Annabi Ishaya ya rubuta cewa: Yanzu fa Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata
budurwa wadda take da ciki, za ta haifi va, za a rava masa suna Immanuwel.

Wani manzon Almasihu, sunasa Matiyu, ya rubuta cewa: Ga yadda haifuwar Yesu
Almasihu take.  Sa'ad da Yusufu ke tashin Maryamu uwar Yesu, tun bai vauke ta
ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki ... Wani mala'ikan
Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin mafarki, ya ce, Yusufu van Dawuda, kada
ka ji tsoron vaukar Maryamu matarka, don cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki
ne.  Za ta haifi va, za ka kuma sa masa suna Yesu, don shi ne zai ceci
mutanensa daga zunubansu.  An yi wannan ne duk don a cika abin da Ubangiji ya
fava ta bakin annabin, cewa, Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi va,
kuma za a sa masa suna Immanuwel.  (Ma'anar Immanuwel kuwa, Allah na tare da
mu.)  Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala'ikan Ubangiji, ya
vauki mata tasa, amma bai san ta ba, sai bayan ta haifi vanta, ya kuma sa masa
suna Yesu.

Annabi Ishaya ya rubuta cewa: Ubangiji ya saukar mini da Ruhunsa.  Ya zape ni,
ya aike ni domin in kawo albishir mai davi ga talakawa, in warkar da wavanda
suka karai a zuci, in yi shelar kwance daurarru, da kuma 'yanci ga davanva ke
cikin kurkuku.  Ya aike ni in yi shela, cewa lokaci ya yi da Ubangiji zai ceci
mutanensa.

Abokin tafiyar wani manzon Yesu mai suna Luka ya rubuta cewa: Yesu ya koma
qasar Galili, ikon Ruhu na tare da shi.  Sai labarinsa ya bazu a dukkan
kewayen.  Ya yi ta koyarwa a majami'unsu, duk ana girmama shi.

Sai ya zo Nazarat inda aka rene shi.  Ya shiga majami'a ran Asabar kamar yadda
ya saba.  Sai ya miqe don ya yi karatu.  Sai aka miqa masa Littafin Annabi
Ishaya, ya buve littafin, ya sami inda aka rubuta cewa, Ruhun Ubangiji na tare
da ni, don ya shafe ni in yi wa matalauta Bishara.  Ya aiko ni in yi shelar
saki ga vaurarru, da kuma buve wa makafi ido, in kuma 'yanta wavanda ke danne,
in yi shela ta zamanin samun karpuwa ga Ubangiji.

Sai ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna.  Duk wavanda ke cikin
majami'a suka zuba masa ido.

Sai ya fara ce musu, Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.  Duk suka yabe shi,
suna mamakin maganarsa ta alheri da ya fava.