3 Sai Joshuwa ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku? 4 Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina. 5 Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa. 6 Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa'an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji Allahnmu. 7 Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.” 8 Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.” 9 Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo. 10 Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.

Yankin Ƙasar da aka Ba Biliyaminu

11 Kuri'ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama'ar Yusufu. 12 A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare. 13 Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari. 14 Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa'an nan ta tsaya a Kiriyatba'al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. 15 A wajen kudu kuwa iyakar ta fara daga karkarar Kiriyat-yeyarim, daga can ta miƙa zuwa Efron a maɓuɓɓugar ruwan Neftowa. 16 Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel. 17 Sai ta nausa ta yi wajen arewa zuwa En-shemesh, sa'an nan ta tafi Gelilot wanda yake daura da hawan Adummim. Daga nan ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 18 Sai ta wuce ta yi arewa daura da gefen Bet-araba, daga nan ta gangara zuwa Araba. 19 Ta kuma zarce zuwa arewa daura da gefen Bet-hogla, ta tsaya a arewacin gaɓar Tekun Gishiri a ƙarshen Urdun wajen kudu. 20 Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda. 21 Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz, 22 da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel, 23 da Awwim, da Fara, da Ofra, 24 da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu. 25 Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot, 26 da Mizfa, da Kefira, da Moza, 27 da Rekem, da Irfeyel, da Tarala, 28 da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.

Joshuwa 19

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Saminu

1 Kuri'a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza. 2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada, 3 da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem, 4 da Eltola, da Betul, da Horma, 5 da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa, 6 da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu. 7 Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu, 8 da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu. 9 Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Zabaluna

10 Kuri'a ta uku ta faɗa a kan kabilar Zabaluna bisa ga iyalanta. Yankin ƙasar gādonsu ya kai har Sarid. 11 Iyakar ta hau wajen yamma zuwa Marala, ta kai Dabbeshet da rafin da yake gabas da Yakneyam. 12 Daga Sarid, ta nufi wajen gabas zuwa iyakar Kislotabar, sa'an nan ta bi ta Daberat da Yafiya. 13 Daga can ta miƙa wajen gabas zuwa Gat-hefer da Et-kazin, har zuwa Rimmon inda ta nausa zuwa Neya. 14 Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa'an nan ta faɗa a kwarin Iftahel. 15 Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna. 16 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Issaka

17 Kuri'a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta. 18 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem, 19 da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat, 20 da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez, 21 da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez. 22 Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa'an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu. 23 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Ashiru

24 Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta. 25 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf, 26 da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat. 27 Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul, 28 da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba. 29 Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib, 30 da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu. 31 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Naftali

32 Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta. 33 Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun. 34 Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun. 35 Garuruwan da suke da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret, 36 da Adama, da Rama, da Hazor, 37 da Kedesh, da Edirai, da En-hazor, 38 da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. 39 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Kabilar Dan

40 Kuri'a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta. 41 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh, 42 da Shalim, da Ayalon, da Itla, 43 da Elon, da Timna, da Ekron, 44 da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat, 45 da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon, 46 da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa. 47 Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan. 48 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Joshuwa

49 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu. 50 Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki. 51 Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.

Joshuwa 20

An Keɓe Biranen Mafaka

1 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, 2 “Ka faɗa wa jama'ar Isra'ila, su keɓe biranen mafaka waɗanda na faɗa wa Musa ya faɗa muku. 3 Domin idan wani mutum ya yi kisankai ba da niyya ba, ba kuma da saninsa ba, sai ya tsere zuwa can. Biranen za su zama muku mafaka daga mai bin hakkin jini. 4 Wanda ya yi kisankan sai ya tsere zuwa ɗaya daga cikin biranen, ya tsaya a bakin ƙofar birnin, ya bayyana wa dattawan garin abin da ya same shi. In sun ji, sai su shigar da shi a birnin, su ba shi wurin zama, ya zauna tare da su. 5 Idan mai bin hakkin jinin ya bi shi, ba za su ba shi wanda ya yi kisankan ba, domin bai kashe maƙwabcinsa da gangan ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu dā ma. 6 Zai yi zamansa a birnin har lokacin da aka gabatar da shi gaban dattawa don shari'a, sai kuma bayan rasuwar babban firist na lokacin, sa'an nan wanda ya yi kisankan zai iya komawa garinsu da gidansa daga inda ya tsere.” 7 Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza. 8 A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra'ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa. 9 Waɗannan su ne biranen mafaka da aka keɓe domin dukan Isra'ilawa, da baƙin da suke baƙuntaka cikinsu. Don duk wanda ya yi kisankai ba da niyya ba zai iya tserewa zuwa can don kada ya mutu ta hannun mai bin hakkin jini. Zai zauna a can har lokacin da za a gabatar da shi a gaban taron jama'a.

Joshuwa 21

Biranen da aka Ba Lawiyawa

1 Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele'azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama'ar Isra'ila. 2 Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan'ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.” 3 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu. 4 Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu. 5 Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa. 6 Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan. 7 Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna. 8 Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa. 9 Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata. 10 Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko. 11 Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak. 12 Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa. 13 Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata, 14 da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata, 15 da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata, 16 da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu. 17 Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata, 18 da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata. 19 Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu. 20-22 Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata. kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata. 25 Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta'anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata. 26 Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba sauran Kohatawa na iyalan Lawiyawa guda goma ne. 27 Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata. kuma ba su birane huɗu daga cikin kabilar Issaka, biranen su ne, Kishiyon da wuraren kiwo nata, da Daberat da wuraren kiwo nata, da Yarmut da wuraren kiwo nata, da Enganim da wuraren kiwo nata. cikin rabon kabilar Ashiru aka ba su birane huɗu, su ne Mishal da wuraren kiwo nata, da Abdon da wuraren kiwo nata, da Helkat da wuraren kiwo nata, da Rehob da wuraren kiwo nata. 32 Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata. 33 Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba iyalan Gershonawa guda goma sha uku ne. 34-35 Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata. kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra'ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata, da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata. cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata. 40 Dukan biranen da aka ba iyalan Merari na Lawiyawa guda goma sha biyu ne. 41 Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama'ar Isra'ila guda arba'in da takwas ne. 42 Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.

Isra'ilawa sun Mallaki Ƙasar

43 Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki. 44 Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko'ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu. 45 Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.

Joshuwa 22

Bagade a Bakin Urdun

1 Sa'an nan Joshuwa ya kira mutanen kabilar Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa. 2 Ya ce musu, “Kun aikata dukan abin da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku, kun kuma yi biyayya da dukan abin da na umarce ku. 3 Ba ku yar da 'yan'uwanku dukan waɗannan yawan kwanaki, har wa yau ba. Amma kuka kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku sosai. 4 Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun. 5 Sai dai ku kiyaye umarnai da dokokin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa, ku bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku.” 6 To, Joshuwa ya sa musu albarka, sa'an nan ya sallame su, suka koma gida. 7 Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka, 8 ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da 'yan'uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.” 9 Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran 'yan'uwansu Isra'ilawa a Shilo ta ƙasar Kan'ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa. 10 Sa'ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan'ana, suka gina babban bagade a wurin. 11 Sauran Isra'ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan'ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.” 12 Da Isra'ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi. 13 Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad. 14 Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila. 15 Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu, 16 “In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade. 17 Zunubin da aka yi a Feyor, ashe, bai ishe mu ba, har annoba ta wahalar da taron jama'ar Ubangiji? Ga shi, har yanzu ma ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba. 18 Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama'ar Isra'ila. 19 Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji inda alfarwa ta sujada take, ku sami abin mallaka a tsakaninmu, amma kada ku tayar wa Ubangiji, ku kuma tayar mana ta wurin gina wa kanku wani bagade dabam da bagaden Allahnmu. 20 Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra'ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.” 21 Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka amsa wa shugabannin iyalan Isra'ilawa suka ce, 22 “Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra'ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau. 23 Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana. 24 Saboda gudun gaba ne muka yi haka, domin kada wata rana 'ya'yanku su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ruwanku da Ubangiji, Allah na Isra'ila. 25 Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada. 26 Don haka muka ce, ‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, 27 amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.’ 'Ya'yanku kuma ba za su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ 28 Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’ 29 Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.” 30 Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai. 31 Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.” 32 Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra'ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mutanen Isra'ila, suka ba su rahoton abin da suka ji. 33 Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba. 34 Ra'ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”

Joshuwa 23

Joshuwa ya Yi wa Jama'a Jawabi

1 An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra'ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa. 2 Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa, 3 kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku. 4 Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma. 5 Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Ka ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku. 6 Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu, 7 domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da suke zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu. 8 Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau. 9 Gama Ubangiji ya kori manyan al'ummai ƙarfafa daga gabanku, har wa yau ba mutumin da ya isa ya yi hamayya da ku. 10 Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku. 11 Ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku. 12 Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da suke tare da ku, har kuka yi aurayya da juna, 13 to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasar nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 14 “A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba. 15 Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, hakanan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasar nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 16 Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”

Joshuwa 24

Jawabin Joshuwa na Bankwana a Shekem

1 Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra'ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra'ila. Suka hallara a gaban Allah. 2 Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka. 3 Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan'ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku. 4 Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar. 5 Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku. 6 Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku. 7 A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa. 8 Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu. 9 Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra'ila, har ya gayyaci Bal'amu, ɗan Beyor, ya zo ya la'anta ku. 10 Amma ban saurari Bal'amu ba, saboda haka ya sa muku albarka, ta haka na cece ku daga hannunsa. 11 Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku. 12 Na kuma aiki zirnako a gabanku, waɗanda suka kori sarakunan nan biyu na Amoriyawa daga gabanku. Ba takobinku, ko bakanku ya kore su ba. 13 Na ba ku ƙasar da ba ku yi wahala a kanta ba, da biranen da ba ku gina ba, ga shi, kuna zaune a ciki, kuna kuma cin 'ya'yan inabi, da na zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba.’ 14 “To fa, ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da sahihanci da aminci, ku yi watsi da gumakan da kakanninku suka bauta wa a hayin Kogin Yufiretis, da cikin Masar. 15 Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.” 16 Jama'a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka. 17 Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al'umman da muka ratsa. 18 Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.” 19 Amma Joshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, gama shi Allah mai tsarki ne, mai kishi kuma, ba kuwa zai gafarta laifofinku da zunubanku ba. 20 Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.” 21 Jama'a kuwa suka ce wa Joshuwa, “A'a, mu dai za mu bauta wa Ubangiji ne.” 22 Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.” Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.” 23 Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra'ila.” 24 Jama'a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.” 25 A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama'a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka'idodi. 26 Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari'ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji. 27 Sai ya ce wa jama'a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.” 28 Joshuwa kuwa ya sallami jama'ar, kowane mutum ya koma wurin gādonsa.

Rasuwar Joshuwa da ta Ele'azara

29 Bayan waɗannan al'amura, sai Joshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya rasu yana da shekara ɗari da goma da haihuwa. 30 Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash. 31 Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra'ilawa. 32 Kasusuwan Yusufu, waɗanda jama'ar Isra'ila suka kawo daga Masar, an binne su a Shekem a yankin ƙasar da Yakubu ya saya a bakin azurfa ɗari daga wurin 'ya'yan Hamor mahaifin Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusufu. 33 Ele'azara, ɗan Haruna kuma ya rasu, aka binne shi a Gebeya a garin ɗansa, Finehas, wanda aka ba shi a ƙasar tuddai ta Ifraimu.

Littafin Mahukunta 1

Yahuza da Saminu sun Ci Adoni-bezek

1 Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?” 2 Sai Ubangiji ya ce, “Yahuza ne zai tafi, ga shi, na ba da ƙasar a gare shi.” 3 Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi. 4 Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek. 5 Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa. 6 Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa. 7 Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.

Kabilar Yahuza ta Ci Urushalima da Hebron

8 Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta. 9 Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari. 10 Suka kuma tafi su yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.

Otniyel ya Ci Birnin Debir ya Auri Aksa

11 Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer. 12 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.” 13 Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure. 14 Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?” 15 Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.

Yawan Wuraren da Yahuza da Biliyaminu Suka Ci

16 Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da yake a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa. 17 Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa. 18 Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta. 19 Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe. 20 Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, a can. 21 Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.

Kabilar Yusufu ta Ci Betel

22 Jama'ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su. 23 Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz. 24 Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.” 25 Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka. 26 Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.

Yawan Wuraren da Manassa da Ifraimu suka Ci

27 Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta'anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan'aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar. 28 Sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan'aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba. 29 Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan'aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan'aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.

Yawan Wuraren da sauran Kabilai suka Ci

30 Mutanen Zabaluna ma ba su kori mazaunan Kattat da na Nahalal ba, amma Kan'aniyawa suka zauna tare da su, suna yi musu aikin gandu. 31 Haka kuma mutanen Ashiru ba su kori mazaunan Akko, da na Sidon, da Alab, da Akzib, da Helba, da Afek, da Rehob ba. 32 Amma Ashirawa suka yi zamansu tare da Kan'aniyawan ƙasar, gama ba su kore su ba. 33 Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan'aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu. 34 Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba. 35 Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu. 36 Iyakar Amoriyawa ta nausa ta kan hawan Akrabbim daga Sela zuwa gaba.

Littafin Mahukunta 2

Mala'ikan Ubangiji a Bokim

1 Mala'ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra'ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba. 2 Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi? 3 Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ” 4 Da mala'ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi. 5 Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.

Rasuwar Joshuwa

6 Da Joshuwa ya sallami Isra'ilawa, kowane mutum ya tafi domin ya ɗauki gādonsa, don ya mallaki tasa ƙasa. 7 Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra'ilawa. 8 Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma. 9 Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa. 10 Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.

Isra'ilawa sun bar Yi wa Ubangiji Sujada

11 Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al. 12 Suka bar yi wa Ubangiji Allah na kakanninsu sujada, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar. Suka fara yi wa allolin mutanen da suke zaune kewaye da su sujada. Suka rusuna wa allolin, da haka suka sa Ubangiji ya yi fushi. 13 Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba'al da Ashtarot. 14 Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba. 15 A duk sa'ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai. 16 Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su. 17 Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha'inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin. 18 Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu. 19 Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba. 20 Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa ya ce, “Saboda al'umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba, 21 don haka daganan gaba ba zan ƙara kore musu wata al'umma daga cikin al'umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba. 22 Da haka ne zan jarraba Isra'ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.” 23 Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al'ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.

Littafin Mahukunta 3

Al'umman da suka Ragu don a Jarraba Isra'ilawa

1 Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba. 2 Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba. 3 Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat, 4 don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa. 5 Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 6 Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.

Otniyel ya Ceci Isra'ilawa

7 Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada. 8 Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushanrishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas. 9 Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa. 10 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi. 11 Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.

Ehud ya Ceci Isra'ilawa daga Mowabawa

12 Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su. 13 Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko. 14 Isra'ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas. 15 Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud. 16 Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa. 17 Sa'an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne. 18 Da Ehud ya gama ba shi kyautan, sai ya sallami mutanen da suka ɗauko kyautan. 19 Amma Ehud ya juya ya koma daga wajen sassaƙaƙƙun duwatsu kusa da Gilgal, ya ce wa Eglon, “Ranka ya daɗe, na kawo maka saƙo na asiri.” Sai sarki ya ce wa fādawansa, “Ku ba mu wuri!” Dukansu kuwa suka fita, suka ba da wuri. 20 Ehud kuwa ya je wurinsa, yana zaune shi kaɗai a jinkakken shirayi mai sanyi. Sai Ehud ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah zuwa gare ka!” Sarki kuwa ya tashi daga inda yake zaune, 21 Ehud ya sa hannun hagunsa, ya zaro takobin da yake wajen cinyarsa ta dama, ya kirɓa masa a ciki. 22 Takobin ya shiga duk da ƙotar, kitse ya rufe ruwan takobin gama bai zare takobin daga cikin sarkin ba. Ƙazanta kuwa ta fita. 23 Ehud kuwa ya fita ta shirayin, ya kukkulle ƙofofin ɗakin. 24 Bayan da ya tafi, fādawan suka zo, suka ga ƙofofin ɗakin suna a kulle, sai suka zaci sarkin ya zaga ne ya yi bawali. 25 Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ba, suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe, sai ga ubangijinsu a ƙasa matacce. 26 Sa'ad da suke ta jira, Ehud ya riga ya tsere, ya wuce sassaƙaƙƙun duwatsu zuwa Seyira. 27 Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba. 28 Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa. 29 A lokacin ne suka kashe ƙarfafan mutane na Mowabawa mutum wajen dubu goma (10,000 ), ba wanda ya tsira. 30 A ranar nan Isra'ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.

Shamgar ya Ceci Isra'ilawa daga Filistiyawa

31 Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra'ilawa.

Littafin Mahukunta 4

Debora da Barak sun Ci Sisera

1 Bayan rasuwar Ehud, Isra'ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji. 2 Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin. 3 Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su. 4 Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra'ilawa. 5 Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra'ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari'a. 6 Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000 ), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna. 7 Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ” 8 Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.” 9 Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh. 10 Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000 ) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi. 11 Eber, Bakene, kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za'anannim wanda yake kusa da Kedesh. 12 Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor. 13 Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon. 14 Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000 ) biye da shi. 15 Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa. 16 Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al'ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira. 17 Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene. 18 Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule. 19 Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi. 20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, ‘Ko akwai wani a nan?’ Sai ki ce, ‘Babu.’ ” 21 Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa'ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu. 22 Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa. 23 A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan'ana, a gaban Isra'ilawa. 24 Isra'ilawa suka yi ta tsananta wa Yabin Sarkin Kan'ana har suka hallaka shi.

Littafin Mahukunta 5

Waƙar Debora da Barak

1 A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka, 2 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi. Mutane suka sa kansu da farin ciki. Alhamdu lillahi! 3 Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna, Ku lura, ya ku hakimai, Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra'ila. 4 Ya Ubangiji, sa'ad da ka bar duwatsun Seyir, Sa'ad da ka fito daga jihar Edom, Ƙasa ta girgiza, Ruwan sama ya zubo daga sararin sama, I, gizagizai suka kwararo da ruwa. 5 Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina'i, A gaban Ubangiji, Allah na Isra'ila. 6 A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, Ayarori suka daina bi ta ƙasar, Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi. 7 Garuruwan Isra'ila, ba kowa ciki, Ba kowa ciki, sai da na zo. Na zo kamar uwa ga Isra'ila, 8 Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba. 9 Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila, Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! 10 Ku ba da labari, Ku da kuke haye da fararen jakuna, Kuna zaune a shimfiɗu, Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku. 11 Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyi Suna ba da labarin nasarar Ubangiji, Wato nasarar jama'ar Isra'ila! Sa'an nan jama'ar Ubangiji Suna tahowa daga biranensu. 12 Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba! Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba! Ka ci gaba, kai Barak, Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba! 13 Sa'an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu, Jama'ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi. 14 Daga Ilraimu mutane suka gangaro zuwa kwari, Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta. Daga Makir shugabannin sojoji suka zo, Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro. 15 Shugabannin Issaka suna tare da Debora, Hakika, Issaka ya zo, Barak kuma ya zo, Suka bi bayansu zuwa kwari. Amma kabilar Ra'ubainu ta rarrabu, Ba su shawarta su zo ba. 16 Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki? Don su saurari makiyaya na kiran garkuna? Hakika kabilar Ra'ubainu ta rarrabu, Ba su shawarta su zo ba. 17 Kabilar Gad suna tsaya a gabashin Urdun, Kabilar Dan kuma ta tsaya a wuraren kiwo. Kabilar Ashiru ta zauna a bakin teku, Sun zauna a gefen teku. 18 Amma mutanen Zabaluna da na Naftali Suka kasai da ransu a bakin dāga. 19 Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta'anak, A rafin Magiddo. Sarakunan Kan'ana suka yi yaƙi, Amma ba su kwashe azurfa ba. 20 Daga sama, taurari suka yi yaƙi, Suna gilmawa a sararin sama Suka yi yaƙi da Sisera. 21 Ambaliyar Kishon ta kwashe su, Wato tsohon Kogin Kishon. Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi! 22 Sa'an nan dawakai sun yi ta rishi Suna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu. 23 Mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ka la'anta Meroz, Ka la'anta mazauna cikinta sosai, Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba, Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.” 24 Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin mata, sai Yayel, Matar Eber, Bakene, Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin matan da suke a alfarwai. 25 Sisera ya roƙi ruwan sha, Sai ta ba shi madara, Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya. 26 Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta, Ta riƙe guduma a guda hannun, Ta bugi Sisera, kansa ya fashe, Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje. 27 Ya fāɗi a gwiwoyinta, Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta. A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi, Ya fāɗi matacce har ƙasa. 28 Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi, Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce, “Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa? Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?” 29 'Yan matanta mafi hikima suka amsa mata, Ita kuwa ta yi nanatawa, tana cewa, 30 “Nema suke kurum su sami ganima, su raba, Yarinya ɗaya ko biyu domin kowane soja, Tufafi masu tsada domin Sisera, Rinannun tufafi masu ado domin sarauniya.” 31 Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu, Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana! Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in.

Littafin Mahukunta 6

Kiran Gidiyon

1 Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai. 2 Madayanawa kuwa sun fi Isra'ilawa ƙarfi, saboda haka Isra'ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka. 3 Duk lokacin da Isra'ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu. 4 Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra'ila, domin Isra'ilawa ko dabbobinsu. 5 Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar. 6 Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su. 7 Da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su, 8 sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar. 9 Na cece ku daga Masarawa, da kuma waɗanda suka yi yaƙi da ku a nan. Na kore su a gabanku, na ba ku ƙasarsu. 10 Na faɗa muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.’ Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.” 11 Mala'ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa. 12 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kai jarumi ne, Ubangiji kuma yana tare da kai.” 13 Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar?’ Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.” 14 Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.” 15 Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.” 16 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.” 17 Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni. 18 Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.” Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.” 19 Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak. 20 Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi. 21 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa. 22 Da Gidiyon ya gane mala'ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala'ikan Ubangiji fuska da fuska.” 23 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.” 24 Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer. 25 A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi. 26 Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.” 27 Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare. 28 Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina. 29 Suka ce wa juna, “Wa ya yi wannan abu?” Da suka binbincika, sai suka tarar Gidiyon ne, ɗan Yowash, ya yi shi. 30 Sai suka ce wa Yowash, “Ka kawo ɗanka a kashe, gama ya rushe bagaden gunkin nan Ba'al, ya kuma sare gumakan da suke kusa da shi.” 31 Yowash kuwa ya ce wa dukan waɗanda suka tasar masa, “Za ku yi hamayya domin gunkin nan Ba'al, ko kuwa za ku goyi bayansa? Duk wanda ya yi hamayya dominsa za a kashe shi da safe. Idan shi allah ne, to, bari ya yi hamayya don kansa, gama an farfashe bagadensa.” 32 A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.” 33 Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel. 34 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi. 35 Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi. 36 Sa'an nan Gidiyon ya ce wa Allah, “Ka ce za ka sa ni in ceci Isra'ilawa. 37 To, zan shimfiɗa uku a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, sa'an nan zan sani za ka ceci Isra'ilawa ta hannuna kamar yadda ka faɗa.” 38 Haka kuwa ya zama Kashegari Gidiyon ya tashi da sassafe, sai ya matse ulun, ruwan raɓa da ya matse daga ulun kuwa, ya cika ƙwarya. 39 Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.” 40 Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.

Littafin Mahukunta 7

Gidiyon ya Ci Madayanawa

1 Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin. 2 Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’ 3 Yanzu sai ka ce wa mutanen, ‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!’ ” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000 ) suka koma, dubu goma (10,000 ) suka tsaya. 4 Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.” 5 Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.” 6 Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan. 7 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.” 8 Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin. 9 A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka. 10 Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka. 11 Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba. 12 Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su. 13 Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.” 14 Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!” 15 Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.” 16 Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun. 17 Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka. 18 Sa'ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoni, sai ku kuma ku busa ƙahonin a kowane gefen sansani, sa'an nan ku yi ihu, ku ce, ‘Ubangiji da Gidiyon!’ ” 19 Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu. 20 Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!” 21 Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu. 22 Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat. 23 Jama'ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa. 24 Gidiyon kuma ya aika a dukan ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce musu, “Ku gangaro, ku yaƙi Madayanawa, ku tare mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.” Aka kuwa kira dukan Ifraimawa, su kuwa suka hana wa Madayanawa mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara. 25 Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.

Littafin Mahukunta 8

1 Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai. 2 Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa. 3 Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.

Nasara ta Ƙarshe a kan Madayanawa

4 Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta. 5 Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.” 6 Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?” 7 Gidiyon ya ce, “To, sa'ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayuwan jeji.” 8 Daga can ya tafi Feniyel, ya roƙe su yadda ya roƙi mutanen Sukkot. Mutanen Feniyel kuma suka amsa masa daidai yadda mutanen Sukkot suka amsa masa. 9 Sai Gidiyon ya ce wa mutanen Feniyel, “Sa'ad da na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiya.” 10 Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000 ), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000 ), masu takuba. 11 Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato. 12 Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice. 13 Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres. 14 Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba'in da bakwai. 15 Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!” 16 Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa. 17 Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin. 18 Sa'an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?” Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da 'ya'yan sarki.” 19 Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.” 20 Ya ce wa Yeter, ɗan farinsa, “Tashi, ka kashe su.” Amma saurayin bai zare takobinsa ba, gama yana jin tsoro domin shi yaro ne. 21 Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.

Sauran Ayyukan Gidiyon

22 Sa'an nan mutanen Isra'ila suka ce wa Gidiyon, “Ka yi mulkinmu, kai da 'ya'yanka, da jikokinka, gama ka cece mu daga hannun Madayanawa.” 23 Gidiyon ya ce musu, “Ba zan yi mulkinku ba, ɗana kuma ba zai yi mulkinku ba, Ubangiji ne zai yi mulkinku.” 24 Ya ci gaba ya ce, “Ina roƙon kowannenku ya ba ni 'yan kunne daga cikin ganimar da ya kwaso.” (Gama Madayanawa suna da 'yan kunne na zinariya, gama su mutanen hamada ne.) 25 Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba 'yan kunnen da ya kwaso ganima. 26 Nauyin 'yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700 ), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu. 27 Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra'ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa. 28 Da haka Isra'ilawa suka mallaki Madayanawa har ba su zamar musu barazana ba. Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in a zamanin Gidiyon.

Mutuwar Gidiyon

29 Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa. 30 Yana kuma da 'ya'ya maza saba'in, gama yana da mata da yawa. 31 Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take a Shekem, ta haifi masa ɗa, ya sa masa suna Abimelek. 32 Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya rasu da kyakkyawan tsufa. Aka binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa, a Ofra, birnin kabilar Abiyezer. 33 Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra'ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba'al sujada. Suka yi Ba'al-berit ya zama allahnsu. 34 Suka daina bauta wa Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga magabtan da suke kewaye da su. 35 Ba su kuwa sāka wa iyalin Gidiyon da alheri ba, saboda dukan alherin da ya yi wa Isra'ilawa.

Littafin Mahukunta 9

Sarautar Abimelek

1 Abimelek, ɗan Yerubba'al, wato Gidiyon, ya tafi Shekem wurin dukan dangin mahaifiyarsa, ya ce musu, 2 “Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, ‘Me ya fi muku kyau, 'ya'yan Yerubba'al, maza saba'in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?’ Amma ku tuna fa ni jininku ne.” 3 Sai dangin mahaifiyarsa suka yi magana da shugabannin Shekem saboda shi. Zuciyarsu kuwa ta saje da Abimelek, gama suka ce, “Shi ɗan'uwanmu ne.” 4 Suka kuma ba shi azurfa saba'in daga cikin gidan gunkin nan Ba'al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar 'yan iska waɗanda suka bi shi. 5 Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe 'yan'uwansa maza, wato 'ya'yan Yerubba'al, mutum saba'in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba'al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya. 6 Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al'amudin da yake a Shekem. 7 Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku! 8 Wata rana itatuwa suka taru don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Kai ka zama sarkinmu.’ 9 Amma itacen zaitun ya ce musu, ‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’ 10 Sai kuma itatuwa suka ce wa itacen ɓaure, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’ 11 Amma itacen ɓaure ya ce musu, ‘In bar kyawawan 'ya'yana masu zaƙi, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’ 12 Itatuwa kuma suka ce wa kurangar inabi, ‘Ki zo, ki mallake mu.’ 13 Sai kurangar inabi ta ce, ‘In bar ruwan inabina wanda yake faranta zuciyar alloli da ta mutane, don in tafi, in yi ta fama da itatuwa?’ 14 Sa'an nan dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’ 15 Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.’ ” 16 Yotam ya ci gaba da cewa, “Yanzu kun naɗa Abimelek sarki da zuciya ɗaya ke nan? Kun yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ke nan? Wannan ne abin da ya cancance shi? 17 Ku tuna fa mahaifina ya yi yaƙi dominku. Ya kasai da ransa domin ya cece ku daga Madayanawa. 18 Amma ga shi, yau kun juya kuna gāba da gidan mahaifina. Kun kashe 'ya'yansa maza, su saba'in, a dutse guda, kuka naɗa Abimelek, ɗan da baiwa ta haifa, ya zama sarki a Shekem, don dai kawai shi ɗan'uwanku ne. 19 Yanzu dai idan abin da kuka yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ne, to, sai ku yi farin ciki da Abimelek, ku sa shi kuma ya ji daɗinku. 20 Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.” 21 Sa'an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan'uwansa Abimelek. 22 Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra'ila. 23 Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa. 24 Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa. 25 Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek. 26 Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa suka yi ƙaura zuwa Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka amince da shi. 27 Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek. 28 Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku! 29 Da ma a ce nake shugabancin mutanen nan, da sai in hamɓare Abimelek!” Sai ya ce wa Abimelek, “Ka tara yawan rundunarka ka fito.” 30 Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga'al, ɗan Ebed, sai ya husata. 31 Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka. 32 Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura. 33 Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!” 34 Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu. 35 Ga'al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu. 36 Sa'ad da Ga'al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.” Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.” 37 Ga'al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.” 38 Sa'an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?’ Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.” 39 Ga'al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek. 40 Abimelek kuwa ya runtumi Ga'al, shi kuwa ya gudu. Mutane da yawa suka ji rauni, ya bi su har bakin ƙofar birnin. 41 Sai Abimelek ya zauna a Aruma. Zebul kuwa ya kori Ga'al da 'yan'uwansa, ya hana su zama a Shekem. 42 Kashegari mutanen Shekem suka tafi saura, sai aka faɗa wa Abimelek. 43 Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su. 44 Abimelek kuma da ƙungiyar da take tare da shi, suka hanzarta, suka tsare ƙofar birnin. Sauran ƙungiya biyu suka ruga, suka faɗa wa dukan waɗanda suke cikin saura, suka karkashe su. 45 Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri. 46 Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira. 47 Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya. 48 Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi. 49 Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu. 50 Sa'an nan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta da sansani, ya ci birnin. 51 Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar. 52 Abimelek kuwa ya zo ya yaƙi hasumiyar. Ya je kusa da ƙofar hasumiyar don ya ƙone ta. 53 Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje. 54 Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu. 55 Da Isra'ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai dukansu suka tafi gida. 56 Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe 'yan'uwansa maza, su saba'in. 57 Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba'al, kuma ya kama su.

Littafin Mahukunta 10

Tola da Yayir sun Shugabanci Isra'ilawa

1 Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu. 2 Ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da uku, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir. 3 Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu. 4 Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir. 5 Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.

Ammonawa sun Matsa wa Isra'ilawa

6 Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada. 7 Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa. 8 Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawa da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune. 9 Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai. 10 Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.” 11 Ubangiji ya amsa musu, ya ce, “Ban cece ku daga hannun Masarawa, da Amoriyawa, da Ammonawa, da Filistiyawa, 12 da Sidoniyawa, da Amalekawa, da Mawonawa ba, wato su da suka matsa muku a dā, ku kuma kuka yi kuka gare ni? 13 Amma duk da haka kuka bar bina, kuka yi sujada ga waɗansu alloli, don haka ni kuma ba zan ƙara cetonku ba. 14 Tafi, ku yi wa allolin da kuka zaɓa kuka, don su cece ku a lokacin wahalarku.” 15 Amma Isra'ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.” 16 Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha. 17 Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa. 18 Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaƙi da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”

Littafin Mahukunta 11

Yefta ya Ceci Isra'ilawa daga Hannun Ammonawa

1 Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa. 2 Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.” 3 Sai Yefta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. 'Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi. 4 Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. 5 Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob. 6 Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.” 7 Amma Yefta ya ce wa dattawan Gileyad, “Ba ku kuka ƙi ni, kuka kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuka zo wurina a lokacina da kuke shan wahala?” 8 Sai dattawan Gileyad suka amsa masa, “Abin da ya sa muka zo wurinka yanzu, shi ne domin ka tafi tare da mu ne mu yi yaƙi da Ammonawa, ka kuma zama shugaban dukan jama'ar Gileyad.” 9 Yefta kuwa ya ce musu, “Idan kuka koma da ni gida domin in yi yaƙi da Ammonawa, idan Ubangiji ya ba da su a hannuna, to, zan zama shugabanku.” 10 Suka amsa suka ce wa Yefta, “Ubangiji shi ne shaida tsakaninmu, lalle za mu yi maka kamar yadda ka ce.” 11 Yefta kuwa ya tafi tare da dattawa Gileyad. Su kuwa suka naɗa shi shugabansu da sarkin yaƙinsu. Yefta kuwa ya faɗi dukan abin da yake zuciyarsa a gaban Ubangiji a Mizfa. 12 Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?” 13 Sarkin Ammonawa ya amsa wa jakadun Yefta cewa, “Domin lokacin da Isra'ilawa suna tahowa daga Masar sun ƙwace mini ƙasa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa Kogin Urdun. Yanzu sai ka mayar mini da ita cikin lumana.” 14 Yefta kuma ya sāke aike da jakadu wurin Sarkin Ammonawa, 15 tare da amsa, ya ce, “Isra'ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba. 16 Amma sa'ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh. 17 Sa'an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra'ilawa suka zauna a Kadesh. 18 “Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab. 19 Sa'an nan Isra'ilawa suka aike da jakadu wurin Sihon Sarkin Heshbon ta Amoriyawa, suka roƙe shi, suka ce, ‘Ka yarda mana mu wuce ta ƙasarka.’ 20 Amma Sihon bai amince wa Isra'ilawa su bi ta ƙasarsa, su wuce ba. Ya kuwa tattara mutanensa, ya kafa sansaninsa a Yahaza, ya yi yaƙi da Isra'ilawa. 21 Ubangiji Allah na Isra'ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra'ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar. 22 Suka mallaki dukan ƙasar Amoriyawa tun daga Kogin Arnon har zuwa Kogin Yabbok, tun kuma daga jeji zuwa Kogin Urdun. 23 To, ai, ka ga Ubangiji Allah na Isra'ila ne ya kori Amoriyawa saboda jama'ar Isra'ila. To, yanzu so kake ka ƙwace mana? 24 Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi. 25 Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra'ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su? 26 Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba? 27 Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara'anta tsakanin Isra'ilawa da Ammonawa.” 28 Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba. 29 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa. 30 Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna, 31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.” 32 Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa. 33 Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra'ilawa.

'Yar Yefta

34 Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga 'yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai 'yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko 'ya. 35 Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.” 36 Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa'adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa'adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.” 37 Ta kuma ce masa, “Ina so ka yardar mini in tafi kan duwatsu ni da ƙawayena in yi makokin budurcina har wata biyu.” 38 Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu. 39 Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa'adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al'ada a cikin Isra'ila, 40 wato matan Isra'ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don 'yar Yefta, mutumin Gileyad.

Littafin Mahukunta 12

Yefta da Mutanen Ifraimu

1 Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.” 2 Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba. 3 Sa'ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?” 4 Sa'an nan Yefta ya tara dukan mutanen Gileyad, suka yi yaƙi da mutanen Ifraimu, suka ci su. Mutanen Ifraimu suka ce musu, “Ku mutanen Gileyad masu neman mafaka ne a cikin Ifraimu da Manassa!” 5 Mutanen Gileyad suka hana mutanen Ifraimu hayewa ta mashigan Kogin Urdun. Idan wani mutumin Ifraimu gujajje ya ce, “Ku bar ni in haye.” Sai mutanen Gileyad su tambaye shi, “Kai mutumin Ifraimu ne?” Idan ya ce, “A'a,” 6 sai su ce masa, to, ka ce, “Shibbolet,” sai mutum ya ce, “Sibbolet,” gama ba ya iya faɗa daidai. Sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Mutanen Ifraimu da aka kashe a lokacin su dubu arba'in da dubu biyu (42,000 ) ne. 7 Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra'ilawa shekara shida, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.

Ibzan, da Elon, da Abdon sun Shugabanci Isra'ilawa

8 Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra'ilawa. 9 Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai. 10 Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami. 11 Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra'ilawa shekara goma. 12 Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Ayalon a ƙasar Zabaluna. 13 Bayan Elon kuma, sai Abdon, ɗan Hillel, mutumin Firaton, ya shugabanci Isra'ilawa. 14 Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas. 15 Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.

Littafin Mahukunta 13

Haihuwar Samson

1 Isra'ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in. 2 Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa. 3 Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa. 4 Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu, 5 gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.” 6 Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala'ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba. 7 Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.” 8 Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.” 9 Allah kuwa ya ji roƙon Manowa, ya sāke aiko da mala'ikansa wurin matar, sa'ad da take a saura, mijinta kuwa ba ya tare da ita. 10 Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.” 11 Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?” Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.” 12 Manowa kuma ya ce, “Lokacin da maganarka ta cika, wane irin yaro ne zai zama, me kuma za mu yi?” 13 Mala'ikan Ubangiji ya amsa, ya ce wa Manowa, “Sai matarka ta kiyaye dukan abin da na faɗa mata. 14 Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.” 15-16 Manowa dai bai san mala'ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala'ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.” Amma mala'ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.” 17 Manowa ya ce, “Ka faɗa mana sunanka domin lokacin da maganarka ta cika mu girmama ka.” 18 Mala'ikan Ubangiji ya ce masa, “Don me kake tambayar sunana? Sunana asiri ne.” 19 Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gari, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala'ika kuma ya yi al'ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo. 20 Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa. 21 Mala'ikan Ubangiji bai sāke bayyana ga Manowa da matarsa ba. Manowa kuma ya gane mala'ikan Ubangiji ne. 22 Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!” 23 Amma matarsa ta ce masa, “Da Ubangiji yana so ya kashe mu, ai, da bai karɓi hadayar ƙonawa da hadayar gārinmu ba, da kuma bai nuna mana, ko ya faɗa mana waɗannan abubuwa ba.” 24 Matar kuwa ta haifi ɗa, aka raɗa masa suna Samson. Yaron ya yi girma, Ubangiji ya sa masa albarka. 25 Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa'ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

Littafin Mahukunta 14

Samson da Budurwa a Timna

1 Samson kuwa ya gangara zuwa Timna inda ya ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa. 2 Sa'ad da ya hauro zuwa gida sai ya faɗa wa iyayensa, ya ce, “Na ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa a Timna, ina so ku auro mini ita.” 3 Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin 'yan'uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin 'yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.” 4 Iyayensa ba su san al'amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra'ilawa. 5 Samson kuwa ya gangara zuwa Timna, shi da iyayensa. Da ya isa gonakin inabin Timna, sai ga sagarin zaki ya taso masa da ruri. 6 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba. 7 Sa'an nan ya gangara ya yi zance da budurwar, yana kuwa sonta. 8 Bayan 'yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki. 9 Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba. 10 Mahaifinsa ya tafi gidan iyayen yarinyar, Samson kuma ya shirya liyafa a can, gama haka samari sukan yi. 11 Sa'ad da Filistiyawa suka gan shi suka sa samari talatin su zauna tare da shi. 12 Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado. 13 Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni riguna talatin na ado.” Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.” 14 Sai ya ce musu, “Daga mai ci, abinci ya fito, Daga kuma mai ƙarfi, zaƙi ya fito.” Ba su iya ba da amsar ba har kwana uku. 15 A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?” 16 Sai matar Samson ta yi kuka a gabansa tana cewa, “Kai dai maƙiyina ne, ba masoyina ba, ka yi wa mutanena ka-cici-ka-cici, amma ba ka gaya mini amsarsa ba.” Amma ya ce mata, “Ko iyayena ma ban faɗa musu ba, sai in faɗa miki?” 17 Ta kuwa yi ta yi masa kuka har rana ta bakwai ta ƙarewar bikinsu. Amma a rana ta bakwai, ya faɗa mata amsar saboda yawan fitinarta. Ita kuwa ta faɗa wa mutanenta amsar ka-cici-ka-cicin. 18 A rana ta bakwai, kafin rana ta faɗi, mutanen garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaƙi? Me kuma ya fi zaki ƙarfi?” Ya kuwa ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, Da ba ku san amsar ka-cici-ka-cicin ɗin nan ba.” 19 Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru. 20 Aka ɗauki matar Samson aka ba wanda ya yi masa abokin ango.

Littafin Mahukunta 15

1 Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.” Amma mahaifinta bai yardar masa ba. 2 Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.” 3 Sai Samson ya ce musu, “A wannan lokaci, zan zama marar laifi saboda abin da zan yi wa Filistiyawa.” 4 Ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku, ya haɗa wutsiyoyinsu, wato wutsiya da wutsiya, sa'an nan ya ɗaura jiniya tsakanin kowaɗanne wutsiya biyu. 5 Da ya sa wa jiniyar wuta, ya sake su zuwa cikin hatsin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi, da hatsin da yake a tsaye, da gonakin zaitun. 6 Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?” Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta. 7 Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!” 8 Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.

Samson ya ci Nasara a kan Filistiyawa

9 Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai. 10 Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?” Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.” 11 Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?” Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.” 12 Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.” Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.” 13 Suka ce masa, “A'a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa'an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen. 14 Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta. 15 Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin. 16 Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce. “Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu, Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.” 17 Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi. 18 Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?” 19 Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau. 20 Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

Littafin Mahukunta 16

Samson a Gaza

1 Daga can Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa, sai ya shiga wurinta. 2 Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa'an nan mu kashe shi.” 3 Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa'an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.

Samson da Delila

4 Bayan wannan kuma sai ya kama ƙaunar wata mace mai suna Delila a kwarin Sorek. 5 Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100 ).” 6 Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.” 7 Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.” 8 Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su. 9 Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba. 10 Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba'a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.” 11 Ya ce mata, “Idan suka ɗaure ni da sababbin igiyoyi waɗanda ba a yi amfani da su ba, to, zan rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.” 12 Sai Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi, ta ɗaure shi da su, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa na zuwa kanka, Samson!” Amma ya katse igiyoyin da ta ɗaure shi da su kamar silin zare. Mutanen kuwa na nan laɓe a wani ɗaki. 13 Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.” Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai da suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.” 14 Sa'ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren. 15 Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.” 16 Sa'ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu. 17 A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.” 18 Sa'ad da Delila ta gane ya faɗa mata ainihin gaskiya, sai ta aika a kirawo shugabannin Filistiyawa tana cewa, “A wannan karo ku zo, domin ya faɗa mini ainihin gaskiyar.” Shugabannin Filistiyawa kuwa suka zo wurinta da kuɗi a hannu. 19 Ta kuwa sa shi ya yi barci a cinyoyinta, sai ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske tukkwayen nan bakwai da suke kansa. Sa'an nan ta yi ƙoƙari ta sa ya harzuƙa, amma ƙarfinsa ya rabu da shi. 20 Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi. 21 Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku. 22 Amma gashin kansa ya fara tohowa.

Samson ya Mutu

23 Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!” 24 Da mutane suka gan shi, sai suka raira waƙar yabon allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya ba da maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya fallasa ƙasarmu, ya kashe mutanenmu da yawa.” 25 Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai. 26 Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da yake ɗauke da gidan nan, domin in jingina.” 27 Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson. 28 Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.” 29 Sai Samson ya kama ginshiƙai biyu da suke a tsakiya, waɗanda suke ɗauke da gidan. Ya riƙe su da hannunsa biyu, ɗaya a kowane hannu, sa'an nan ya jingina jikinsa a kansu, 30 ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa'ad da yake da rai. 31 'Yan'uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin.

Littafin Mahukunta 17

Gumakan Mika

1 Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika. 2 Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100 ), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.” Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.” 3 Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100 ). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la'anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.” 4 Da ya mayar mata da azurfar, ta ɗibi azurfa ɗari biyu ta ba maƙerin azurfa, shi kuwa ya sassaƙa gunki ya kuma yi na zubi. Aka ajiye su a gidan Mika. 5 Mika kuwa yana da ɗakin gumaka. Ya yi gumaka, da falmaransu, da kan gida. Ya keɓe ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza domin ya zama firist nasa. 6 A wannan lokaci ba sarki a Isra'ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama. 7 Akwai wani saurayi Balawe da yake zama a Baitalami ta Yahudiya. 8 Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa'ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu. 9 Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?” Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.” 10 Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.” 11 Balawen kuwa ya yarda ya zauna tare da Mika. Ya kuwa zama kamar ɗa ga Mika. 12 Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa. 13 Sa'an nan Mika ya ce, “Yanzu na sani Ubangiji zai sa mini albarka, da yake na sami Balawe ya zamar mini firist.”

Littafin Mahukunta 18

Mika da Kabilar Dan

1 A kwanakin nan ba sarki a Isra'ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra'ila ba. 2 Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika. 3 Sa'ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?” 4 Ya ce musu, “Mun yi yarjejeniya da Mika, in yi masa aikin firist, shi kuma ya biya ni.” 5 Suka ce masa, “In ka yarda ka roƙar mana Allah ko tafiyarmu na da sa'a.” 6 Firist ɗin ya ce musu, “Kada ku damu, Ubangiji yana tare da ku a tafiyarku.” 7 Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha'anin kome da kowa. 8 Da mutanen nan biyar suka koma wurin 'yan'uwansu a Zora da Eshtawol, sai 'yan'uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu. 9 Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni'ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta! 10 Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.” 11 Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol. 12 Suka tafi suka kafa sansani a yammacin Kiriyat-yeyarim, birni ne a Yahudiya. Saboda haka ake kiran wurin Mahanedan, wato sansanin Dan, har wa yau. 13 Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika. 14 Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?” 15 Sai suka juya zuwa gidan Mika, inda saurayin nan Balawe yake, suka gaishe shi. 16 Danawa ɗari shida ɗin da suka yi shirin yaƙi, suka tsaya a bakin ƙofa. 17 Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi. 18 Sa'ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?” 19 Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra'ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?” 20 Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su. 21 Suka juya, suka tafi da 'ya'yansu da dabbobinsu, da mallakarsu. 22 Sa'ad da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa. 23 Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan 'yan iska?” 24 Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa'an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ” 25 Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.” 26 Sa'an nan Danawa suka kama hanyarsu. Da Mika ya ga dai sun fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida. 27 Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin. 28 Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha'ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki. 29 Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne. 30 Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta. 31 Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.

Littafin Mahukunta 19

Balawe da Ƙwarƙwararsa

1 A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawe da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa. 2 Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu. 3 Sa'an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki. 4 Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare. 5 A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.” 6 Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.” 7 Sa'ad da mutumin ya tashi zai tafi sai mahaifin macen ya roƙe shi, ya kuma kwana. 8 A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare. 9 Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.” 10 Amma mutumin bai yarda ya sāke kwana ba, sai ya tashi shi da ƙwarƙwararsa suka kama hanya. Ya kai daura da Yebus, wato Urushalima ke nan. Yana tare da jakinsa biyu da ya yi musu shimfiɗa, da ƙwarƙwararsa. 11 Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.” 12 Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya, 13 mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.” 14 Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu. 15 Suka ratse don su kwana a Gibeya. Balawen ya tafi ya zauna a dandalin garin, gama ba wanda ya kai su gidansa su kwana. 16 To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne. 17 Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?” 18 Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungu da yake ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa. 19 Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.” 20 Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.” 21 Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha. 22 Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!” 23 Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya. 24 Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!” 25 Amma 'yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa'an nan suka ƙyale ta. 26 Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira. 27 Sa'ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar. 28 Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa'an nan ya kama hanya zuwa gida. 29 Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko'ina cikin dukan ƙasar Isra'ila. 30 Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”

Littafin Mahukunta 20

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

1 Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa. 2 Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000 ). 3 Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra'ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra'ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.” 4 Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana. 5 Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa. 6 Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila. 7 Dukanku nan Isra'ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al'amari?” 8 Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa. 9 Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi. 10 Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.” 11 Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi. 12 Kabilar Isra'ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata? 13 Yanzu sai ku ba da mutanen nan 'yan iska da suke cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra'ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar 'yan'uwansu, Isra'ilawa ba. 14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fita daga Gibeya gaba ɗaya domin su yi yaƙi da jama'ar Isra'ila. 15 A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da dubu shida (26,000 ). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai. 16 Daga cikin waɗannan duka akwai zaɓaɓɓun mutane bakwai, bahagwai. Kowannensu yana iya ya baraci gashi guda da majajjawa ba kuskure. 17 Isra'ilawa kuwa banda kabilar Biliyaminu, suka tara mayaƙa dubu ɗari huɗu (400,000 ) horarru.

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

18 Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.” 19 Sa'an nan Isra'ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya. 20 Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya. 21 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000 ), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar. 22-23 Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?” Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.” Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā. 24 Sai mutanen Isra'ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu. 25 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000 ) daga cikin Isra'ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne. 26 Dukan rundunan Isra'ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa'an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama. sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?” Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa. 29 Isra'ilawa kuwa suka sa 'yan kwanto kewaye da Gibeya. 30 Sa'an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā. 31 Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra'ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye. 32 Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.” Amma Isra'ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.” 33 Isra'ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba'altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito. 34 Horarrun sojojin Isra'ila, su dubu goma (10,000 ), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba. 35 Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100 ) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne. 36 Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi. Mutanen Isra'ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto. 37 Sai 'yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin. 38 Alamar da mayaƙan Isra'ila da na 'yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin. 39 Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.” 40 Amma sa'ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama. 41 Da mutanen Isra'ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu. 42 Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa. 43 Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas. 44 Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000 ). 45 Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu. 46 Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000 ) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne. 47 Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata huɗu. 48 Mutanen Isra'ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.

Littafin Mahukunta 21

Mata domin Mutanen Biliyaminu

1 Mutanen Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji ƙaƙƙarfan alkawari a Mizfa cewa, “Ba wani daga cikinmu da zai ba da 'yarsa aure ga mutumin Biliyaminu.” 2 Sai mutanen Isra'ila suka zo Betel, suka zauna a nan a gaban Allah har maraice. Suka yi makoki mai zafi. 3 Suka ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa wannan abu ya faru a cikin Isra'ila, har da za a rasa kabila guda ta Isra'ila?” 4 Kashegari mutanen suka tashi da safe, suka gina bagade a can. Suka miƙa hadayun ƙonawa da na salama. 5 Suka kuma ce, “Daga cikin kabilar Isra'ila, wace ce ba ta halarci wannan taro na gaban Ubangiji ba?” Gama sun riga sun yi ƙaƙƙarfan alkawari cewa, “Duk wanda bai hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba, za a kashe shi.” 6 Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi juyayin 'yan'uwansu, mutanen Biliyaminu, suka ce, “Yau an hallaka kabila guda daga cikin Isra'ila. 7 Ƙaƙa za mu yi don mutanen da suka ragu su sami mata. Ga shi, mum riga mu rantse da Ubangiji ba za mu ba su 'ya'yanmu mata su aura ba?” 8 Sa'an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra'ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?” Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron. 9 Gama sa'ad da aka tattara mutanen, aka ga ba wani daga cikin mazaunan Yabesh-gileyad a wurin. 10 Taron jama'a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000 ) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara. 11 Abin da za ku yi ke nan, ku je ku kashe dukan maza, da kowace mace wadda ba budurwa ba ce.” 12 Suka sami budurwai ɗari huɗu daga mutanen Yabesh-gileyad, sai suka kawo su zango a Shilo, wadda take a ƙasar Kan'ana. 13 Sa'an nan taron jama'a suka aika wa mutanen Biliyaminu da suke a Dutsen Rimmon, cewa, yaƙi ya ƙare, sai salama. 14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka komo, aka ba su budurwan nan da aka bar su da rai aka kawo su Yabesh-gileyad, amma budurwan ba su ishe su ba. 15 Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra'ila. 16 Saboda haka dattawan taron jama'a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?” 17 Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra'ila, 18 amma fa ba za mu iya aurar musu da 'ya'yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da 'yarsa ga mutumin Biliyaminu la'ananne ne.” 19 Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.) 20 Suka umarci mutanen Biliyaminu suka ce, “Ku tafi ku yi kwanto a gonakin inabi, 21 ku lura, idan 'yan matan Shilo sun fito domin su yi rawa, sai ku fito daga cikin gonakin inabi, kowa ya kama daga cikin 'yan matan da ƙarfi, ya sami mata ke nan, ya tafi da ita a ƙasar Biliyaminu. 22 Sa'ad da iyayensu ko 'yan'uwansu sun kawo ƙara gare mu, za mu ce musu, ‘Ku bar mana su, muna roƙonku, domin ba daga wurin yaƙi muka kamo su domin su zama matanmu ba. Amma tun da ba ku ba mu su ba, ba ku da laifin ta da alkawari.’ ” 23 Haka kuwa mutanen Biliyaminu suka yi. Suka kama budurwai gwargwadon yawansu daga cikin masu rawa. Sa'an nan suka koma zuwa yaƙin ƙasarsu ta gādo. Suka sāke gina garuruwansu, suka zauna. 24 Hakanan kuma sauran mutanen Isra'ila suka tashi daga can. Kowa ya tafi wurin kabilarsa, da iyalinsa, da abin da ya mallaka. 25 A lokacin ba sarki a Isra'ila, sai kowa ya yi ta yin abin da ya ga dama.

Rut 1

Elimelek da Iyalinsa a Mowab

1 A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu. 2 Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yansu maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can. 3 Elimelek, mijin Na'omi, ya rasu, aka bar Na'omi da 'ya'yansu maza biyu. 4 Sai suka auri 'yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can, 5 sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.

Na'omi da Rut sun Komo Baitalami

6 Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta. 7 Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya. 8 Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan. 9 Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su. Sai suka fashe da kuka, 10 suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.” 11 Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku? 12 Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza, 13 za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.” 14 Suka sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata. 15 Na'omi ta ce wa Rut, “Kin ga, 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi 'yar'uwarki.” 16 Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna. 17 Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!” 18 Da Na'omi ta ga Rut ta ƙudura ta tafi tare da ita, sai ta ƙyale ta. 19 Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na'omi ce wannan?” 20 Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai. 21 Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?” 22 Haka Na'omi ta koma daga ƙasar Mowab tare da surukarta Rut, mutuniyar Mowab. Suka isa Baitalami a farkon kakar sha'ir.

Rut 2

Rut a Gonar Bo'aza

1 Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne. 2 Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.” Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.” 3 Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek. 4 Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.” Suka amsa, “Alaikun salamu.” 5 Sa'an nan Bo'aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “'Yar wace ce wannan?” 6 Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab. 7 Ita ce ta ce mana, ‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.’ Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai 'yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.” 8 Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana. 9 Ki kula da gonar da suke girbi, ki bi su. Ga shi, na riga na umarci barorina kada su dame ki. Sa'ad da kika ji ƙishirwa, sai ki tafi ki sha ruwa a tuluna, wanda barorin suka ɗebo.” 10 Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?” 11 Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā. 12 Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.” 13 Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.” 14 Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura. 15 Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta. 16 Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.” 17 Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu. 18 Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage. 19 Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.” Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo'aza.” 20 Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.” 21 Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, ‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.’ ” 22 Sa'an nan Na'omi ta ce wa Rut, “Madalla, 'yata, ki riƙa bin 'yan matan gidansa, kada ki tafi wata gona dabam.” 23 Sai ta riƙa bin 'yan matan gidan Bo'aza. Ta yi ta kala har aka gama girbin sha'ir da na alkama, tana zaune tare da surukarta, wato Na'omi.

Rut 3

Bo'aza da Rut a Masussuka

1 Wata rana, Na'omi ta ce wa Rut, “'Yata, ya kamata in nemar miki miji don ki sami gida inda za ki huta, ki ji daɗi. 2 Bo'aza wanda kika yi aiki da barorinsa danginmu ne. Ga shi, zai tafi sussukar sha'ir a masussuka da maraice. 3 Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha. 4 Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.” 5 Rut ta amsa, “Zan yi dukan abin da kika faɗa.” 6 Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata. 7 Sa'ad da Bo'aza ya ci ya sha yana cikin jin daɗi, sai ya je ya kwanta kusa da tsibin tsabar sha'ir. Sa'an nan Rut ta tafi a hankali, ta buɗe mayafin da ya rufa da shi wajen ƙafafunsa, ta kwanta a ciki. 8 Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa. 9 Ya ce, “Wace ce?” Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.” 10 Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba. 11 Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce. 12 Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni. 13 Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.” 14 Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar. 15 Bo'aza ya ce mata, “Kawo mayafinki, ki shimfiɗa shi.” Sai ta shimfiɗa mayafin, ya zuba mata sha'ir ya kusa garwa huɗu ya aza mata a kā. Sa'an nan ta koma gari. 16 Lokacin da ta zo wurin surukarta, sai surukarta ta ce mata, “'Yata, ina labari?” Sai ta faɗa mata dukan abin da mutumin ya faɗa mata. 17 Ta kuma ce, “Ga sha'ir da ya ba ni, gama ya ce, ‘Ba za ki koma wurin surukarki hannu wofi ba.’ ” 18 Sai surukarta ta ce, “Ki jira dai, 'yata, har ki ga yadda al'amarin zai zama, gama mutumin ba zai huta ba, sai ya daidaita al'amarin a yau.”

Rut 4

Bo'aza ya Auri Rut

1 Bo'aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo'aza ya ambata, ya iso. Bo'aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna. 2 Bo'aza ya kuma kirawo goma daga cikin dattawan gari, ya ce musu, “Ku zauna nan.” Suka kuwa zauna. 3 Sa'an nan ya ce wa dangin nan nasa na kusa, “Ga Na'omi wadda ta komo daga ƙasar Mowab, tana so ta sayar da gonar Elimelek danginmu. 4 Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.” 5 Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.” 6 Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.” 7 Wannan ita ce al'adar Isra'ilawa a dā a kan sha'anin fansa ko musaya, don tabbatar da al'amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra'ila. 8 Saboda haka a sa'ad da dangin nan mafi kusa ya ce wa Bo'aza, “Sai ka saye ta,” sai ya tuɓe takalminsa ya ba Bo'aza. 9 Sa'an nan Bo'aza ya ce wa dattawan da dukan jama'ar da suke wurin, “Yau ku ne shaidu, cewa, na sayi dukan abin da yake na Elimelek, da na Kiliyon, da na Malon daga hannun Na'omi. 10 Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na 'yan'uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.” 11 Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji ya sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, ya sa ka yi suna a cikin Baitalami, 12 gidanku kuma ya zama kamar gidan Feresa, wanda Tamar ta haifa wa Yahuza, saboda 'ya'yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace.” 13 Bo'aza kuwa ya auri Rut, ta zama matarsa. Ya kuma shiga wurinta, Ubangiji kuwa ya sa ta yi ciki, ta haifa masa ɗa. 14 Sai mata suka ce wa Na'omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra'ila. 15 Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki 'ya'ya maza bakwai, ita ta haife shi.” 16 Sa'an nan Na'omi ta ɗauki yaron ta rungume shi a ƙirjinta, ta zama mai renonsa. 17 Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.

Asalin Zuriyar Dawuda

18-22 Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa'an nan Yesse ya haifi Dawuda.

1 Sama’ila 1

Haihuwar Sama'ila

1 Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf. 2 Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta haihuwa. 3 A kowace shekara Elkana yakan haura daga garinsu zuwa Shilo domin ya miƙa wa Ubangiji Mai Runduna hadaya, ya kuma yi masa sujada. 'Ya'yan Eli, maza biyu, Hofni da Finehas, su ne firistoci na Ubangiji a can. 4 Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo. 5 Amma Hannatu, sai ya ba ta babban rabo guda ɗaya, gama yana ƙaunarta, amma Ubangiji ya kulle mahaifarta. 6 Kishiyarta takan tsokane ta don ta ji haushi, gama Ubangiji ya hana mata haihuwa. 7 Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci. 8 Elkana mijinta kuwa, ya ce mata, “Hannatu, me ya sa kike kuka? Me ya sa kike ƙin cin abinci? Me ya sa zuciyarki ta ɓaci? Ni ban fi 'ya'ya maza goma a gare ki ba?”

Hannatu da Eli

9 Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji. 10 Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu'a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji. 11 Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.” 12 Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a. 13 Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓunanta suke motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne, 14 ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.” 15 Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da ke baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata. 16 Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.” 17 Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.” 18 Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa'an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.

Haihuwar Sama'ila da Miƙawarsa

19 Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita. 20 Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.” 21 Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa'adinsa. 22 Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.” 23 Elkana ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi kyau, ki jira har ki yaye shi, Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Hannatu ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta. 24 Sa'ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami. 25 Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli. 26 Sa'an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji. 27 Na roƙi Ubangiji wannan yaro, Ubangiji kuwa ya biya mini bukatata da na roƙa a gare shi. 28 Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.” A can ya yi wa Ubangiji sujada.

1 Sama’ila 2

Waƙar Hannatu

1 Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce, “Ubangiji ya cika zuciyata da murna. Ina farin ciki da abin da ya yi. Ina yi wa maƙiyana dariya, Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni. 2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji, Babu wani mai kama da shi, Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu. 3 Kada ku ƙara yin magana ta girmankai, Ku daina maganganunku na fariya, Gama Ubangiji Allah shi ne masani, Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi. 4 An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji, Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi. 5 Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci, Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai, Wadda ta haifi 'ya'ya da yawa kuwa ta rasa su duka. 6 Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar, Yana kai mutane kabari, Ya kuma tā da su. 7 Yakan sa waɗansu mutane su zama matalauta, Waɗansu kuwa attajirai. Yakan ƙasƙantar da waɗansu, Ya kuma ɗaukaka waɗansu. 8 Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya. 9 “Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba. 10 Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.” 11 Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.

'Ya'yan Eli Maza

12 'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba. 13 Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman. 14 Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo. 15 Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.” 16 Idan mutumin ya ce, “To, bari a ƙona kitsen tukuna, sa'an nan ka ɗibi iyakar abin da kake bukata,” sai baran firist ɗin ya ce, “A'a, tilas ne ka ba ni yanzu, idan kuwa ba haka ba, zan ɗiba ƙarfi da yaji!” 17 Zunubin 'ya'yan nan maza na Eli ya yi yawa a gaban Ubangiji, gama sun wulakanta hadayar Ubangiji ƙwarai da gaske.

Sama'ila a Shilo

18 Yaron nan Sama'ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran. 19 A kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka 'yar rigar ado, ta kai masa a sa'ad da ita da mijinta sukan tafi miƙa hadayarsu ta shekara shekara. 20 Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.” Bayan wannan sai su koma gida. 21 Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi 'ya'ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama'ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.

Eli da 'Ya'yansa Maza

22 Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada. 23 Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa. 24 Haba 'ya'yana, ku bari! Jama'ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu. 25 Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?” Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.

Annabci a kan Gidan Eli

26 Yaron nan Sama'ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane. 27 Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa'ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir'auna a Masar, na bayyana kaina gare shi. 28 Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade. 29 Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila? 30 Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai. 31 Ga shi, lokaci yana zuwa da zan karkashe samari cikin iyalinka da danginka, har da ba za a sami wanda zai rayu har ya tsufa a gidanka ba. 32 Za ka kasance da damuwa da jin kishi, za ka duba dukan albarkun da zan sa wa Isra'ila, amma a gidanka ba za a taɓa samun wanda zai rayu har ya tsufa ba. 33 Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji. 34 Lokacin da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, za su mutu rana ɗaya wannan zai nuna maka abin da na faɗa sai ya cika. 35 Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina. 36 Dukan wanda ya ragu daga zuriyarka zai je wurin sarki ya roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa ya taimaki firistoci da aiki domin ya sami abin da zai ci.”

1 Sama’ila 3

Ubangiji ya Kira Sama'ila

1 Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba. 2 Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada. 3 Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama'ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake. 4 Ubangiji kuwa ya kira Sama'ila. Sama'ila ya ce, “Na'am.” 5 Ya sheƙa zuwa wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce masa, “Ban kira ka ba, koma ka kwanta.” Sai Sama'ila ya koma ya kwanta. 6 Ubangiji ya sāke kiran Sama'ila. Sama'ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.” 7 (Sama'ila dai bai san Ubangiji ba tukuna, gama Ubangiji bai riga ya fara magana da shi ba.) 8 Ubangiji kuma ya kira Sama'ila sau na uku. Sai kuma Sama'ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sa'an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron, 9 saboda haka Eli ya ce wa Sama'ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama'ila kuwa ya koma ya kwanta. 10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!” Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” 11 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Zan yi wa Isra'ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana. 12 A ranar zan cika abin da na faɗa game da Eli da iyalinsa daga farko har zuwa ƙarshe. 13 Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda 'ya'yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba. 14 Domin haka na faɗa da ƙarfi, cewa laifin gidan Eli ba za a yi kafararsa da sadaka, ko da hadaya ba har abada.” 15 Sama'ila ya kwanta har safiya, sa'an nan ya buɗe ƙofofi. Amma ya ji tsoron faɗa wa Eli wahayin. 16 Amma Eli ya kira shi, ya ce, “Ya ɗana, Sama'ila.” Sama'ila ya ce, “Ga ni.” 17 Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.” 18 Sama'ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.” 19 Sama'ila fa ya yi girma, Ubangiji yana tare da shi. Dukan maganarsa kuwa Ubangiji yana cika ta. 20 Dukan mutanen Isra'ila fa daga wannan kusurwar ƙasa zuwa wancan, sun tabbata Sama'ila annabin Ubangiji ne. 21 Ubangiji kuma ya yi ta bayyana a Shilo inda ya bayyana kansa ga Sama'ila, ya kuma yi magana da shi. Duk lokacin da Sama'ila ya yi magana dukan mutanen Isra'ila suna kasa kunne.

1 Sama’ila 4

Filistiyawa sun Ƙwace Akwatin Alkawari

1 A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek. 2 Filistiyawa suka shirya su fara yaƙi. Bayan yaƙi mai zafi, sai Filistiyawa suka ci Isra'ilawa, suka kashe mutane wajen dubu huɗu (4,000 ) a bakin dāga. 3 Da sojojin da suka ragu suka koma sansani, sai shugabannin Isra'ila suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa Filistiyawa suka ci mu yau? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo ya kasance tare da mu, ya cece mu daga ikon abokan gābanmu.” 4 Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin. 5 Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra'ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa. 6 Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin, 7 sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba. 8 Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada! 9 Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.” 10 Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra'ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000 ). 11 Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji, 'ya'yan Eli guda biyu, Hofni da Finehas kuma, aka kashe su.

Mutuwar Eli

12 Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa. 13 Sa'ad da ya iso, Eli yana zaune a kujerarsa a bakin hanya, yana jira, gama zuciyarsa ta damu saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shiga gari ya ba da labari, dukan garin ya ruɗe da kuka. 14 Sa'ad da Eli ya ji kukan, sai ya tambaya ya ce, “Me ake wa kuka?” Mutumin kuwa ya gaggauta zuwa wurin Eli ya faɗa masa. 15 (Eli yana da shekara tasa'in da takwas, ya kuwa makance ɗungum.) 16 Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.” Eli ya ce, “Dana, me ya faru?” 17 Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.” 18 Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba'in yana shugabancin Isra'ila.

Mutuwar Matar Finehas

19 Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu. 20 Tana bakin mutuwa, matan kuwa da suke taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba. 21 Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu. 22 Ta ce, “Daukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

1 Sama’ila 5

Akwatin Alkawarin Allah a wurin Filistiyawa

1 Sa'ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod. 2 Suka shigar da shi cikin haikalin gunkinsu, Dagon, suka ajiye shi kusa da gunkin. 3 Kashegari da safe sa'ad da mutanen Ashdod suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Suka ta da shi, suka ajiye a wurinsa. 4 Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu. 5 (Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba su taka dokin ƙafar Dagon a Ashdod ba har wa yau.)

6 Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su. 7 Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra'ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.” 8 Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?” Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can. 9 Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya. 10 Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra'ila don ya kashe dukanmu.” 11 Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani. 12 Marurai sun fito wa mutanen da ba su mutu ba, mutane suka yi kuka domin allolinsu su cece su.

1 Sama’ila 6

Filistiyawa sun Komar da Akwatin Alkawari

1 Akwatin alkawarin Ubangiji ya yi wata bakwai a ƙasar Filistiyawa. 2 Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.” 3 Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.” 4 Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?” Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku. 5 Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra'ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku. 6 Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra'ilawa su tafi. 7 Yanzu kuwa ku yi sabon keken shanu, ku sami shanun tatsa biyu waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba, ku ɗaura wa shanun keken, amma ku tsare 'yan maruƙansu a gida. 8 Sa'an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa'an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi. 9 Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.” 10 Suka yi yadda aka faɗa musu, suka sami shanun tatsa biyu, suka ɗaura musu karkiyar keken. Suka tsare 'yan maruƙansu a gida. 11 Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran. 12 Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh. 13 Mutanen Bet-shemesh kuwa suna cikin yankan alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga kai sai suka ga akwatin alkawari, sai suka yi murna matuƙa. 14 Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji. 15 Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana. 16 Sarakunan nan biyar na Filistiyawa sun ga an yi wannan, sa'an nan suka koma Ekron a ran nan. 17 Waɗannan su ne siffofin marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin yin hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron. 18 Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh. 19 Sai Ubangiji ya kashe mutum saba'in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.

Akwatin Alkawari a Kiriyat-yeyarim

20 Mutanen Bet-shemesh suka ce, “Wa ya isa ya tsaya a gaban Ubangiji, Allahn nan mai tsarki? A wurin wa zai tafi don ya rabu da mu?” 21 Sai suka aiki manzanni wurin mutanen Kiriyat-yeyarim, suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawari na Ubangiji, sai ku zo, ku ɗauka, ku tafi da shi.”

1 Sama’ila 7

1 Mutanen Kiriyat-yeyarim kuwa suka zo suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji suka kai shi gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa, Ele'azara, ya lura da akwatin alkawarin Ubangiji.

Sama'ila ya Shugabanci Isra'ila

2 Akwatin alkawarin Ubangiji ya daɗe a Kiriyat-yeyarim, ya kai har shekara ashirin. A wannan lokaci kuwa dukan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji don ya taimake su. 3 Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da bāƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.” 4 Isra'ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba'al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai. 5 Sama'ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra'ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu'a ga Ubangiji dominku.” 6 Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa. 7 Da Filistiyawa suka ji Isra'ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra'ilawa. Sa'ad da Isra'ilawa suka ji labari, sai suka tsorata, 8 suka ce wa Sama'ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.” 9 Sama'ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra'ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu'arsa. 10 A sa'ad da Sama'ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra'ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje. 11 Isra'ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar. 12 Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.” 13 Ta haka aka ci Filistiyawa. Daganan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra'ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama'ila. 14 Aka mayar wa Isra'ilawa garuruwan da Filistiyawa suka ƙwace musu, tun daga Ekron har zuwa Gat. Isra'ilawa kuma suka ƙwato dukan yankin ƙasarsu daga hannun Filistiyawa. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Isra'ilawa da Ƙan'aniyawa. 15 Sama'ila kuwa ya yi mulkin Isra'ilawa dukan kwanakin ransa. 16 A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari'a. 17 Sa'an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra'ilawa shari'a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.

1 Sama’ila 8

Isra'ilawa sun Roƙa a Naɗa musu Sarki

1 Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa maza su zama alƙalan Isra'ila. 2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abiya. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba. 3 Amma 'ya'yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya. 4 Dukan shugabannin Isra'ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama'ila a Rama, 5 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma 'ya'yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.” 6 Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji. 7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu. 8 Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka. 9 Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.” 10 Sama'ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. 11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa 'ya'yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman. 12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa. 13 Zai sa 'ya'yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye. 14 Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa. 15 Zai kuma karɓi ushirin hatsinku da na inabinku ya ba shugabannin fādarsa da sauran fādawansa. 16 Zai ƙwace bayinku mata da maza, da mafi kyau na shanunku da jakunanku, domin su riƙa yi masa aiki. 17 Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa. 18 A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.” 19 Amma mutane suka ƙi yin abin da Sama'ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu, 20 don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.” 21 Sa'ad da Sama'ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji. 22 Ubangiji kuwa ya ce wa Sama'ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.” Sai Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Kowa ya koma gida.”

1 Sama’ila 9

Aka Zaɓi Saul ya Zama Sarki

1 Akwai wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror, na iyalin Bekorat, dangin Afinya, shi attajiri ne. 2 Yana da wani ɗa, sunansa Saul, kyakkyawan saurayi ne. A cikin jama'ar Isra'ila ba wanda ya fi shi kyau, ya fi kowa tsayi a cikin Isra'ilawa duka. 3 Ana nan sai jakunan Kish, mahaifin Saul suka ɓace, Kish kuwa ya ce wa Saul, ɗansa, “Tashi, kai da ɗaya daga cikin barorin ku tafi, ku nemo jakunan.” 4 Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba. 5 Da suka kai ƙasar Zuf, sai Saul ya ce wa baransa da yake tare da shi, “Zo mu koma gida, kada babana ya bar damuwa a kan jakunan ya yi ta damuwa a kanmu.” 6 Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.” 7 Saul ya ce wa baransa, “Idan muka tafi, me za mu ba shi? Gama guzurin da yake tare da mu ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu ba shi.” 8 Baran kuma ya ce wa Saul, “Ina da 'yar azurfa tsaba da zan ba shi domin ya faɗa mana inda za mu same su.” 9 (A dā a Isra'ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.) 10 Sai Saul ya ce wa baransa, “Maganarka daidai ce, zo, mu tafi.” Suka kuwa tafi garin da mutumin Allah yake. 11 Sa'ad da suka haura zuwa garin, suka gamu da waɗansu 'yan mata za su ɗebo ruwa, suka ce musu, “Maigani yana nan?” 12 'Yan matan suka amsa, suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi nan ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu. 13 Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.” 14 Suka kuwa haura zuwa cikin garin. Da shigarsu suka ga Sama'ila ya nufo wajen da suke, za shi wurin da ake yin sujadar. 15 Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama'ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama'ila. 16 Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.” 17 Da Sama'ila ya ga Saul, sai Ubangiji ya ce masa, “To, ga mutumin da na faɗa maka! Shi ne wanda zai sarauci jama'ata.” 18 Sa'an nan Saul ya tafi wurin Sama'ila a ƙofar gari, ya tambaye shi, “Ina gidan maigani?” 19 Sama'ila ya amsa ya ce, “Ni ne maiganin, wuce gaba, mu tafi wurin yin sujada a kan tudu, gama yau dukanku za ku ci abinci tare da ni. Gobe da safe zan amsa muku dukan tambayoyinku, sa'an nan in sallame ku. 20 A kan zancen jakunanku da suka ɓace yau kwana uku ke nan da suka wuce, kada ka damu, gama an same su. Banda wannan ma, ga wa Isra'ilawa duka suke sa zuciya? Ba kai ba ne da gidan mahaifinka?” 21 Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra'ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?” 22 Sa'an nan Sama'ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata. 23 Sama'ila kuwa ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman nan da na ba ka, wanda na ce ka ajiye shi dabam.” 24 Sai mai dahuwa ya kawo cinya da gadon baya ya ajiye a gaban Saul. Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Sai ka ci naman da aka ajiye a gabanka, gama dominka aka ajiye shi don ka ci a wannan lokaci tare da waɗanda na gayyata.” A wannan rana kuwa Saul ya ci tare da Sama'ila. 25 Sa'ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene. 26 Ya kwanta, ya yi barci. Sama'ila ya Keɓe Saul ya Zama Sarki Da asuba, Sama'ila ya kira Saul ya ce, “Tashi, in sallame ka.” Saul kuwa ya tashi, shi da Sama'ila suka fita waje zuwa kan titi. 27 Sa'ad da suka kai bayan gari, sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Ka sa baranka ya yi gaba, kai ka tsaya nan tukuna domin in faɗa maka abin da Allah ya ce.”

1 Sama’ila 10

1 Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki 'yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama'arsa. 2 Yau, sa'ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’ 3 Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi. 4 Za su gaishe ka, su ba ka malmala biyu, kai kuwa sai ka karɓa. 5 Sa'ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa'ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa. 6 Sa'an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam. 7 Sa'ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai. 8 Za ka riga ni zuwa Gilgal inda zan zo in miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai, har in zo in sanar da kai abin da za ka yi.” 9 Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama'ila, sai Ubangiji ya ba shi sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar. 10 Sa'ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su. 11 Sa'ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?” 12 Sai wani mutumin da yake wurin ya ce, “Sauran fa, su ma, iyayensu annabawa ne?” Wannan kuwa ya zama karin magana, “Har Saul kuma yana cikin annabawa?” 13 Da ya gama rawa da sowa sai ya tafi wurin bagaden a kan tudu. 14 Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?” Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama'ila.” 15 Kawunsa kuma ya ce, “In ka yarda ka faɗa mini abin da Sama'ila ya faɗa maka.” 16 Saul kuwa ya ce wa kawunsa, “Ya faɗa mana a fili an gane jakunan.” Amma bai faɗa wa kawunsa zancen sarautar da Sama'ila ya faɗa masa ba.

An yi Na'am da Zaman Saul Sarki

17 Sama'ila kuwa ya tara mutanen Isra'ila a gaban Ubangiji a Mizfa. 18 Ya ce musu, “In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Ni na fito da Isra'ilawa daga Masar, na cece ku daga Masarawa da kuma daga hannun mulkokin da suka wahalshe ku. 19 Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ” 20 Sa'an nan Sama'ila ya ce wa kabilan Isra'ila su guso, kuri'a kuwa ta faɗa a kan kabilar Biliyaminu. 21 Sai kuma ya sa kabilar Biliyaminu ta guso iyali iyali, kuri'a kuwa ta faɗa a kan iyalin Matri. Sa'an nan kuma ya guso da iyalin Matri mutum mutum, kuri'a ta faɗa a kan Saul, ɗan Kish. Amma sa'ad da suka neme shi, ba a same shi ba. 22 Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?” Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.” 23 Sai suka sheƙa, suka fito da shi daga wurin da ya ɓuya, ya tsaya cikin mutane, ya fi kowa tsayi da misalin ƙafa guda. 24 Sama'ila ya ce wa dukan jama'a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama'a.” Jama'a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!” 25 Sa'an nan Sama'ila ya faɗa wa jama'a ka'idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa'an nan ya sallami jama'a duka kowa ya koma gidansa. 26 Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu. 27 Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.

1 Sama’ila 11

Saul ya Ci Ammonawa

1 Sai Nahash Ba'ammone ya kewaye Yabesh da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.” 2 Nahash Ba'ammone kuwa ya ce, “Zan ƙulla amana da ku a kan wannan sharaɗi, wato in ƙwaƙule idanunku na dama don ku zama abin raini ga Isra'ilawa.” 3 Dattawan Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ba mu zarafi kwana bakwai domin mu aika da manzanni a dukan ƙasar Isra'ila, idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, to, sai mu ba da kanmu gare ku.” 4 Da manzannin suka zo Gibeya inda Saul yake, suka ba mutane labarin abin da ya faru. Sai jama'a duka suka yi kuka. 5 Saul kuwa yana dawowa daga gona ke nan, tare da shanunsa na huɗa. Sai ya ce, “Me ya sami jama'a suke kuka haka?” Suka faɗa masa labarin mutanen Yabesh. 6 Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai. 7 Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko'ina a ƙasar Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama'ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!” Jama'a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda. 8 Sa'ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000 ) daga Isra'ila, dubu talatin (30,000 ) kuma daga Yahuza. 9 Suka faɗa wa manzannin da suka zo. “Ga abin da za ku faɗa wa mutanen Yabesh, ‘Gobe, kafin rana ta yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa'ad da manzannin suka je, suka faɗa wa mutanen Yabesh saƙon, suka yi murna. 10 Saboda haka mutanen Yabesh suka ce wa Nahash Ba'ammone, “Gobe za mu zo wurinku, ka yi mana yadda ka ga dama.” 11 Gari yana wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya. 12 Jama'ar Isra'ila kuwa suka ce wa Sama'ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.” 13 Amma Saul ya ce, “Ba wanda za a kashe a yau, gama Ubangiji ya yi wa Isra'ila ceto a yau.” 14 Sai Sama'ila ya ce wa jama'a, “Ku zo, mu tafi Gilgal a yi wankan sarautar a can.” 15 Jama'a duka kuwa suka nufi Gilgal, suka yi wa Saul wankan sarauta a gaban Ubangiji. Suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama. A can kuwa Saul tare da dukan mutanen Isra'ila suka yi murna ƙwarai.

1 Sama’ila 12

Sama'ila ya yi Jawabin Bankwana

1 Sama'ila ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ga shi, na kasa kunne gare ku, na kuwa yi muku abin da kuka ce mini, na naɗa muku sarki. 2 Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau. 3 To, ga ni nan, ku shaida a kaina a gaban Ubangiji da gaban wanda Ubangiji ya naɗa sarki. Takarkari ko jakin wa na ƙwace? Wa kuma na zalunta, ko na wulakanta? A wurin wa na karɓi hanci don in danne gaskiya? Sai ku shaida, ni kuwa zan mayar masa.” 4 Jama'a suka amsa, suka ce, “Ba ka zalunci kowa ba, ba ka wulakanta kowa ba, ba ka kuma yi wa kowa ƙwace ba.” 5 Sa'an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.” Jama'ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.” 6 Sama'ila kuma ya ce wa jama'a, “Ubangiji ne ya sa Musa da Haruna su fito da kakanninku daga ƙasar Masar. 7 Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku. 8 Sa'ad da Yakubu da 'ya'yansa suka tafi Masar, Masarawa suka wulakanta su, sai suka kai kuka ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiki Musa da Haruna waɗanda suka fito da kakanninku daga ƙasar Masar, suka kawo su su zauna a wannan wuri. 9 Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su. 10 Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.’ 11 Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya. 12 Amma da kuka ga Nahash Sarkin Ammonawa ya zo don ya yi yaƙi da ku, sai kuka ce mini, ‘Mu dai a yi mana sarki da zai sarauce mu,’ alhali kuwa Ubangiji Allahnku ne Sarkinku. 13 To, ga sarkin da kuka zaɓa nan, kuka roƙa. Ga shi, Ubangiji ya naɗa muku shi. 14 Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai. 15 Amma idan kun ƙi yin biyayya da maganar Ubangiji, kuka kuma karya umarnin Ubangiji, to, Ubangiji zai yi gāba da ku da sarkinku. 16 Yanzu fa ku tsaya shiru ku ga babban al'amarin da Ubangiji zai yi a idanunku. 17 Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.” 18 Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai. 19 Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.” 20 Sama'ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya. 21 Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani. 22 Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama'arsa. 23 Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu'a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwa da suke daidai. 24 Ku dai ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aminci, da zuciya ɗaya. Ku tuna da manyan al'amuran da ya yi muku. 25 Amma idan kuka ci gaba da aikata mugunta, za a shafe ku, ku da sarkinku.”

1 Sama’ila 13

Yaƙi da Filistiyawa

1 Saul yana da shekara talatin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara arba'in da biyu yana sarautar Isra'ila. 2 Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000 ) daga Isra'ila, dubu biyu (2,000 ) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000 ) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama'a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa. 3 Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko'ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi. 4 Isra'ilawa duka kuwa suka ji cewa Saul ya kashe shugaban yaƙi na Filistiyawa, da kuma, Isra'ilawa sun zama abin ƙi ga Filistiyawa, sai jama'a suka amsa kiran, suka tafi wurin Saul a Gilgal. 5 Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000 ), da mahayan dawakai dubu shida (6,000 ), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen. 6 Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai. 7 Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki. 8 Ya dakata kwana bakwai bisa ga adadin lokacin da Sama'ila ya ɗibar masa, amma Sama'ila bai iso Gilgal ba. Mutane suka yi ta watsewa suna barin Saul. 9 Sai Saul ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadayun salama.” Ya kuwa miƙa hadaya ta ƙonawa. 10 Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama'ila ya iso. Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi. 11 Sai Sama'ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash. 12 Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!” 13 Sama'ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra'ila har abada. 14 Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama'arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.” 15 Sama'ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne. 16 Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash. 17 Sai runduna uku na mahara suka fito daga sansanin Filistiyawa. Runduna ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal. 18 Runduna guda kuma ta nufi Bet-horon, guda kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji. 19 A wannan lokaci ba maƙeri a ƙasar Isra'ila duka, domin Filistiyawa sun hana Ibraniyawa su ƙera wa kansu takuba ko māsu. 20 Saboda haka kowane Ba'isra'ile yakan gangara zuwa Filistiyawa don ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa, 21 duk lokacin da za su koɗar bakin garma da fartanya sai su biya sulusin shekel ne, ladan koɗar gatari da shirya abin korar shanun noma sulusin shekel ne. 22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Saul da Jonatan. Amma Saul da ɗansa, Jonatan, suna da su. 23 Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.

1 Sama’ila 14

Karfin Zuciyar Jonatan

1 Wata rana Jonatan, ɗan Saul, ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye mu je sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai faɗa wa mahaifinsa ba. 2 Saul kuwa yana zaune a karkarar Gibeya a gindin itacen rumman a Migron. Mutum wajen ɗari shida suna tare da shi. 3 Ahiya ɗan Ahitub kuma, ɗan'uwan Ikabod, wato jikan Eli, firist na Ubangiji, yana Shilo, yana sāye da falmaran. Mutane kuma ba su sani ba, ashe Jonatan ya tafi wani wuri. 4 A tsakanin mashigin dutse inda Jonatan yake so ya bi zuwa sansanin Filistiyawa, akwai dutse mai tsayi a kowane gefe. Sunan ɗaya Bozer, ɗayan kuma Sene. 5 Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba. 6 Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.” 7 Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.” 8 Sa'an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su. 9 Idan sun ce mana, ‘Ku dakata har mu zo wurinku,’ to, sai mu tsaya cik, ba za mu tafi wurinsu ba. 10 Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.” 11 Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.” 12 Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.” Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra'ilawa.” 13 Sa'an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su. 14 A wannan karo na farko Jonatan da mai ɗaukar makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi kamar rabin kadada. 15 Dukan Filistiyawa da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa. 16 Da matsara na Saul a Gibeya ta Biliyaminu suka duba, sai ga taron Filistiyawa ya watse, kowa ya nufi wajensa, suna tafiya barkatai. 17 Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan. 18 Sai Saul ya ce wa Ahiya, “Kawo akwatin alkawarin Allah a nan.” Gama a wannan lokaci akwatin Allah yana hannun Isra'ilawa. 19 Sa'ad da Saul yake magana da firist ɗin, sai hargowa a sansanin Filistiyawa ta yi ta ƙaruwa, Saul kuwa ya ce wa firist, “Janye hannunka.” 20 Sa'an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa. 21 Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra'ilawan da suke tare da Saul da Jonatan. 22 Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su. 23 Haka Ubangiji ya ceci Isra'ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.

Abin da ya Faru bayan Yaƙin

24 A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci. dukan mutane suka shiga kurmi, sai ga zuma ko'ina, amma ba wanda ya lakata da yatsa ya sa a baka, domin mutane suna tsoron la'anar Saul. 27 Amma Jonatan bai ji barazanar da mahaifinsa ya yi wa jama'a ba, sai ya lakaci saƙar zuma da kan sandansa ya sa a hannu ya kai baka, sa'an nan idanunsa suka buɗe. 28 Sai wani daga cikin jama'a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke. 29 Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama'a! Dubi yadda na wartsake sa'ad da na ɗanɗana 'yar zuman nan. 30 Da yaya zai zama yau da a ce mutane sun ci abinci sosai daga ganimar abokan gābansu, wadda suka samo! Ai, da kisan da aka yi wa Filistiyawa ya fi haka.” 31 Filistiyawa sun sha ɗibga a wannan rana, tun daga Mikmash har zuwa Ayalon. Isra'ilawa suka tafke da yunwa. 32 Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yanyanka su, suka ci naman ɗanye. 33 Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.” Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.” 34 Sa'an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama'a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin. 35 Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji. 36 Sa'an nan Saul ya ce, “Mu tafi, mu fallasa Filistiyawa da dare har wayewar gari, kada ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira.” Sai suka ce masa, “Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau.” Amma firist ɗin ya ce, “Bari mu yi tambaya ga Allah.” 37 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra'ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba. 38 Sai Saul ya ce wa shugabanni, “Ku zo nan dukanku don mu bincike, mu san zunubin da aka yi a yau. 39 Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome. 40 Ya kuma ce, “Dukanku ku tsaya waje ɗaya, ni kuma da Jonatan, ɗana, mu tsaya waje ɗaya.” Sai jama'ar suka ce wa Saul, “Ka yi abin da ya yi maka kyau.” 41 Sa'an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama'a kuwa suka kuɓuta. 42 Sa'an nan Saul ya ce, “A jefa kuri'a tsakanina da ɗana Jonatan.” Kuri'a kuwa ta fāɗa a kan Jonatan. 43 Sa'an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana 'yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.” 44 Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.” 45 Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba. 46 Sa'an nan Saul ya komo daga runtumar Filistiyawa, suka koma yankin ƙasarsu.

Mulkin Saul da Iyalinsa

47 Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara. 48 Ya yi aikin jaruntaka, ya bugi Amalekawa, ya ceci Isra'ilawa daga hannun dukan waɗanda suka taso musu. 49 'Ya'yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da 'ya'ya mata biyu, Merab, 'yar fari, da Mikal. 50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam 'yar Ahimawaz. Sunan shugaban rundunansa kuwa Abner ne, ɗan Ner, kawunsa. 51 Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, 'ya'yan Abiyel ne. 52 Saul ya yi ta yaƙi mai zafi da Filistiyawa dukan zamanin da yake sarauta. Idan Saul ya ga ƙaƙƙarfan mutum, ko jarumi, sai ya sa shi cikin sojansa.

1 Sama’ila 15

Yaƙi da Amalekawa

1 Sama'ila ya ce wa Saul, “Ubangiji ya aike ni in zuba maka man keɓewa don ka zama sarkin mutanensa, Isra'ila. Yanzu sai ka yi biyayya da maganar Ubangiji. 2 Zai hukunta Amalekawa saboda sun yi gāba da Isra'ilawa lokacin da suke tahowa daga Masar. 3 Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.” 4 Saul kuwa ya kira mutanen da ya ƙidaya a Telem, sojoji dubu ɗari biyu (200,000 ) daga Isra'ila, da dubu goma (10,000 ) daga Yahuza. 5 Sa'an nan Saul ya zo birnin Amalekawa ya yi kwanto a cikin kwari. 6 Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa. 7 Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar, 8 ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi. 9 Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.

An Ƙi Saul da Zaman Sarauta

10-11 Sai Ubangiji ya yi magana da Sama'ila ya ce, “Na yi baƙin ciki da na sa Saul ya zama sarki, gama ya rabu da ni, ya yi rashin biyayya ga umarnaina,” Sama'ila kuwa ya yi fushi, ya yi ta roƙo ga Ubangiji dukan dare. 12 Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal. 13 Sai Sama'ila ya tafi wurin Saul, Saul kuwa ya gaishe shi, ya ce, “Ubangiji ya sa maka albarka, Sama'ila, na yi biyayya ga umarninsa.” 14 Sama'ila ya ce masa, “To, ina baicin wannan kukan shanu da na tumaki da nake ji?” 15 Saul kuwa ya ce, “Ai, mutanena ne suka kawo su daga Amalekawa. Gama sun bar mafi kyau na tumaki, da na shanu domin su miƙa su sadaka ga Ubangiji Allahnka. Mun hallaka sauran ƙaƙaf.” 16 Sa'an nan Sama'ila ya ce wa Saul, “Dakata, in faɗa maka abin da Ubangiji ya faɗa mini a daren jiya.” Sai Saul ya ce, “Faɗa mini.” 17 Sama'ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra'ila ba? Ubangiji ya sa ka zama Sarkin Isra'ila, 18 ya kuma umarce ka ka tafi ka hallakar da waɗannan mugayen mutane, wato Amalekawa. Ya faɗa maka ka yi yaƙi, har ka hallaka su ƙaƙaf, kada ka rage ko guda ɗaya. 19 Me ya sa ba ka yi biyayya da shi ba? Don me ka fāɗa wason ganima, ka yi abin da Ubangiji ba ya so?” 20 Sai Saul ya amsa wa Sama'ila, ya ce, “Na yi wa Ubangiji biyayya, gama na tafi kamar yadda ya faɗa mini, na kamo sarki Agag, na kuma hallaka Amalekawa ƙaƙaf. 21 Amma mutanena ba su kashe tumaki da shanu mafi kyau ba, amma suka kawo su domin sadaka ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.” 22 Sai Sama'ila ya ce, “Me Ubangiji ya fi so? Biyayya, ko kuwa sadakoki da hadayu? Ya fi kyau a yi masa biyayya, da a miƙa masa hadayar tumaki mafi kyau. 23 Gama tayarwa kamar zunubin bokanci take. Taurinkai kuma kamar bautar gumaka yake. Kamar yadda ka ƙi umarnin Ubangiji, hakanan shi ma ya ƙi ka da zama sarki.” 24 Sa'an nan Saul ya ce wa Sama'ila, “Na yi zunubi, na yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da kuma koyarwarsa. Na ji tsoron mutanena, na kuwa biye wa abin da suke so. 25 Yanzu fa, ina roƙonka ka gafarta mini zunubina, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji sujada.” 26 Sama'ila ya ce wa Saul, “Ba zan tafi tare da kai ba, gama ka ƙi umarnin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ƙi ka da zama Sarkin Isra'ila.” 27 Sa'an nan Sama'ila ya juya zai tafi, amma Saul ya kama alkyabbar Sama'ila, sai ta yage. 28 Sai Sama'ila ya ce masa, “Yau Ubangiji ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka. Ya ba da ita ga maƙwabcinka wanda ya fi ka. 29 Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.” 30 Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.” 31 Sama'ila kuwa ya tafi tare da Saul, Saul kuwa ya yi wa Ubangiji sujada. 32 Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Ku kawo mini Agag Sarkin Amalekawa.” Sai Agag ya taho wurinsa, yana rawar jiki don tsoro, yana cewa a ransa, “Hakika, azabar mutuwa ta fi ɗaci.” 33 Sama'ila ya ce masa, “Kamar yadda takobinka ya mai da mata marasa 'ya'ya, haka za a mai da mahaifiyarka ta zama marar ɗa.” Sai Sama'ila ya sassare Agag gunduwa gunduwa a gaban bagade a Gilgal. 34 Sa'an nan Sama'ila ya tafi Rama, Saul kuwa ya tafi gidansa a Gibeya. 35 Daga ran nan Sama'ila bai ƙara saduwa da sarki Saul ba, har rasuwar Sama'ila, amma ya ji juyayin Saul. Ubangiji kuwa bai ji daɗi da ya sa Saul ya zama Sarkin Isra'ila ba.

1 Sama’ila 16

An Keɓe Dawuda ya Zama Sarki

1 Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.” 2 Sama'ila kuwa ya ce, “Ƙaƙa zan yi wannan? Gama idan Saul ya ji zai kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce, “Ka tafi da ɗan maraƙi, ka ce, ka zo ne ka miƙa wa Ubangiji hadaya. 3 Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.” 4 Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?” 5 Ya ce, “I, lafiya lau. Na zo ne in miƙa wa Ubangiji hadaya, sai ku tsarkake kanku, ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da 'ya'yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar. 6 Da suka isa wurin hadayar, Sama'ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa. 7 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.” 8 Sa'an nan Yesse ya kira Abinadab ya wuce a gaban Sama'ila. Amma Sama'ila ya ce, “Ubangiji kuma bai zaɓi wannan ba.” 9 Sa'an nan Yesse ya sa Shimeya ya zo. Sama'ila kuma ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ba.” 10 Ta haka Yesse ya sa 'ya'yansa maza, su bakwai, suka zo a gaban Sama'ila. Sama'ila kuwa ya ce wa Yesse, “Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.” 11 Sai ya tambayi Yesse, “Ko kana da sauran waɗansu 'ya'ya maza?” Yesse ya ce, “Da sauran autan, ga shi kuma, yana wurin kiwon tumaki.” Sama'ila ya ce masa, “Sai ka aika a taho da shi, gama ba zan koma ba, sai ya zo.” 12 Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.” 13 Sama'ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban 'yan'uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama'ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.

Dawuda ya Kaɗa wa Saul Garaya

14 Yanzu kuwa Ruhun Ubangiji ya rabu da Saul, sai Ubangiji ya sa mugun ruhu ya azabtar da shi. 15 Barorin Saul kuwa suka ce masa, “To, ga shi yanzu, Ubangiji ya sa mugun ruhu yana azabtar da kai. 16 Saboda haka muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo mutum gwanin kiɗan garaya, domin sa'ad da mugun ruhun nan da Allah ya sa maka, ya hau kanka, sai ya kaɗa maka garayar don ya sauka.” 17 Saul kuwa ya ce wa barorinsa. “To, sai ku samo mini mutum gwanin kiɗa, ku kawo mini shi.” 18 Sai wani daga cikin samarin ya amsa, ya ce, “Na san wani ɗan Yesse mutumin Baitalami. Shi gwanin kiɗan garaya ne, jarumi ne kuma, mayaƙi, mai lafazi, kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.” 19 Sai Saul ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse, ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka, Dawuda, mai kiwon tumakinka.” 20 Yesse kuwa ya yi wa jaki labtu da abinci, da salkar ruwan inabi, da ɗan akuya, ya aiko Dawuda ɗansa, ya kai wa Saul. 21 Sa'an nan Dawuda ya zo wurin Saul, ya kama aiki. Saul kuwa ya ƙaunaci Dawuda ƙwarai, har Dawuda ya zama mai ɗaukar masa makamai. 22 Sa'an nan Saul ya aika wa Yesse cewa, “Ina so Dawuda. Ka bar shi ya zauna nan ya yi mini aiki.” 23 Tun daga ran nan zuwa gaba, a duk lokacin da mugun ruhun nan da Allah ya sa masa ya hau kansa, sai Dawuda ya ɗauki garaya, ya kaɗa masa. Sa'an nan mugun ruhu ya sauka, sai Saul ya wartsake.

1 Sama’ila 17

Goliyat yana Cakunar Isra'ilawa

1 Sai Filistiyawa suka tattaru a Soko ta Yahuza, suka kafa sansani a tsakanin Soko da Azeka, a Efes-dammim. 2 Saul kuma da mutanen Isra'ila suka tattaru, suka kafa sansani a kwarin Ila, suka jā dāga don su yi yaƙi da Filistiyawa. 3 Filistiyawa suka jeru a tudu guda, Isra'ilawa kuwa a ɗaya tudun. Kwari yana tsakaninsu. 4 Akwai wani jarumi, sunansa Goliyat, ya fito daga sansanin Filistiyawa. Tsayinsa kamu shida da rabi. 5 Yana sa kwalkwali na tagulla a kansa, yana kuma saye da sulke na tagulla wanda nauyinsa ya fi shekel dubu biyar (5,000 ). 6 Ya sa safa ta tagulla a ƙafafunsa, yana kuma da māshi na tagulla saɓe a kafaɗarsa. 7 Gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa. Nauyin ruwan māshinsa na baƙin ƙarfe shekel ɗari shida ne. Mai ɗaukar masa garkuwa yana tafe a gabansa. 8 Goliyat ya ta da murya da ƙarfi, ya yi kira ga rundunar Isra'ila, ya ce, “Don me kuka fito ku jā dāgar yaƙi? Ai, ni Bafiliste ne, ku kuwa barorin Saul! Ku zaɓi mutum guda daga cikinku ya gangaro nan wurina. 9 Idan ya iya yaƙi da ni, ya kashe ni, to sai mu zama bayinku, amma idan na fi ƙarfinsa, na kashe shi, sai ku zama bayinmu, ku bauta mana.” 10 Ya ƙara da cewa, “Na raina rundunan Isra'ila yau. Ku ba ni mutumin da zan yi yaƙi da shi.” 11 Sa'ad da Saul da dukan Isra'ilawa suka ji maganganun da Bafilisten nan yake faɗa, sai suka karaya, suka tsorata ƙwarai.

Dawuda a Sansanin Saul

12 Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul. 13 Manyan 'ya'yansa maza uku sun tafi yaƙi tare da Saul. Sunan babban ɗan, Eliyab, na biye da shi kuma, Abinadab, na ukun kuwa Shimeya. 14 Dawuda shi ne auta. Sa'ad da manyan 'yan'uwansa uku suka tafi tare da Saul wurin yaƙi, 15 Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa. 16 Goliyat yana ta tsokanar Isra'ilawa safe da maraice, har kwana arba'in. 17 Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa 'yan'uwanka da sauri a sansanin. 18 Ga waɗannan dunƙulen cuku goma, ka kai wa shugaba na mutum dubu. Ka dubo lafiyar 'yan'uwanka, ka kawo mini labari. 19 Da Saul, da 'yan'uwanka, da dukan mazajen Isra'ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.” 20 Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi. 21 Isra'ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna. 22 Sai Dawuda ya bar abin da ya kawo a wurin mai jiran kaya, ya sheƙa zuwa bakin dāga domin ya gai da 'yan'uwansa. 23 Sa'ad da yake magana da su, sai ga Goliyat, jarumin Filistiyawa na Gat, ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya yi maganganu irin na dā. Dawuda kuwa ya ji. 24 Sa'ad da dukan mazajen Isra'ila suka ga mutumin, suka guje masa saboda tsoro. 25 Suka ce, “Kun ga mutumin nan da ya fito? Lalle ya fito ne don ya nuna mana raini. Duk wanda ya kashe shi, sarki zai arzutar da shi, ya ba shi 'yarsa aure, ya kuma 'yantar da gidan mahaifinsa cikin Isra'ila.” 26 Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?” 27 Mutane suka maimaita masa abin da sarki ya faɗa. 28 Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa 'yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.” 29 Dawuda kuwa ya ce, “To, me kuma na yi, ba tambaya kawai na yi ba?” 30 Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā. 31 Sa'ad da waɗansu suka ji maganar da Dawuda ya yi, sai suka faɗa wa Saul. Shi kuwa ya aika a kira Dawuda. 32 Dawuda kuwa ya ce wa Saul, “Kada zuciyar kowa ta karai saboda wannan mutum, baranka zai tafi ya yi yaƙi da shi.” 33 Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.” 34 Amma Dawuda ya ce wa Saul, “Ai, baranka makiyayin tumakin mahaifinsa ne, sa'ad da zaki ko beyar ya zo ya kama ɗan rago daga garken, 35 nakan bi shi, in fāɗa masa, in ƙwato ɗan ragon daga bakinsa. Idan ya tasar mini da faɗa, sai in kama reronsa, in buge shi, in kashe shi. 36 Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai. 37 Ubangiji wanda ya cece ni daga dāgin zaki da na beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafiliste.” Sa'an nan Saul ya ce wa Dawuda, “Tafi, Ubangiji ya taimake ka.” 38 Ya sa wa Dawuda kayan yaƙinsa, ya sa masa kwalkwalin tagulla a kansa, ya kuma sa masa sulke. 39 Da Dawuda ya sa kayan yaƙin, ya rataya takobi, ya fara tafiya, sai ya ji ba zai iya ba, domin bai saba da su ba. Sai ya ce wa Saul, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, gama ban saba da su ba.” Ya kuwa tuɓe su. 40 Sa'an nan ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya zuba a angararsa. Ya kuma riƙe majajjawarsa, ya tafi, ya fuskanci Bafilisten.

Dawuda ya Kashe Goliyat

41 Bafilisten kuma ya nufo Dawuda, mai ɗaukar masa garkuwa yana gabansa. 42 Sa'ad da ya ga Dawuda, sai ya raine shi, gama Dawuda saurayi ne kawai, kyakkyawa. 43 Ya ce wa Dawuda, “Ni kare ne da za ka nufo da sanduna?” Ya zagi Dawuda da sunan allolinsu na Filistiyawa. 44 Ya kuma ce wa Dawuda, “Ya ka nan, ni kuwa in ba da namanka ga tsuntsayen sama da namomin jeji.” 45 Dawuda kuwa ya ce masa, “Kai, kana nufo ni da takobi, da māshi, da k�re, amma ni ina zuwa wurinka da sunan Ubangiji Mai Runduna, Allah na sojojin Isra'ila, wanda ka raina. 46 A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila. 47 Taron jama'ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da māshi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.” 48 Goliyat kuwa ya fara gusowa ya gamu da Dawuda, sai Dawuda ya sheƙa zuwa bakin dāgar yaƙin don ya gamu da shi. 49 Sa'an nan Dawuda ya ɗauko dutse daga cikin angararsa, ya wurga, dutsen kuwa ya sami Goliyat a goshi, har ya lume. Goliyat kuwa ya faɗi rubda ciki. 50 Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba. 51 Sa'an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu. 52 Mutanen Isra'ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron. 53 Da Isra'ilawa suka komo daga runtumar Filistiyawa, suka wāshe sansanin Filistiyawa. 54 Dawuda kuwa ya ɗauki kan Bafilisten ya kawo Urushalima, amma ya ajiye kayan yaƙin Bafilisten a alfarwarsa.

An Kai Dawuda wurin Saul

55 Sa'ad da Saul ya ga Dawuda ya tafi ya yi yaƙi da Goliyat, ya ce wa Abner, sarkin yaƙinsa, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya amsa, ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, ban sani ba.” 56 Sai ya ce, “Ka tambaya mini, wane ne uban saurayin nan.” 57 Da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai Abner ya kai shi wurin Saul, Dawuda yana ɗauke da kan Bafilisten. 58 Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?” Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”

1 Sama’ila 18

Alkawarin Jonatan da Dawuda

1 Da Dawuda ya gama magana da Saul, sai zuciyar Jonatan ta saje da ran Dawuda. Jonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar kansa. 2 Daga ran nan Saul ya riƙe Dawuda, bai bari Dawuda ya koma gidan mahaifinsa ba. 3 Jonatan kuma ya yi dawwamammen alkawari da Dawuda, domin shi, wato Jonatan, yana ƙaunar Dawuda kamar kansa. 4 Sai ya tuɓe rigarsa ya ba Dawuda, ya kuma ba shi jabbarsa, da takobinsa, da bakansa, da abin ɗamararsa. 5 Duk inda Saul ya aiki Dawuda, sai ya tafi, ya kuma ci nasara. Saboda haka Saul ya maishe shi shugaban sojoji. Dukan jama'a da barorin Saul kuma suka ji daɗi.

Saul yana Kishin Dawuda

6 Sa'ad da sojoji suke komowa gida, bayan da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai mata daga kowane gari na Isra'ila suka fito domin su taryi sarki Saul. Suna raira waƙar farin ciki, suna rawa, suna kaɗa kuwaru da molaye. 7 Suka raira waƙa, suna cewa, “Saul ya kashe dubbai, amma Dawuda ya kashe dubun dubbai.” 8 Wannan waƙa ta ba Saul haushi, ya ce, “Sun ba Dawuda dubun dubbai, amma dubbai kawai suka ba ni, me kuma ya rage masa, ai, sai sarauta.” 9 Tun daga wannan rana Saul ya fara kishin Dawuda. 10 Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da māshi. 11 Yana cewa a ransa, “Zan nashe shi in kafe shi da bango.” Sau biyu yana cakar Dawuda da māshi, amma Dawuda ya goce. 12 Saul ya ji tsoron Dawuda, gama Ubangiji yana tare da Dawuda, amma ya rabu da Saul. 13 Saboda haka Saul bai yarda Dawuda ya zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban dubu. Shi kuwa ya riƙa bi da su cikin kai da kawowa. 14 Dawuda kuwa ya yi ta yin nasara cikin ayyukansa duka, domin Ubangiji yana tare da shi. 15 Da Saul ya ga Dawuda yana yin nasara, sai ya ƙara jin tsoronsa. 16 Dukan mutanen Isra'ila da na Yahuza suka ƙaunaci Dawuda, domin yana kai da kawowa a cikinsu.

Dawuda ya Auri 'Yar Saul

17 Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar 'yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.) 18 Dawuda, ya ce wa Saul, “Wane ni ko iyalin mahaifina a cikin Isra'ila, har da zan zama surukin sarki?” 19 Amma sa'ad da lokaci ya yi da za a ba Dawuda Merab, 'yar Saul, ya aura, sai aka aurar da ita ga Adriyel, mutumin Abel-mehola. 20 Mikal, 'yar Saul kuwa, ta ƙaunaci Dawuda, sai aka faɗa wa Saul, shi kuwa ya yarda da haka. 21 Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.” 22 Sai Saul ya umarci fādawansa, ya ce, “Ku yi magana da Dawuda a ɓoye, ku ce masa, ‘Ga shi, sarki yana jin daɗinka, dukan fādawansa kuma suna ƙaunarka, yanzu sai ka zama surukin sarki.’ ” 23 Fādawan Saul kuwa suka faɗa wa Dawuda wannan magana. Sai Dawuda ya ce, “Zama surukin sarki ƙaramin abu ne a ganinku? Ga shi, ni talaka ne wanda ba sananne ba.” 24 Fādawan suka faɗa wa Saul abin da Dawuda ya faɗa. 25 Saul kuma ya ce, “Haka za ku faɗa wa Dawuda, ‘Sarki ba ya so ka ba da sadaki don auren, sai dai ka ba da loɓar Filistiyawa guda ɗari, domin ka ɗauki fansa a kan maƙiyan sarki.’ ” (Saul dai yana so Filistiyawa su kashe Dawuda kawai.) fādawan suka faɗa wa Dawuda abin da Saul ya ce, sai Dawuda ya ji daɗi ƙwarai ya zama surukin sarki. Kafin lokacin da aka yanka masa ya yi, sai Dawuda ya tashi, ya tafi tare da mutanensa, suka kashe Filistiyawa ɗari biyu. Ya kawo loɓarsu duka, aka ba sarki, domin ya zama surukin sarki. Saul kuwa ya aurar da Mikal, 'yarsa, ga Dawuda. 28-29 Da Saul ya gane lalle Ubangiji yana tare da Dawuda, Mikal 'yarsa kuma tana ƙaunar Dawuda, sai ya ƙara jin tsoronsa, ya maishe shi maƙiyinsa na din din din. 30 Sarakunan Filistiyawa sukan zo da yaƙi. Idan sun zo, sai Dawuda ya yi nasara da su fiye da sauran shugabannin yaƙi na Saul. Wannan ya sa ya yi suna.

1 Sama’ila 19

Saul ya Tsananta wa Dawuda

1 Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai. 2 Jonatan ya faɗa wa Dawuda ya ce, “Saul, mahaifina, yana so ya kashe ka, domin haka sai ka lura da kanka da safe, ka ɓuya a wani lungu. 3 Ni kuwa zan tafi in tsaya kusa da mahaifina a saura inda ka ɓuya, zan yi masa magana a kanka, abin da ya faru, zan sanar da kai.” 4 Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne. 5 Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?” 6 Saul kuwa ya saurari maganar Jonatan, ya rantse masa ya ce, “Hakika, ba za a kashe shi ba.” 7 Jonatan kuwa ya kira Dawuda ya faɗa masa dukan abin da Saul ya faɗa. Ya kuma kai Dawuda gaban Saul, ya zauna tare da shi kamar dā. 8 Aka kuma yi yaƙi da Filistiyawa, Dawuda kuwa ya tafi ya yi yaƙi da su, ya kashe su da yawa, sai suka gudu a gabansa. 9 Ubangiji kuma ya sa mugun ruhu ya sauko kan Saul sa'ad da yake zaune a gidansa, da māshi a hannunsa. Dawuda kuma yana ta kaɗa masa garaya. 10 Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, māshin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere. 11 A daren nan Saul ya aiki manzanni su je gidan Dawuda don su yi fakonsa, su kashe shi da safe. Amma Mikal, matar Dawuda, ta faɗa masa cewa, “Idan ba ka gudu da daren nan ba, gobe za a kashe ka.” 12 Sai ta zurarar da Dawuda ta taga, ya gudu, ya tsere. 13 Mikal kuwa ta ɗauki kan gida ta kwantar da shi a gado, ta kuma sa masa matashin kai na gashin awaki, sa'an nan ta lulluɓe shi da mayafi. 14 Sa'ad da manzannin Saul suka zo don su kama Dawuda, sai ta ce musu, “Ba shi da lafiya.” 15 Saul kuma ya sāke aiken manzannin su tafi su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi nan wurina a kan gadonsa don in kashe shi.” 16 Da manzannin suka tafi, sai suka tarar da kan gida a gadon, da matashin kai na gashin awaki wajen kansa. 17 Saul kuwa ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya tsere?” Ta ce wa Saul, “Ya ce mini, idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni.” 18 Dawuda ya gudu, ya tsere zuwa wurin Sama'ila a Rama, ya faɗa masa dukan abin da Saul ya yi masa. Shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot. 19 Aka faɗa wa Saul cewa, “Dawuda yana a Nayot ta Rama.” 20 Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci. 21 Aka faɗa wa Saul, sai ya sāke aiken waɗansu, su kuma suka shiga yin annabci. Ya kuma sāke aiken manzanni aji na uku, su kuma suka shiga yin annabci. 22 Saul kuma ya tafu Rama da kansa. Da ya kai babbar rijiyar da take a Seku, sai ya tambayi inda Sama'ila da Dawuda suke. Wani ya ce masa, “Suna Nayot ta Rama.” 23 Sai ya tashi daga can zuwa Nayot ta Rama. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kansa, sai shi kuma ya shiga yin annabci har ya kai Nayot ta Rama, 24 ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”

1 Sama’ila 20

Abutar Dawuda da Jonatan

1 Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?” 2 Jonatan ya ce masa, “Allah ya sawwaƙa, ba za a kashe ka ba, gama babana yakan faɗa mini kome, ƙarami ko babba, kafin ya aikata. To, me zai sa babana ya ɓoye mini wannan? Wannan ba haka yake ba.” 3 Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!” 4 Sai Jonatan ya ce wa Dawuda, “Duk abin da ka ce, zan yi maka.” 5 Dawuda kuwa ya ce masa, “Ga shi, gobe ce amaryar wata, dole ne in zauna tare da sarki a teburinsa. Ka bar ni in tafi in ɓuya a saura har kwana uku. 6 Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu. 7 Idan ka ji ya ce, ‘Da kyau,’ to, baranka zai tsira ke nan, amma idan ya husata, to, sai ka sani yana niyyar kashe ni ke nan, 8 kai kuwa ka nuna mini alheri, gama ka yi mini alkawari mai ƙarfi. Amma idan ina da laifi, sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bar mahaifinka ya kashe ni?” 9 Jonatan ya masa ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Da na sani babana yana da nufi ya yi maka mugunta, ai, da na faɗa maka.” 10 Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?” 11 Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura. 12 Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka. 13 Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina. 14 Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba. 15 Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.” 16 Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda. 17 Sai Jonatan ya sa Dawuda ya yi masa alkawari zai ƙaunace shi, gama shi kansa yana ƙaunar Dawuda ƙwarai kamar yadda yake ƙaunar kansa. 18 Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Gobe ce amaryar wata, ba kowa a wurin zamanka ke nan da yake ba za ka zo ba. 19 A rana ta uku za a gane ba ka nan sosai, to, sai ka tafi, ka ɓuya a wurin da ka ɓuya a waccan rana. Ka zauna kusa da tarin duwatsu. 20 Zan harba kibau guda uku kusa da tarin duwatsun, kamar ina harbin wani abu ne. 21 Zan aiki yaro ya tafi ya nemo kiban. Idan na ce masa, ‘Duba, ga kiban kusa da kai, ka kawo su,’ To, sai ka fito, ka zo, wato lalle kome lafiya ke nan, ba abin da zai cuce ka. 22 Amma idan na ce wa yaron, ‘Duba, kiban suna a gabanka,’ To, ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka, ka tafi. 23 A kan alkawarin da muka yi, ni da kai kuwa, Ubangiji shi ne shaida a tsakaninmu har abada.” 24 Dawuda ya ɓuya a saura. A ranar amaryar wata kuwa sarki ya zauna domin cin abinci. 25 Ya zauna inda ya saba zama kusa da bango. Jonatan ya zauna daura da shi, Abner kuwa ya zauna kusa da Saul, amma ba kowa a wurin zaman Dawuda. 26 Saul kuwa bai ce kome a wannan rana ba, gama ya zaci wani abu ya sami Dawuda, kila ba shi da tsarki, lalle kam Dawuda ba shi da tsarki. 27 Amma kashegari, wato rana ta biyu ta amaryar watan, ba kowa kuma wurin zaman Dawuda, sai Saul ya ce wa Jonatan, ɗansa, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo wurin cin abinci ba, jiya da yau?” 28 Jonatan ya ce masa, “Dawuda ya roƙe ni da naciya in bar shi ya tafi Baitalami. 29 Ya ce mini, ‘In ka yarda ka bar ni in tafi, gama a gidanmu ana ba da sadaka a gari, ɗan'uwana kuwa ya umarce ni in je. Idan na sami tagomashi a wurinka ka bar ni in tafi in ga 'yan'uwana.’ Abin da ya sa bai zo ba ke nan.” 30 Sai Saul ya husata da Jonatan, ya ce masa, “Kai yaron banza ne, mai ƙin ji, ai, na sani kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulakantar da kanka da mahaifinka. 31 Muddin ɗan Yesse na da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za ta kahu ba. Yanzu sai ka je ka taho mini da shi. Dole kashe shi za a yi.” 32 Jonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa za a kashe shi? Me ya yi?” 33 Sai Saul ya jefe shi da māshi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda. 34 Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi. 35 Da safe Jonatan ya tafi saura tare da wani yaro daidai lokacin da ya shirya da Dawuda. 36 Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi. 37 Da yaron ya kai inda Jonatan ya harba kibiyar, sai ya ce masa, “Ba kibiyar tana a gaban ka ba?” 38 Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa. 39 Amma yaron bai san abin da ake nufi ba. Jonatan da Dawuda kaɗai suka san abin da ake ciki. 40 Sa'an nan Jonatan ya ba yaron makamansa, ya ce masa, “Kai su gari.” 41 Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi. 42 Jonatan ya ce wa Dawuda, “Sai ka tafi lafiya, tun da yake mun riga mun rantse wa juna da sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji zai zama shaida tsakanina da kai, da tsakanin zuriyarmu har abada.’ ” Dawuda ya yi tafiyarsa, Jonatan kuwa ya koma gari.

1 Sama’ila 21

Dawuda ya Gudu daga wurin Saul

1 Sa'an nan Dawuda ya tafi wurin Ahimelek, firist, a Nob. Ahimelek kuwa ya fita da rawar jiki domin ya tarye Dawuda, ya ce masa, “Me ya sa kake kai kaɗai, ba wani tare da kai ba?” 2 Dawuda ya ce masa, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya aiko ni in yi. Jama'ata kuwa na riga na shirya inda zan sadu da su. 3 Yanzu me kake da shi? Sai ka ba ni abinci malmala biyar ko wani abu da kake da shi a nan.” 4 Firist ɗan ya ce wa Dawuda, “Ba ni da abinci don kowa da kowa, sai dai gurasa ta ajiyewa. Zan iya in ba ka muddin dai samarin sun keɓe kansu daga mata.” 5 Dawuda ya ce masa, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena suka keɓe kansu a koyaushe suka tashi 'yar tafiya, balle fa yanzu da muka fito yin wani abu musamman.” 6 Firist ɗin kuwa ya ba Dawuda tsattsarkan abinci na ajiya, gama ba wani abinci a wurin, sai gurasar ajiyewa kaɗai wadda akan kawar, a sāke sa wata mai ɗumi a ranar da aka kawar da ita. 7 A ranar kuwa akwai wani mutum daga cikin barorin Saul, wanda aka tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom ne. Shi ne shugaban masu kiwon garkunan Saul. 8 Dawuda kuwa ya ce wa Ahimelek, “Kana da māshi ko takobi a nan kusa? Gama ban zo da takobina ko wani makami ba, domin ka sani sha'anin sarki na gaggawa ne.” 9 Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.” Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.” 10 Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat. 11 Fādawan Akish kuwa suka ce masa, “Ashe, wannan ba shi ne Dawuda, sarkin ƙasar ba? Ba a kansa suka raira waƙa cikin raye-rayensu suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?’ ” 12 Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat. 13 Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa. 14 Akish kuwa ya ce wa fādawansa, “Ashe, mutumin mahaukaci ne? Don me kuka kawo shi wurina? 15 Na rasa mahaukata ne da za ku kawo mini wannan mutum ya yi ta hauka a gabana? Wannan mutum ne zai shiga gidana?”

1 Sama’ila 22

An Kashe Firistoci

1 Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da 'yan'uwansa da mutanen gidan ubansa, suka ji labari, suka tafi can wurinsa. 2 Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu. 3 Daga can Dawuda ya wuce zuwa Mizfa ta Mowab. Ya ce wa Sarkin Mowab, “Ina roƙonka, ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Ubangiji zai yi da ni.” 4 Sai ya bar iyayensa a wurin Sarkin Mowab, suka zauna a wurinsa duk lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu. 5 Sa'an nan Gad, annabi, ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tafi ƙasar Yahuza.” Sai ya tashi, ya tafi kurmin Haret.

Saul ya Kashe Firistoci na Nob

6 Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da māshinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi. ya ce wa fādawan da yake tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba ko wannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?” 9 Sa'an nan Doyeg, mutumin Edom, da yake tsaye tare da fādawan Saul, ya ce, “Na ga ɗan Yesse yana zuwa Nob wurin Ahimelek, ɗan Ahitub. 10 Shi kuwa ya roƙi Ubangiji domin Dawuda, ya kuma ba shi guzuri, har ya ba shi takobin Goliyat, Bafilisten.” 11 Sarki kuwa ya aika a kira Ahimelek, firist, ɗan Ahitub, da dukan mutanen gidan mahaifinsa, da firistocin da suke a Nob. Dukansu kuwa suka zo wurin sarki. 12 Saul kuwa ya ce, “Ka ji, ya ɗan Ahitub.” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka ya daɗe, ina ji.” 13 Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?” 14 Ahimelek kuwa ya ce wa sarki, “Daga cikin barorinka duka wa yake da aminci kamar Dawuda? Wane ne surukin sarki? Wane ne shugaban jarumawanka, wanda ake girmamawa a gidanka? 15 Yau ne na fara roƙar masa Allah? A'a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.” 16 Sai sarki ya ce, “Hakika, mutuwa za ku yi, Ahimelek, kai da dukan gidan mahaifinka.” 17 Ya ce wa matsara da yake tsaye kewaye da shi, “Ku fāɗa wa firistocin Ubangiji, ku kashe su gama suna goyon bayan Dawuda, ga shi, sun sani ya gudu, amma ba su faɗa mini ba.” Amma barorin sarki ba su yarda su fāɗa wa firistocin Ubangiji ba. 18 Sa'an nan sarki ya ce wa Doyeg, “Kai ka fāɗa wa firistocin.” Sai Doyeg, mutumin Edom, ya fāɗa wa firistocin, ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke saye da falmaran na lilin a wannan rana. 19 Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakai, da tumaki. 20 Amma Abiyata ɗaya daga cikin 'ya'yan Ahimelek, ɗan Ahitub, ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda. 21 Sai ya faɗa wa Dawuda Saul ya kashe firistocin Ubangiji. 22 Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka. 23 Sai ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro, gama wanda yake neman raina yana neman naka. Ka yi zamanka lafiya tare da ni.”

1 Sama’ila 23

Dawuda ya Kuɓutar da Garin Kaila

1 Aka faɗa wa Dawuda, cewa Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Kaila, suna washe musu hatsi a masussukai. 2 Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.” 3 Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, nan ma a Yahuza muna jin tsoro, balle mu tafi Kaila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa.” 4 Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.” 5 Sa'an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Kaila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kashe su da yawa, suka kwashe shanunsu. Da haka Dawuda ya kuɓutar da mazaunan Kaila. 6 Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa. 7 Aka faɗa wa Saul Dawuda ya zo Kaila. Sai ya ce, “Madalla, Allah ya bashe shi a hannuna, gama ya kulle kansa, da yake ya shiga garin da yake da ƙofofin da akan kulle da sandunan ƙarfe.” 8 Saul ya kirawo dukan mutanensa, su fita yaƙi, su tafi Kaila don su kewaye Dawuda tare da mutanensa. 9 Dawuda kuwa ya sani Saul yana shirya hanyar kashe shi, sai ya ce wa Abiyata, firist, “Kawo falmaran a nan.” 10 Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, hakika bawanka ya ji Saul yana niyyar zuwa Kaila don ya hallakar da garin saboda ni. 11 Ko mutanen Kaila za su bashe ni a hannunsa? Ko Saul zai zo kamar yadda na ji? Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ina roƙonka ka faɗa wa bawanka.” Ubangiji kuwa ya ce, “Saul zai zo.” 12 Dawuda kuma ya ce, “Mutanen Kaila za su bashe ni da mutanena a hannun Saul?” Ubangiji ya ce masa, “Za su bashe ku.” 13 Sa'an nan Dawuda da mutanen da suke tare da shi, mutum wajen ɗari shida, suka tashi daga Kaila, suka tafi inda hali ya kai su. Da Saul ya ji Dawuda ya tsere daga Kaila, sai ya fasa tafiya can.

Dawuda a Jejin Ƙasar Tudu

14 Dawuda ya zauna a ɓoye cikin jeji a ƙasar tudu ta jejin Zif. Saul kuwa ya yi ta nemansa kowace rana, amma Ubangiji bai ba da Dawuda a hannunsa ba. kuwa ya ji tsoro, gama Saul ya fito don ya farauci ransa. Sa'ad da yake cikin jejin Zif, a Horesh, sai Jonatan ɗan Saul, ya zo wurinsa, ya tabbatar masa da kiyayyewar Allah. 17 Ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama Saul, mahaifina ba zai same ka ba. Za ka zama Sarkin Isra'ila, ni kuma zan zama wazirinka. Saul mahaifina ya san da haka.” 18 Su biyu fa suka yi wa juna alkawari a gaban Ubangiji. Dawuda ya zauna a Horesh, Jonatan kuwa ya koma gida. 19 Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza. 20 Sai ka gangara, ka zo, ya sarki, ta yadda kake so. Mu za mu bashe shi a hannun sarki.” 21 Saul ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka, gama kuna jin juyayina. 22 Ku tafi, ku ƙara tabbatar da inda ya ɓuya, da wanda ya gan shi a wurin, gama an faɗa mini, cewa shi mai wayo ne. 23 Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.” 24 Sai suka yi gaba, suka tafi Zif. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon, cikin Araba, kudu da Yeshimon. 25 Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon. 26 Saul yana gefe ɗaya na dutsen, Dawuda kuma da mutanensa suna wancan gefe. Dawuda ya yi sauri ya tsere daga Saul domin Saul da mutanensa suna ƙoƙari su kewaye su, su kama su. 27 Suna bin su Dawuda kusa kusa, sai manzo ya zo ya ce wa Saul, “Sai ka komo da sauri domin Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.” 28 Saul kuwa ya koma daga bin Dawuda, ya tafi, ya yi yaƙi da Filistiyawa, don haka aka riƙa kiran wurin, Sela-hammalekot, wato dutsen tserewa. 29 Dawuda kuwa ya tashi daga can, ya tafi jejin En-gedi inda ya ɓuya.

1 Sama’ila 24

Dawuda ya Bar Saul da Rai a En-gedi

1 Da Saul ya komo daga yaƙi da Filistiyawa, sai aka faɗa masa Dawuda yana jejin En-gedi. 2 Sai Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000 ) daga cikin dukan mutanen Isra'ila, ya tafi ya nemi Dawuda da mutanensa a gaban duwatsun awakin jeji. 3 Saul ya isa garken tumaki a gefen hanya, inda akwai kogo. Sai ya shiga cikin kogon don ya huta. Dawuda da mutanensa kuwa suna zaune a ƙurewar kogon. 4 Mutanen Dawuda suka ce masa, “Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka yi yadda ka ga dama da shi.” Dawuda kuwa ya tashi a hankali, ya yanke shafin rigar Saul. 5 Daga baya zuciyar Dawuda ta kāshe shi domin ya yanke shafin rigar Saul. 6 Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji ya sawwaƙa in yi wa ubangijina irin abu haka, har in miƙa hannuna in kashe keɓaɓɓe na Ubangiji.” 7 Da wannan magana Dawuda ya rinjayi mutanensa, bai yarda musu su fāɗa wa Saul ba. Sai Saul ya fita daga kogon ya kama hanya, ya yi tafiyarsa. 8 Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna. 9 Ya ce wa Saul, “Me ya sa kake kasa kunne ga maganganun mutanen da suke cewa, ‘Dawuda yana nema ya cuce ka?’ 10 To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na j